An buɗe bincike kan 'yan wasan Italiya Sandro Tonali da Nicolo Zaniolo

Sandro Tonali na Newcastle da Nicolo Zaniolo na Aston Villa sun bar sansanin atisayen tawagar Italiya bayan an shaida masu cewa masu gabatar da kara na Italiya na gudanar da bincike kansu bisa al'amuran da suka shafi caca.

Hukumar ƙwallon ƙafar Italiya (FIGC) ta ce 'yan wasan ba su da kwanciyar hankalin da ya kamata su buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai na Euro 2024 da Italiya za ta yi guda biyu.

Hukumar FIGC ba ta fayyace dalilin binciken ba, amma kamfanin dillancin labaran Italiya ANSA ya ba da rahoton cewa yana da alaƙa da binciken yin cacan da ya shafi wasanni ba bisa ƙa'ida ba.

Labarin na zuwa ne kwana guda bayan da masu gabatar da ƙara na FIGC suka sanar da gudanar da bincike kan ɗan wasan tsakiyar Juventus Nicolo Fagioli mai shekara 22, wanda ake zargin ya yi amfani da wasu mutane daban-daban wajen yin caca a kan haramtattun shafukan caca da ke intanet.

Masu gabatar da ƙara daga Turin sun sanar da tsohon dan wasan tsakiyar Milan Tonali, mai shekara 23, da tsohon ɗan wasan Roma Zaniolo, mai shekaru 24 game da binciken ranar Alhamis.

A ranar Asabar ne Italiya za ta karbi bakuncin Malta kafin ta kara da Ingila ranar Laraba a rukunin C.