Nimet ta ce za a samu jinkirin saukar damina a wasu jihohin Najeriya

.

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen cewa za a samu jinkirin saukar damina a wasu sassan ƙasar musamman jihohin yankin arewa ta tsakiya.

Ministan kula da harkokin sufurin jiragen sama da sararin samaniyar ƙasar, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a lokacin fitar da rahoton hasashen da hukumar Nimet ta saba fitarwa na duk shekara.

Rahoton ya ce jihohin yankunan ƙasar da dama za su gamu da matsalar ɗaukewar damunar da wuri a bana.

Sai dai kuma hukumar ta NIMET ta ce, za kuma a samu saukar ruwan saman da wuri a jihohin Borno da Abiya da kuma Akwa Ibom saɓanin yadda aka saba gani.

Hasashen ya nuna cewa, za a samu ɗaukewar ruwan sama da wuri a jihohin Kano da Jigawa da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna a yankin arewa maso yamma.

Sai kuma Bauchi da Gombe da Yobe da Taraba a yankin Arewa maso gabas. Akwai kuma Filato da Nasarawa a yankin arewa maso tsakiya.

Sannan jihohin Legas da Ogun a kudu maso yamma da kuma Cross River a kudu maso kudu, da Ebonyi a kudu masu gabashin Najeriyar.

Sai dai kuma hasashen hukumar kula da yanayin ta Najeriya , NIMET ya nuna cewa wasu jihohin kasar za su iya samun saukar damina kamar yadda suka saba gani inda kuma za su samu ruwan sama kaman yadda suka saba samu a shekara.

Fargabar manoma

..

Asalin hoton, Getty Images

Tuni dai manoman ƙasar suka fara nuna fargaba kan wannan rahoto.

Kamar yadda sakataren yaɗa labaran ƙungiyar manoma ta Najeriya AFFAN, Honarabil Muhammad Magaji ya shaida wa BBC.

''Wannan babbar matsala ce indai wannan hasashe ya tabbata, domin tabbatar hakan zai janyo matsala mai yawa''.

Najeriya dai na fama da tsadar kayan abinci sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Wani abu da masana ke dangantawa da rashin yin noma a wasu yankunan ƙasar, sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke hana manoma zuwa gonakinsu domin yin noma.

Haka kuma a wasu lokutan ambaliyar ruwa da fari, kan taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarancin abinci a Najeriyar.

Me ya kamata manoma su yi?

Sakataren ƙungiyar manoman ya ce abin da ya kamata shi ne gwamnati da manoman su ɗauki matakan da suka dace don kauce wa asara.

''Abin da ya kamata idan aka samu irin wannan hasashen, to mu manoma mukan ɗauki matakan da suka dace don kauce wa asarar abin da za mu noma'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa abu na farko da ya kamata a yi shi ne gwamnati ta samar wa manoma ingantacen irin shuka da zai nuna da wuri kuma kan lokaci.

''Ya kamata tun watan ukun nan da za mu shiga kowace jiha ta tanadi kayan noma domin raba wa manoman da ke jihar'', in ji shi.

Sakataren ƙungiyar manoman ya ce idan ana so a wadata ƙasa da abinci, to gwamnati ta bai wa manoma tallafi mai yawa domin taimaka ma su.

"A kawo taimako mai yawa, ba ɗan kaɗan ba, a samar da irin nau'ikan amfanin gona mai inganci ta yadda manoma za su samu damar yin noma''.

Ya ce duk abin da gwamnati ta bai wa manoma ba faɗuwa ta yi ba.

Shugaban hukumar kula da yanayin ta Najeriya, NIMET, Farfesa Charles Anosike kamar sauran ƙwararru ya danganta wannan sauyi na yanayin damina da illar ɗumamar yanayi da duniya ke fuskanta.

Farfesa Anosike ya nuna yadda matsalar ke shafar duniya musamman Afirka, nahiyar da sama da mutum miliyan 110 suka gamu da matsalar sauyin yanayi, ta fannin yanayi da ruwa, a 2022.

Lamarin da ya haifar da asara da ta kai ta biliyoyin daloli.