Zaɓen Amurka: Su wane ne wakilan masu zaɓe da ake kira 'electoral college' kuma wace rawa suke takawa?

A ranar Talata ne miliyoyin Amurkawa suka kaɗa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasar Amurka. Sai dai akwai yiwuwar ɗan takarar da ya fi yawan kuri'u ba shi ne zai yi nasara ba.
Domin kuwa ba masu kaɗa ƙuri’a ne ke zaɓar shugaban ƙasa kai tsaye ba, wani tsari ne da ake kira wakilan masu zaɓe ko kuma electoral college a Turance.
Me ake nufi da wakilan masu zaɓe?
Mafi yawan masu zaɓe sun kaɗa ƙuri'a ne ga ƴar takarar Democrat Kamala Harris ko ɗan Republican Donald Trump.
Amma waɗannan ƙuri'un ba su za su tantance wanda ya yi nasara kai tsaye ba. A maimakon zaɓe na ƙasa bai-ɗaya, zaɓen na kasancewa ne a matakin jiha-jiha.
Samun ɗaya daga cikin jihohi 50 na nufin ɗan takara ya lashe duk ƙuri'un abin da ake kira wakilan zaɓe na wanna jihar. Akwai adadin kuri'u 538 na wakilan zaɓe a Amurka baki ɗaya.
Ana buƙatar dan takara ya sami rinjayen kuri'u - 270 ko fiye da haka - don lashe zaɓen shugaban ƙasa. Abokin takararsu kuma ya zama mataimakin shugaban ƙasa.
Ya ake fayyace batun wakilan zaɓe?
Kowace jiha tana da adadin kuri'un wakilan zaɓe da ta ke da su, kuma hakan na kasancewa ne daidai da yawan al'ummarta.
California tana da mafi yawan wakilan zaɓe inda ta ke da 54, yayin da ɗimbin jahohin da ba su da yawa kamar Wyoming da Alaska da North Dakota (da Washington DC) suna da mafi ƙaranci inda kowannensu ke da guda uku.
Gabaɗaya, jihohi suna ba da dukkan ƙuri'unsu na wakilan zaɓe ne ga duk wanda ya samun ƙuri'un masu yawa daga al'ummar jihar.
Misali, idan ɗan takara ya lashe kashi 50.1% na ƙuri'un da aka kaɗa a Texas, ana ba su dukkan kuri'u 40 na jihar wakilan zaɓen jihar. Ko ma wani irin rinjaye ɗan takara ya samu a ƙuri'un da aka kaɗa yawan ƙuri'un zaɓen da zai samu ɗaya ne.
Shin za a iya lashe mafi yawan ƙuri'u a faɗin ƙasar amma duk da haka a faɗi zaɓe?
Ƙwarai da gaske. Mai yiyuwa ne ɗan takara ya zama shugaban ƙasa ta hanyar lashe zaɓuka masu tsauri, duk da samun ƙarancin ƙuri’u a faɗin ƙasar baki ɗaya.
A shekarar 2016, Donald Trump ya doke Hillary Clinton duk da cewa ta tsere masa da tazarar ƙuri'u kusan miliyan uku. A shekara ta 2000, George W Bush ya doke Al Gore duk da cewa ɗan takarar jam'iyyar Democrat tsere masa da adadin kuri'u fiye da dubu ɗari biyar.
An zaɓi wasu shugabanni uku ne kawai ba tare da sun lashe mafi yawan adadin ƙuri'u ba, dukkansu a cikin karni na 19.
Me ya sa ake kiransa 'electoral college'?
Kalmar “kwaleji” tana nufin gungun mutanen da ke da alhakin kaɗa ƙuri’ar jiha, waɗanda aka fi sani da wakilan zaɓe.
Ana amfani da wannan tsarin ne kawai don zaɓar shugaban ƙasa - duk sauran zaɓen Amurka ana lashe su ne ta hanyar samun mafi yawan adadin ƙuri'un da aka kaɗa.
Shin dole ne wakilan zaɓe su zaɓi ɗan takaran da ya yi nasara a jiharsu?

Asalin hoton, Getty Images
A wasu jihohin, wakilan zaɓe za su iya kaɗa wa duk ɗan takarar da suka ga dama, ba tare da la'akari da wanda al'umma suka goyi baya ba.
