Saliyo na gudanar da zaɓe cikin yanayi na fargaba

Fiye da mutum miliyan uku ne ake sa ran za su kada kada kuri'a domin zaɓen shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki da kuma na kananan hukumomi, a Saliyo.
Wannan shi ne zaɓe na biyar tun bayan kawo karshen yaƙin basasar kasar shekaru 21 da suka gabata.
Shugaba Julius Maada Bio da ke neman sake tsayawa na tsawon shekaru biyar, zai fatata ne da wasu ‘yan takara 12, amma masana sun ce babban abokin hamayyarsa shi ne Dr Samura Kamara, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban kasar da aka yi a 2018.
Kowanensu ya yi ikirarin samun nasara a zaɓen.
Sai dai kasar na fama da dimbin matsaloli da suka hada da tsadar rayuwa, talauci da hauhawar farashin kayayaki da kuma rashin aikin yi.
Mutane da dama sun adana abinci gabanin zaɓen saboda fargabar tashin hankali, bayan da aka yi taho-mu-gama tsakanin ‘yan sanda da magoya bayan 'yan adawa wanda ya yi sanadin mutuwar mutum daya a ranar Laraba.
Kungiyoyi masu sa ido kan zaɓe sun yi kira da a tabbatar da zaman lafiya tare da mutunta doka.
Dole ne wanda ya yi nasara ya samu kashi 55 cikin 100 na kuri'u, idan kuma hakan bai samu ba, toh za a yi zaɓe zagaye na biyu tsakanin manyan 'yan takara biyu da ke gaba-gaba a zagayen farko.
Ana kyautata zaton matasa masu kaɗa kuri'a ne za su yi tasiri a wannan zaɓe.
Duk da dimbin albarkatun kasa, Saliyo ta kasance ɗaya daga cikin kasashe mataulata a duniya.
Kasar mai yawan al'umma miliyan 8 ta fuskanci iftila'i a baya ciki harda annobar Ebola a 2014 da kuma cutar korona.











