Jair Bolsonaro, bindigogi da kuma karuwar rikici a Brazil

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Katy Watson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sao Paulo, Brazil
Dabi'ar amfani da bindiga ita ce ginshikin nasarar da Shugaba Bolsonaro ya yi ta zama shugaban kasar Brazil.
Amma shekaru uku bayan hakan, wane irin tasiri ya yi a kasar, da dangantaka tsakanin Brazil da Amurka ta fuskar siyasa, da dangataka tsakanin kasar da hukumar da ke sa ido kan mallakar makamai?
Wake da shinkafa abinci ne ma fi soyuwa a zukatan yawancin 'yan Brazil.
Akalla dai ana kaunar wani nau'in abinci a kasar da ke fama da rarrabuwar kai, kasar da ake siyasantar da komai.
Sai dai duk wannan gabannin Jair Bolsonaro ya kawo wani abu na daban mafi soyuwa ga 'yan kasar.
"Masu ra'ayin 'yan mazan jiya sun ce mutane ba za su ci bindiga ba, sai wake," in ji Bolsonaro cikin raha. Makwanni kadan bayan nan ya farwa masu sukar lamirinsa da ke cewa sayen abinci ya fi muhimmanci ga 'yan Brazil maimakon makamai.
"To idan wani ya kai maka hari gida, ka harbe shi da wake," in ji Bosonaro.
Haka kuma wata hanya da yake amfani da ita wajen musguna wa masu sukar gwamnatinsa ita ce daga yatsu biyu.
A lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2018, ya yi amfani da yatsu biyu kamar harbin bindiga, wannan sako ne yake aika wa magoya bayansa, duk kuwa da cewa ko a kasashen da ake samun yawan mace-mace sanadiyar harbin bindiga, sassauta dokar mallakar bindiga ba abu ne mai sauki ba.
A ranar 15 ga watan Janairun 2019, makwanni biyu da shan rantsuwar kama aiki, Bolsonaro ya yi wa 'yan kasar alkawarin sassauta dokar.
Shugaban Brazil ya rattaba hannu kan dokar shugaban kasa da ta saukaka wa 'yan kasar ajiye bindiga a gidajensu, da kuma kara wa'adin mallakar bindiga daga shekara biyar zuwa 10.
Kamar yadda Bolsonaro ya bayyana mataki ne da zai kwantar wa da 'yan kasar hankula a gidajensu.
Ba a nan ya tsaya ba, shugaban ya kuma yi sauye-sauye sama da 32 ga dokokin mallakar bindiga, ciki har da kara adadin bindigar da mutum guda zai iya mallaka, da sassauta dokar mallakar alburusan da mutum zai saya a lokaci daya, da ikon mallakar manyan makamai.
Ga Akira Ando, da ya mallaki wani kulob din bindiga a garin Atibaia da ke Sao Paulo, ya ce cikin 'yan shekarun nan kasuwa ta bude sosai.
"Ko da yaushe za ka ji karan wayar tarho," in ji Akira, lokacin da yake tsokaci bayan zartar da dokar shugaban kasa kan mallakar bindiga.
"Mutanen da ba sa taba tunanin mallakar makami domin ajiyewa a gidajensu, yanzu su ne ke kiran waya domin bukatar saya."
Dole ta sanya ya rubanya ma'aikatan da ke aiki karkashinsa, ya kara ma'aikata a bangaren gudanarwar kulob dinshi, inda a yanzu yake da ma'aikata sama da 2,500.
Amma a shekarar da ta gabata ma'aikata 1,000 kadai yake da.
"Bayanan wadanda suke shiga kulob din ya yi matukar sauyawa, idan aka kwatanta da shekarun baya," in ji Ando.
"Aikinmu shi ne mu koya musu harbin bindiga, da bin ka'idojin mallakarta kafin su saya a wajenmu domin kare iyalansu a gida."

