Netanyahu da Keir Starmer sun taya Trump murna

Asalin hoton, Reuters
Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya taya Donald Trump murna, bayan ɗan takarar ya yi jawabin nasararsa.
Netanyahu ya ce, "ina taya ka murnar samun nasarar yin dawo-dawo mafi girma. Dawowarka shugaban ƙasar Amurka wata dama ce domin samar da sabuwar Amurka, da kuma ƙara inganta alaƙa da Isra'ila," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "wannan nasara ce babba."
Shi ma firaiministan Hungary, Viktor Orban ya taya Trump murna, inda ya ce, "wannan babbar nasara ce a tarihin siyasar Amurka. Muna taya Donald Trump murna."
Shi ma firaiministan Burtaniya Keir Starmer ya shiga cikin jagororin ƙasashen da suka taya Trump murna, inda ya bayyana nasarar da "nasara babba."
"Za mu ci gaba aiki tare kamar yadda muka saba, kasancer ƙawancenmu tun aru ne. Za mu ɗaura ne daga inda muka tsaya wajen yin aiki kafaɗa da kafada domin ciyar da ƙasashenmu da dimokuraɗiyya gaba."
Ya ƙara da cewa za su yi aiki tare wajen inganta tsaro da haɓaka tattalin arziki da sauransu, sannan ya ƙara da cewa, "na san alaƙar Amurka da Burtaniya da na kyau."
Trump dai ya bayyana nasararsa ne duk da kasancewar bai riga ya kai adadin wakilan zaɓen da ake buƙata ba.
Donald Trump dai samun wakilan masu zaɓe 279 da ake buƙata mutum ya ci zaɓen daga cikin 538 a jihohi 50 na ƙasar, inda ya doke abokiyar takararsa, mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris wanda ta samu wakilan masu zaɓen 223.
Duk da cewa har yanzu ba a kai ga bayyana Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen a hukumance ba to amma tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ayyana kansa a matsayin wanda ya samu gagarumar nasara a zaɓen.

Asalin hoton, Getty Images
Trump ya yi jawabin samun nasara

Donald Trump da matarsa Melania Trump da mataimakinsa JD Vance sun hau dandamalin jawabi domin yi wa magoya bayansa jawabi na samun nasara.
A cewarsa, "za mu dawo da ƙasarmu hayyacinta," sannan ɗimbin magoya bayansa suka fara tafi suna ihu.
Ya sake nanata ƙudurinsa na tsuke iyakokin ƙasar.
Ya ƙara da cewa, "wannana nasara ce ga ƴan Amurka, wanda kuma hakan ne zai ba mu damar sake dawo da martabar Amurka.
A ƙarshe ya yi godiya ga matarsa da mataimakinsa da magoya bayansa baki ɗaya.
Trump ya bayyana samun nasararsa, duk da cewa har zuwa yanzu bai kai ga tara adadin wakilan zaɓen da ake buƙata ba a hukumance.
Trump ya yaba wa matarsa Melania

Asalin hoton, Reuters
A jawabin nasa, Donald Trump ya kuma yaba wa matarsa Melania Trump, inda ya kira ta da uwargidan shugaban ƙasa.
Ya yaba wa littafin da ta rubuta a ciki, inda ya bayyana littafin da ɗaya daga cikin waɗanda suka fi cin kasuwa.
"Ta yi aiki sosai," in ji shi, sannan yaƙara da cewa, "tana taimakon mutane sosai."
Ya kuma yi godiya da yaransa, inda ya kira sunansu ɗaya bayan ɗaya a saman dandamalin.
Haka kuma a cikin jawabin nasa, Trump ya bayyana Elon Musk, wanda ya shiga cikin yaƙin zaɓensa sosai a matsayin "mutumin kirki."
Ya bayar da labarai mai tsawo kan alaƙar da ke tsakaninsu.











