Dubbai na zanga-zangar neman tsaurara matakan mallakar bindiga a Amurka

Asalin hoton, Reuters
Dubban jama'a a ne suka yi zanga-zanga a Washington DC da sauran sassan Amurka inda suke rajin ganin an bullo da dokoki masu tsauri na mallakar bindiga.
Matakin ya biyo bayan jerin kisan tarin mutane da aka yi ne ta hanyar amfani da bindiga a kasar a cikin kwanakin nan, abin da masu fafutuka ke cewa za tilasta wa majalisar dokokin Amurkar daukar mataki.
Taken wannan gangami dai shi ne, ''Wannan lokacin zai zama daban.'' Tsawon shekaru dai majalisar dokokin Amurkar ta ki daukar matakin yin dokokin takaita mallakar bindiga a kasar wanda zai kai ga rage aikata ta'asar da 'yan bindiga-dadi kan tafka.
Masu rajin mallakar bindiga da kuma 'yan jam'iyyar Republican ne kan yi wa 'yan majalisar tarnaki a kan hakan.
To amma harbin da dan bindiga-dadi ya yi a wata makarantar furamare a Texas inda ya hallaka yara 19 hadi da malamansu biyu, ya sauya salon muhawarar da ake yi a kan batun.

Asalin hoton, Reuters
Wannan hari da kuma wani da aka kai 'yan kwanaki kafin shi a Buffalo, da ke New York, inda dan bindiga ya kashe mutum goma, sun kara tayar da hankalin mutane da ke son ganin an dauki mataki a kan takaita mallakar bindiga a Amurka, inda a yanzu batun ya koma kan maganar kare yara.
A ranar Asabar masu fafutukar ganin an dauki matakan takaita mallakar bindiga, wadanda suka kunshi mutanen da suka tsira daga harin makarantar Parkland a Florida a 2018, sun ce za a yi irin wannan gangami har 450 a fadin Amurkar.
A biranen da suka hada da Washington DC da New York da Los Angeles da Chicago.
Kungiyar ta ce ba za ta bari 'yan siyasa su zauna sasakai kawai su bari ana kashe mutane ba.
A farkon makon da ke karewa 'yan majalisa wakilan Amurkar sun amince da wani kudurin doka, wanda ko makawa babu 'yan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican za su yi watsi da shi.

Asalin hoton, Reuters
To amma akwai wadanda suke aiki don ganin an samu matsaya a kan lamarin, wanda da hakan ake ganin kila kudurin ya samu nasara.
Shugaba Biden ya yi kira ga masu zanga-zangar da su ci gaba da matsa lamba, har sai hakarsu ta cimma ruwa:
Ya ce, ''Ku ci gaba da maci! Yana da muhimmanci! Wannan abu ne da ya zama batun zaben. Yadda mutane ke sauraro, sanatoci, majalisa, idan har mutane suka ce, wannan zai shafi kuri'ata'.
Ana hallaka tarin mutane haka kawai, kuma kudurin da ake kokarin aiwatarwa a majalisar wakilai da kuma ta dattijai ba wani abu ne na a-zo-a-gani ba.
Abu ne mai muhimmanci, amma kuma ba dukkaninsa ba ne ya wajaba a yi.
Haka suma masu raji suna fadi tashin kira ga jama'a da su kada kuri'a, da cewa mutane sun gaji da kasancewa a yanayi na rashin tsaro a makaranta.











