'Ba zan daina gwagwarmayar bunƙasa Amurka ba'

Asalin hoton, Getty Images
Kamala Harris ta amsa shan kayi hannun Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasar Amurka.
Da take jawabi ga magoya bayan ta a birnin Washington, Ms Harris ta ce tane sane da alhinin da suke ciki, kuma ta sha alwashin bayar da goyon baya wajen miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali.
Mataimakiyar shugaban ƙasar ta ce za ta ci gaba da yaƙin tabbatar da dimokuradiyyar Amurka, da kare doka da oda da kuma jajircewa wajen cimma nasarar abin da ta sanya a gaba.
A jawabi na farko da ta yi wa masoyanta bayan shan kayi a zaɓen, Ms Harris ta fara ne da sanar da su cewa tana sane da yadda suke ji a zukatan su, amma ta ce yanzu lokaci ne na aiki tare domin cimma nasarar miƙa mulki ga sabuwar gwamnati.
Mataimakiyar shugabar Amurkan ta ce babu ja da baya a gwagwarmayar ceton Amurka da Amurkawa.
Ta ce: "Ba zan taɓa gajiyawa ba wajen gwagwarmayar kyautata rayuwar Amurkawa da tabbatar da muradin su, ta yadda matan Amurka za su samu ƴancin yanke hukunci a kan abin da ya shafi rayuwar su da kuma jikinsu.Ba aikin gwamnati bane yin haka.
‘‘Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen bayar da kariya a makarantu da kan titunanmu, da kawar da yawaitar bindiga a hannun jama’a. Babu ja da baya a ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci ga kowanne ɗan Amurka domin kuwa dukkanmu muna da ƴanci da ya kamata a mutumta’’

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakiyar shugaban ƙasar ta sha alwashin ci gaba da tsayawa domin kare tsarin dimokuraɗiyyar Amurka, tare da ƙarfafa gwiwar masoyan nata don ganin sun ci gaba da kare zaɓinsu.
Ta ce: ‘‘Lokacin yaƙin neman zaɓe na riƙa cewa idan muka jajirce za mu yi nasara, amma gaskiyar magana wani lokaci jajircewar ba ta gajeren zango ba ce. Amma hakan ba ya nufin ba za mu yi nasara ba.
‘‘Abu mafi muhimmanci shi ne kada ku taɓa gazawa. Kada ku ja da baya, kuma kada ku karaya. Kada ku taɓa yanke ƙauna ga ƙoƙarin inganta halin da duniya ke ciki. Kuma kada ku taɓa sauraron waɗanda za su ce maku abu kaza ba zai yiwu ba saboda ba a taɓa yi ba a tarhi.’’
Kafin jawabin nata a birnin Washington dai, Ms Harris da shugaba Biden sun kira Donald Trump ta waya, inda suka taya shi murnar nasarar da ya samu, kuma zaɓaɓɓen shugaban kasan ya gamsu da kiran da suka yi na aiki tare domin haɗa kan Amurka.