Amma a zahiri, kusan kodayaushe wakilan zaɓe kan zaɓi ɗan takarar da ya fi yawan kuri'u a jiharsu ne.
Idan wakilin zaɓe ya kaɗawa wanda ba shi al'ummar jiharsa suka zaɓa ba, aka yi masa laƙabi da "wanda ba ya bin aƙidar jihar".
A shekarar 2016, gugun wakilan zaɓe bakwai ne suka kaɗa irin wannan ƙuri'a, amma hakan bai sauya sakamakon zaɓen ba.
A wasu jihohi, ana iya cin tarar wakilan masu irin wannan ra'ayin ko kuma a tuhume su.
Me zai faru idan ƴan takara suka yi kunnen doki a adadin ƙuri'un wakilan zaɓe?
Idan ba a samu wanda ke da rinjaye ba, Majalisar Wakilan Amurka ce za ta kaɗa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasa.
Wannan ya faru sau ɗaya ne kawai a tarihi a shekarar 1824, lokacin da ƴan takara huɗu suka raba ƙuri'un wakilan zaɓe, suka hana kowane ɗayansu samun rinjaye.
Idan aka yi la’akari da rinjayen da jam’iyyun Republican da Democrats ke da shi a yanzu, da wuya hakan ya faru a yau.
Me ya sa aka ƙirƙiro da wannan tsarin?
Lokacin da aka tsara kundin tsarin mulkin Amurka a shekara ta 1787, zai yi wuya a iya tabbatar da wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da adadin ƙuri'un da al'umma suka kaɗa saboda girman ƙasar da kuma rashin ingantattun hanyoyin sadarwa.
Don haka masu tsara kundin tsarin mulkin suka kirkiro tsarin wakilan zabe.
Ya sami karɓuwa a jihohin kudanci inda bayi ke da kaso mai yawa na yawan al'umma.
Ba su da ƴancin kaɗa ƙuri'a ba amma ana kidaya su a matsayin wani bangare na yawan al'ummar, wanda hakan ya baiwa jihohin kudanci gagarumintasiri.
Mece ce fa'ida ko akasin haka na tsarin wakilan zaɓe?
Fa'idoji:
- Ƙananan jihohi za su kasance da muhimmanci ga ƴan takara
- bai zame dole ga ƴan takara sai sun ziyarci duka jihohin da ke faɗin ƙasar ba
- suna iya mayar da hankali kan wasu jihohi masu muhimmanci
- Sake kidayar zaɓe zai zo da sauki saboda jami'an zaɓe na iya mayar da hankali kan inda aka sami akasi a kowace jiha
Rashin fa'ida:
- Wanda ya lashe adadin ƙuri'u mafi yawa na iya rashin nasara a zaɓen
- Wasu masu kaɗa ƙuri'a na ganin cewa ƙuri'unsu ba su da wani amfani
- ''Jihohi marasa tabbas'' na yin babban tasiri kan sakamakon zaɓen
Waɗanne jihohi ne ''marasa tabbas''?
Galibin jihohi sun kasance suna zaɓar jam’iyya ɗaya ce kowane zaɓe.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ƴan takarar shugaban ƙasa ke kai mayar da hankali kan wasu jihohin da za su iya sauyawa a kowane lokaci, inda kuri'a za ta iya tafiya ta kowace hanya maimakon ƙoƙarin samun nasara a kan masu jefa kuri'a a duk faɗin ƙasar.
A shekarar 2024, manyan jihohin da ke wannan matsayi su ne Arizona da Georgia da Michigan da Nevada da Pennsylvania da kuma Wisconsin.
Su wane ne wakilan zaɓe na bogi?
A shekarar 2020, masu kada ƙuri'a a Amurka suka fara sanin abin da ake kira "Wakilan zaɓe na bogi" bayan da ƴan jam'iyyar Republican masu goyon bayan Trump a jihohi bakwai na Amurka suka ƙirƙiro nasu wakilan zaɓen na daban a wani yunƙuri na juya sakamakon zaɓen.
A wasu lokuta, sun ƙirƙira tare da sanya hannu kan takardu masu kama da hukuma ko kuma sun isa manyan biranen jihohi a ranar 14 ga Disamba - lokacin da wakilan zaɓe a duk faɗin ƙasar suka hadu don kada ƙuri'unsu a hukumance.
Wasu daga cikin waɗanda ke da hannu a lamarin sun fuskanci tuhuma kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.











