'Ba mu yi mamakin dage zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ba'

 BVAS

Asalin hoton, INEC

Bayanan hoto, Kotu ta yarda INEC ta sake saita na'urar BVAS don zaɓen gwamnoni

Masu sharhi kan lamuran siyasa a Najeriya sun fara tsokaci kan matakin da hukumar zabe mai zaman kan ta INEC ta dauka, na dage lokacin zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha daga 11 ga watan Maris zuwa 18 ga watan.

A daren Laraba ne hukumar zaen ta yi wannan sanarwa bayan kammala wani taron sirri da manyan jami'anta a birnin Abuja, fadar gwamnatin kasar.

Shugaban gidauniyar McAthor a Najeriya Dr Kole Shettima shugaba, ya shaidawa BBC cewa bai yi mamaki ba da sanarwar INEC, kasancewar wasu jam'iyyu sun shigar da kara gaban kotu tare da neman a bada damar duba na'urar tantance masu zabe ta BV's wadda akai ta korafin ba ta yi aiki yadda ya dace ba a lokacin zanben shugaban kasa da aka kallama.

''INEC ta je gaban kotu tare da bukatar a dage umarnin da aka bada na duba na'urar in ba haka ba, ba za su samu damar yin zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihi kamar yadda aka tsara gudanarwa ranar 11 ga watan Maris.

Kotu ba ta bada na ta bayanin ba sai a ranar Laraba, hakan kuma na nufin lokaci ya kurewa INEC yin duk wani shiri gyara, da tura ma'aikatan da za su gudanar da aikin zaben nan.

Kuma kowacce na'ura ana sanya ranar da za a yi zabe da lokaci a cikinta, kafin ayi aikin nan na na'urori kusan 100,000 gaskiya babu lokaci,'' in Kole Shetiima.

Kole ya ce hukumar zabe ta bi umarnin kotu ne akan tsarin ta, kuma hakan ya yi daidai domin kaucewa zargin ko akwai wani da INEC din ke boyewa na rashin gaskiya.

'Yan siyasa za su ci gaba da kamfe, kuma jam'iyyu ba za su ji dadi ba har da ita kan ta hukumar zabe, saboda sun kashe kudade akan wannan mako mai zuwa.

''Mutane da dama za su yi asarar kudadensu, ciki har da masu sanya ido na cikin gida da waje, da mutanen da su ma suka yi shirin zuwa jihohinsu domin zaben, dan haka kowa zai yi asara. Fatan mu shi ne hukumar zabe ta tabbatar da yi gyara da kaucewa kura-kuran da aka samu a zaben shugaban kasa da na 25 ga watan jiya.''