Dan bindiga dadi ya kashe mutum 12 a mashaya a Amurka

'Yan mata suna tsaye kusa da 'yan sanda

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mashayar ta shahara sosai a wajen daliban jami'a a yankin
Lokacin karatu: Minti 3

Mutum 12 ne suka mutu ciki har da dan sanda, lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta a mashayar Aoks, da ke birnin California.

'Yan sanda sun ce da karfe 11:30 agogon Amurka dan bindigar ya fara harbin kan mai tsautsayi.

Akalla mutum 200 ne aka kiyasta na cikin mashayar, inda daliban jami'a ke gudanar da wani biki na dare, lokacin da aka kai harin.

'Yan sanda sun bayyana sunan wani mutum mai shekara 28 Ian David Long, wanda ake zaton yana da tabin hankali, a matsayin wanda ake zargi da kai harin.

Hukumomi sun ce maharin, wanda tsohon dan sandan kundumbala ne ya kashe kansa a cikin mashayar.

Yalamarin ya faru?

'Yan sanda sun ce wanda ake zargin Ian David Long ya yi shigar bakaken kaya ne, sannan ya kutsa cikin mashayar bayan ya harbe mai gadin mashayar.

Wani shaida ya ce maharin ya kuma jefa wani gurneti mai hayaki sannan ya bude wuta.

Two women hug outside the shooting

Asalin hoton, EPA

Wata da ta tsira mai suna Telor ta ce "Ina kan dandamalin rawa kawai sai na ji karar harbin bindiga, da na waiga sai kawai sai na ji kowa yana ihun cewa: A Kwanta!

"An shiga gagarumin rudani sai kowa ya mike, an tattake ni, kusan an bar ni wanwar a kasa, sai da wani ya zo ya kama ni ta baya ya ja ni waje."

Mutane sun yi amfani da kujeru wajen fasa gilasan tagogin mashayar, yayin da wasu kuma suka fake a bandakunan mashayar.

'Yan sanda sun ce akalla mutum 10 sun ji rauni a harin.

Amurka ta jima tana fama da matsalar 'yan bindiga dadi masu kashe mutane, to sai dai lamarin ya fi muni a 'yan shekarun nan.

Presentational white space

A mako biyu da suka gabata kadai wani mutum ya bindige wasu mutum biyu har lahira a birnin Florida, wani mutumin kuma ya bude wuta a wajen bautar Yahudawa a garin Pittsburgh, inda ya kashe mutum 11.

Hari mafi muni kuwa a tarihin Amurka ya faru ne bara a Las Vegas, lokacin da wani mutum mai shekara 62, ya bude wuta a kan mutum 22,000 da suka taru domin wata gagarumar rawa, inda ya kashe mutum 58, ya kuma jikkata wasu daruruwa.

Harin mafi muni da ke biye masa kuma shi ne wanda aka kai bara waccan, wanda aka kashe mutum 49, a wani gidan rawa na 'yan luwadi a cikin watan Yuni na 2016.

Presentational white space

Wasu dalibai daga babbar makarantar Marjory Stoneman Douglas a Parkland, Florida - inda aka kashe dalibai 17 a watan Fabrairun bana - sun kaddamar da wani gangami na sanya dokar hana mallakar bindiga a 'yan watannin nan, to amma babu wani sauyin a zo- a gani da aka samu daga 'yan majalisa.

A cewar shafin intarnet din wata kungiya da ke tattara irin barnar da ake yi da bindiga a Amurka, sama da mutum 12,000 aka kashe ta amfani da bindiga a Amurka a bana kawai, ciki har da kimanin mutum 3,000 'yan kasa da shekara 18.

Adadin bai hada da wadanda suke kashe kansu ba da bindiga da aka kiyasta cewa suna kaiwa 22,000 duk shekara.

Taswirar mashayar da aka harin na California

Shugaba Trump ya mayar da martani

Shugaba Donald Trump ya aika sakon Twitter yana Alla-wadai da harin, inda ya ce an yi masa bayani kan al'amarin.

Ya bayyana harin a matsayin wani babban bala'i, sannan ya jnjina wa jarumtar dan sandan da ya mutu a harin.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

An kuma yo kasa-kasa da tutoci a fadar shugaban Amurka ta White House domin girmama wadanda aka kashe.