Koken 'yan Kasuwar Maigatari game da rufe iyakar Najeriya da Nijar

Koken 'yan Kasuwar Maigatari game da rufe iyakar Najeriya da Nijar

Rufe kan iyakar Najeriya da Nijar, sanadin juyin mulkin sojojin watan Yuli ya janyo durkushewar harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen manyan aminan juna na Afirka ta Yamma.

Daya daga cikin manyan wuraren da ake jin radadin rufe kan iyakar kasashen, shi ne Kasuwar Maigatari da ke kan iyakar Najeriya, a cikin jihar Jigawa, inda 'yan kasuwa ke cewa hada-hada da ciniki sun yi matukar raguwa tun bayan wannan mataki na kungiyar Ecowas.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta sanya wa Nijar takunkuman karya tattalin arziki ne har sai sun mayar da hambararren shugaban kasar Bazoum Mohamed kan karagar mulki.

Sai dai, shugabannin mulkin sojin Nijar karkashin jagorancin Janar Abdurahmane Tchiani sun ce hakan ba za ta taba yiwuwa ba, kuma sun yi alkawarin mayar da mulki hannun farar hula a cikin shekara uku.

Kalli bayanin da 'yan kasuwar Maigatarin suka yi wa BBC a kan halin da suke ciki a wannan bidiyo.