Asalin hoton, Getty Images
Wani dan kasuwa mai suna Elias Paulo Kury daya ne daga cikin mambobin kulob din. Sabon shiga ne a fannin koyon harbin bindiga, ya ce yana jin dadin wajen, ya bayyana karara abin da yake buri shi ne ya dauki bindiga da iya harbi da ita.
"Duk bata-gari suna da bindiga, don me ya sa mu ba za mu mallaka domin kare kanmu da iyalanmu ba? A ganina wannan bai dace ba.
A wannan zamanin alhakin abin da ya same mu ya rataya ne a wuyanmu saboda ba mu kare kanmu ba," in ji Paulo, ya kuma kara da cewa rashin aikin yi da talauci na kara munanan tashin hankali da muggan laifuka a kasar.
Lokaci ya yi matukar sauyawa a Brazil.
A shekarar 2003 aka rattaba hannu kan dokar zub da makamai, da tsaurara dokar mallakarsu.
Bayan shekara guda aka yi gangamin zub da makamai na kasa baki daya, inda aka mika wa gwamnati sama da makamai 500,000.
Amma a shekarar 2005 aka gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan haramcin mallaka da sayar da bindiga.
Duk da cewa bindiga ce sanadiyar yawancin mace-mace a Brazil, sai aka samu bambancin ra'ayi inda yawanci ke bukatar a ci gaba da sayarwa da mallakarta, a bangare guda kuma 'yan kasa sun nuna kin amincewa da dokokin baki daya.
Wata kwararriya a fannin tsaro kuma darakta a cibiyar Igarapé Institute da Rio de Janeiro, Melina Risso ta ce an samu karuwar shigowa da sayar da makamai a kasar cikin 'yan shekarun nan.
"A baya ba ka isa ka dinga yawo da bindiga a Brazil ba, akwai tsattsaurar doka kan hakan.
Amma daga shekarar 2005, masoya bindiga sun yi kokarin sauyawa 'yan Brazil tunani.
Ba wai Bolsonaro ne ya fara hakan ba."
Sai dai babu shakka Bolsonaro ne ya janyo muhawara kan mallakar bindiga ta zafafa tsakanin 'yan kasar tun bayan karbar ragamarta.
Hukumar da ke sa ido kan mallakar makamai da tsaron al'umma ta ce a shekarar da ta gabata an samu rubanyar wadanda suke zuwa hukumar 'yan sanda domin yin rijistar mallakar bindiga, idan aka kwatanta da shekarar 2017.
Sannan a shekarar da ta gabata kadai an samu karuwar yin rijistar makamai , 186,071 , adadin da ya kai kashi 97 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Samurai Caçador daya ne daga cikin wadanda suka ci gajiyar sabuwar dokar.
Maharbi ne, kuma fitacce a shafukan sada zumunta, yakan yi batun bindiga lokaci zuwa lokaci a shafukan intanet.
"Ban taba mallakar makami ba," in ji shi, ya yi bayanin cewa ya fito daga iyalan da ba su amince da mallakar bindiga a gida ba saboda dalilai na tsaro.
"Ina son sanin yaya duniya take, na dauki wannan batu na bindiga da nufin sanin abin da ya kunsa."
Samurai maharbi ne da ke farautar dabbar daji ta Boar mai hdri, kuma ita ce kadai dabbar da aka amince a harbe ta a Brazil domin a rage yawanta sakamakon cutar da jama'a da take yi.
Tsakanin shekarar 2019 da 2020, an samu karuwar kusan kashi 30 na mafarauta da ke bukatar shaidar mallakar bindiga.
"Ina son ganin na ba da tawa gudummawar, domin bayyanawa mutane abin da ake nufi da makamai, da dalilan mallakarsu da hanyoyin da ya dace a yi amfani da su.
Hakan 'yanci ne, to amma kana da damar zabar mallakar makamai ko akasin haka.
Kuma shugaban kasa yana kokarin ganin kare hakan."
Sai dai kwararru na cewa wannan mataki ne da zai janyo koma baya, a ksar da ke fama da talauci, mai al'umma sama da miliyan 200, da mace-macen sama da mutum 500,00 sandin harbin bindiga a shekarar da ta gabata. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan na ta nuna kashi biyu cikin uku na 'yan Brazil sun nuna kin amincewa da mallakar bindiga.
Wasu su na alakanta hakan da dokar mallakar bindiga a Amurka karkashin mulki shugaba Donald Trump.
"Ba na zaton hakan ba amfani da abin da ke faruwa a rayuwar yau da kullum ba ne, kawai dai wani salo ne na Bolsonaro da ya yi wa kwaskwarima da kwaikwayon Shugaba Trump.
Dukkansu biyun suna amfani da dabi'ar amfani da bindiga, sai suka ce yawwa mun samu abin fakewa."

Asalin hoton, Getty Images
Bolsonaro ya bayyana karara yadda Donald Trump da dabi'un Amurka ke burge shi, ya kuma sha fada a bainar jama'a, kuma makusanta Bolsonaro da jami'an gwamnati da aminansa mazauna Amurka irin su Olavo de Carvalho da Rodrigo Constantino, sun san da hakan.
Sai dai ba kamar Trump ba, shi Bolsonaro harkar kamar ta gida ce. Dansa Eduardo mamba ne na kud-da-kud da masu karfin fada a ji na Amurka, inda ya yi kokarin kulla alaka mai inganci da mutane kamar Steve Bannon.
Akwai wai hoto da aka nuna Eduardo da dan Shugaba Trump, Don Trump Jr inda suka rike bindiga, kusan mutane da dama na Brazil sun ga wannan hoto tare da birge su.
"Abin da mutane ke kallo kawai shi ne yadda 'ya'yan manyan mutanen biyu suka dauki hoto da bindiga samfurin AR15s," in ji Winter.
Amma a yanzu fa? Shugaba Trump ba shi ne shugaban Amurka ba, sannan har yanzu Bolsonaro bai sanar ko zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a karo na biyu ba a zaben shekara mai zuwa.
Har wa yau, yadda ya tafiyar da barkewar annobar cutar koron a kasar, ya janyo ma sa bakin jini a idanun 'yan kasar.
Sai dai duk da haka, wasu 'yan kasar na ganin ya yi matukar tasirin sauya siyasar Brazil, musamman fannin mallakar bindiga.
"Idan muka duba kididdiga, duk wani muhimmin nazari da aka yi, ya nuna idan kana da bindigogi da yawa, to kuwa kana cikin tashin hankalin fuskantar kalubale da dama musamman a kasa kamar Brazil,"in ji Melissa Risso.
"Matsalar ta yi mummunar illa da tasiri a Brazil, idan aka duba ta fuskar takaita amfani da makaman, da sassauta dokokin mallakar bindiga, da kuma yawan al'ummar da kasar ke da su.
Illar sai nan gaba za a gan ta, za kuma a dauki lokaci kafin a shawo kan matsalar da hakan za ta haifar."











