Brazil ta tsaurara matakan mallakar bindiga

Luiz Inacio Lula da Silva

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaba Lula da Silva ya yi hakan ne bayan da Bolsonaro ya sassauta matakin

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya sanya hannu a wata doka da za ta tsaurara matakan mallakar bindiga.

Shugaban mai ra’ayin ‘yan gaba-dai-gaba-dai ya yi hakan ne kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabensa.

Ya yi ne kuwa domin takaita yadda ake mallakar bindiga, barkatai, a dalilin sassaucin da wanda ya gada, Jair Bolsonaro mai ra’ayin rikau ya yi.

A dalilin sassaucin yawan masu makamin da rijista ya ninka sau bakwai a lokacin.

Shugaba Lula ya dauki wannan mataki ne ganin yadda ake ta samun karuwar yawan tashin hankali kamar yadda ya dora alhakin rikicin siyasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a bara, a kan sassaucin matakan mallakar bindigar.

Mista Lula, ya ce ''abu ne na daban, batun farar hula ya mallaki bindiga a gida domin kariya, domin tsaro, saboda wasu mutanen na dauka cewa mallakar bindiga a gida na ba su tsaro. To amma ba za mu bari gidan ya zama rumbun makamai a hannun jama’a ba.’’

Ya kaddamar da sabbin matakan masu tsauri ne bayan hare-haren bindiga aka kai a makarantu a kwanan nan, a kasar wadda aka yi kiyasin aikata kisan kai sama da biyar a cikin sa’a daya a shekarar da ta gabata 2022, kamar yadda binciken da wata kungiya mai zaman kanta ta yi ( Public Security Forum).

A lokacin da aka zabi tsoshon shugaban kasar Bolsonaro, Brazil tana da kusan mutum 800,000 da ke da bindiga da rijista , yawan da ya karu daga kasa da mutum 120,000 a 2018.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsohon shugaban a lokacin yana cewa mallakar bindigar ya sa kasar ta yi lafiya, yana nuni da raguwar laifukan kisan kai a lokacin mulkinsa.

Tsarin mulkin kasar bai tanadi dokar da ta bayar da damar mallakar bindiga ba.

To amma karkashin wata doka ta shugaban kasa wadda Bolsonaro ya zartar a 2019, ‘yan Brazil suka samu damar mallakar bindiga har guda hudu.

Yayin da wasu kuma sauka samu damar rike bindigar hatta a cikin jama’a ma, amma bisa wasu sharudda.

A bisa tanadin sabbin matakan a yanzu maharbin da ke da rijista zai iya mallakar bindiga shida mai makon 30 a baya.

Sannan kuma za a hana mallakar wasu nau’ukan bindigogin ciki har da ‘yar kararrama ta hannu mai tsawon milimetre tara.

Bugu da kari an mayar da ikon sanya ido a kan farar hula da ke da bindiga a kan ‘yan sandan tarayya maimakon hukumar sojin kasa, bayan da aka yi ta sukan tsarin na da kan sassaucin sojin a wannan aiki.

Ba za a tilasta wa wadanda suka sayi bindigoginsu lokacin Mista Bolsonaro mika su ba, to amma za a iya bullo da wani tsari da gwamnati za ta saye su daga wajensu a wannan shekara.