Yadda tarkacen tauraron ɗan'adam ya faɗo daga sararin sama

Asalin hoton, ESA
- Marubuci, Jonathan Amos
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent
Wani tauraron ɗan’adam na Turai – wanda ya zama tsuhen binciken kimiyya a ɓangaren yanayi ya faɗo kan duniya.
Tauraron ɗan’adam ɗin da ake kira ERS-2 mai nauyin tan biyu, kusan ya ƙone ne ƙurmus a sararin samaniya ta yankin tekun Pacific.
Sai dai babu wanda ya iya ganin abin da ya faru da tauraron daga nan doron duniya.
ERS-2 na daga cikin tauraron ɗan’adam ɗin da Hukumar nazari kan sararin samaniya na Turai ta harba zuwa sama a shekarun 1990 domin yin nazari kan yanayin sararin samaniyar duniya, da ƙasa da kuma tekuna.
Haka nan tauraron ya samu damar yin nazari kan halin da lemar da ke kare duniya daga tsananin zafin rana ke ciki.
Dama dai a ranar Laraba aka yi hasashen faɗowar tauraron a kan doron duniya ta wani yanayin da masana ba za su iya sarrafa shi ba.
Tauraron ba ya ɗauke da na’urar da za a iya amfani da ita wajen sarrafa tafiyarsa.
Sai dai na’ura ta bibiyi yadda tauraron ya faɗo.
Hukumar nazari kan sararin samaniya ta Turai ta ce tauraron ɗan’adam ɗin ya ƙone a sararin samaniya da misalin ƙarfe biyar na yammacin Laraba a yankin Tekun Pacific na arewaci, tsakanin yankin Alaska da Hawaii, kimanin nisan kilomita 2,000 ta ɓangaren yammacin jihar California ta ƙasar Amurka.
Babu wata alamar da ta nuna cewa wani daga cikin tarkacen tauraron ya faɗo kan doron duniya.

Asalin hoton, ESA
ERS-2 ne na farko daga cikin tauraron ɗan'adam guda biyu da suka faɗo kan duniya.
Da farko dai yana kewaya duniya sama da kilomita 780, amma a shekarar 2011, injiniyoyi sun yi amfani da ragowar man da ya rage wajen rage girmansa zuwa kilomita 570.
An sa ran daga karshe sararin sama zai ja tauraron ɗan'adam ya lalata shi, wanda aka shirya zai faru kimanin shekaru 15.

Asalin hoton, AIRBUS
Da farko dai an yi tsammanin cewa ɓangarorin tauraron ɗan'adam ɗin waɗanda za su iya faɗowa kan duniya sun haɗa da fale-falensa da sauran abubuwan da aka haɗa da ƙarfe kamar tankunan man fetur da kuma eriyarsa.
Lokacin da aka harba ERS-2, akwai ƙarancin ƙa'idodi sarrafa tarkacen sararin samaniya, don haka dawo da tauraron dan'adam a cikin shekaru 25 na ƙarshen aikinsa yana iya samun karɓuwa.

Asalin hoton, HEO
SpaceX, wani fitaccen kamfanin Amurka, wanda ke gudanar da mafi yawan tauraron ɗan'adam masu aiki a halin yanzu a sararin samaniya, jimlar sama da 5,400.
Kwanan nan, SpaceX ta sanar da shirin faɗowar 100 daga cikin waɗannan taurarin dan'adam bayan gano kuskuren da ka iya haifar da matsala a nan gaba. Suna son cire kumbon ne kafin wata matsala ta taso.
A makon da ya gabata, gidauniyar Secure World Foundation da LeoLabs, wani kamfani da ke bin diddigin tarkacen sararin samaniya, sun jaddada mahimmancin kawar da tauraron dan adam a sararin samaniya. Sun yi nuni da cewa barin tsofaffin tauraron dan adam a sararin samaniya yana taimakawa wajen tara manyan abubuwa da ba a iya sarrafa su.
Gidauniyar ta ce waɗannan abubuwa suna haifar da babban hadari ga dubban sabbin tauraron dan adam da ake harbawa, wadanda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin sararin samaniyar duniya.

Asalin hoton, ESA











