Sifaniya ta nada Del Bosque ya kula da hukumar kwallon kafar kasa

Asalin hoton, Getty Images
An nada tsohon kociyan tawagar Sifaniya, Vicente del Bosque, domin ya ja ragamar kwamitin da zai kula da harkokin hukumar kwallon kafar kasar.
A makon jiya gwamnatin Sifaniya ta sanar cewar za ta kafa wani kwamiti na musamman da zai kula da hukumar kwallon kafar kasar, domin maye gurbin Rubiales.
Rubiales, tsohon shugaban hukumar kwallon kafar kasar na tsare a hannun jami'ai tun daga 3 ga watan Afirilu kan zargin cin hanci da rashawa.
Haka kuma ana tuhumar Rubiales da cin zarafi ta hanyar lalata, bayan da ya sumbaci Jenni Hermoso, bayan da Sifaniya ta lashe kofin duniya na mata a Australia a 2023.
Del Bosque ya ja ragamar tawagar Sifaniya ta maza ta dauki kofin duniya na farko a tarihi a 2010 da kuma kofin nahiyar Turai a 2012.
Mai shekara 73 ya lashe kofi takwas a lokacin da ya ja ragamar Real Madrid har da Champions League biyu a 2000 da kuma 2002.
Sifaniya na shirin karbar hadakar gasar kofin duniya ta maza a 2030 da za a buga a kasashe shida, ciki har da Portugal da Morocco da wasu uku daga kudancin Amurka.
Fifa ta ce tana bibiyar dukkan abinda yake faruwa a Sifaniya sau da kafa, kuma ta damu da lamarin da zai iya kawo tsaiko a shirin da take na karbar bakuncin kofin duniya.











