Garin da mabiya Sunna da 'yan Shi'a ke sallah a masallaci ɗaya

Ɗan Shia da Sunni na musabaha
Bayanan hoto, Syed Mazhar Ali Abbas shugaban ƴan Shia (hannun dama) a masallacin Pira da ake amfani da shi tare, da jagoran ƴan Sunni, Muhammad Shakeel - daga wani masallaci mai makwabtaka
    • Marubuci, Iftikhar Khan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service
    • Aiko rahoto daga, Northern Pakistan
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zaman tankiya tsakanin ƙungiyoyin addinin Islama ba sabon abu ba ne a yawancin ƙasashen Musulmi.

Yana ɗaya daga cikin abubuwa da suka janyo faɗa a baya-bayan nan a Syria, kuma kazamin artabu tsakanin ƴan Sunni da Shi’a na ƙaruwa a Pakistan.

Sai dai a arewacin Pakistan, akwai wani ƙauye da ya zama abin misali na yadda ɓangarorin biyu za su iya zama lafiya da juna.

Masallacin mai ɗan tsayi da kuma lasifikoki a samansa, shi ne abu na farko da matafiyi zai gani idan ya doshi ƙauyen Pira da ke lardin KhyberPakhtunkwha a arewa maso yammacin Pakistan.

Wuri ne da duka ɓangarori da ke zama a can ke koyi, ganin cewa ƴan Sunni da kuma Shi’a na amfani da masallacin a tsakaninsu.

Idan aka ji kiran sallah, al'ummomi guda suna yin sauri su shiga gida. Minti 15 bayan idar da sallarsu, suna fita zuwa kan tituna - yayin da ɗaya al'ummar kuma ta shiga nata sallah.

A cewar Syed Mazhar Ali Abbas, malami a masallaci, ya ce an fara yin haka ne tsawon shekara 100 da ta wuce, duk da cewa an sake gina masallacin - babu wanda ya ga dalilin sauya shi.

A rubuce, masallacin mallakin al'ummar Shi'a ne, sai dai duka ƙungiyoyin na biyan kuɗin lantarki da sauran abubuwa, kuma Mazhar Ali ya nanata cewa ƴan Sunni su ma suna da hakkin amfani da shi.

Kowanne daga cikinsu - Sunni da Shi’a na sallah yanda shari'a ta bayyana, sai dai kiran sallarsu ta bambanta, musamman idan aka duba da wanda yake kiran.

A cikin wata yarjejeniya da ba a rubuta ba, ƴan Shi’a ne ke kiran sallah da safe, rana da kuma yamma yayin da Sunni kuma ke yi da rana da kuma dare.

Sai dai a lokacin Ramadan, ƴan Sunni na fara buɗe-baki kafin Shi’a, don haka kiran sallar tsakaninsu ya bambanta da yamma a watan.

Waɗanda suka zo daga baya a cikin ƙungiya ta farko na bin ƙungiya ta biyu don yin sallah yadda suka saba tare da sauran.

Hoton saman masallacin Pira
Bayanan hoto, Masallacin da al'ummomin suke amfani da shi tare - ya kasance a matsayin wata alama ta haɗin-kai da ke haɗa Sunni da Shia wuri ɗaya.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai wasu masallatai da ke makwabtaka da Pira, sai dai wannan masallaci da Sunni da Shi’a ke amfani da shi tare ya fi kowanne girma.

Mutanen ƙauyen kusan 5,000, waɗanda suka haɗa ƴan Sunna da Shi'a - na rayuwa cikin farin ciki da juna - haka kuma suna da makabarta da suke amfani da ita a tare, wasu lokutan ma har da auratayya tsakaninsu.

Muhammad Siddiq, ɗan Sunni yana auren wata mata ƴar asalin Shi’a. Ya ce ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya shawo kan surukansa su amince da batun auren, sai dai ya ce ba don shi Sunni ba ne. Matsalar ita ce wai saboda zai aure ta don soyayya da ke tsakaninsu, wanda ba al'ada ba ne a Pakistan.

Ya ce aurensu ya kai tsawon shekara 18 yanzu kuma shi da matarsa na ci gaba da yin addininsu yadda ya dace.

Wani ɗan ƙauyen, Amjad Hussain Shah, ya ce a wasu gidaje iyaye suna kasancewa ƴan Shi’a yayin da ƴaƴansu kuma Sunni, ko iyaye Sunni sannan ƴaƴa kuma Shi’a.

"A nan mutane sun fahimci cewa imani da addini abu ne na daban," in ji shi.

Bukukuwan addini su ma suna sake haɗa kan mutanen.

Lokacin babbar sallah, Shi’a da Sunni na fita don murna tare - su kuma sayi dabba su yanke.

Idan ƴan Sunni suka zo murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammad SAW, a wani biki da suke kira milad, ƴan Shi’a na fitowa domin taya su tare a Pira, a cewar wani malamin Sunni a masallacin, Syed Sajjad Hussain Kazmi.

Haka ma, Sunni su ma suna halartar tarukan ƴan Shi’a lokacin watan Muharram, don tunawa da shahadar Imam Hussein, jikan Manzon Allah.

Ta haka ne, ƙauyawan ke murna da juna lokacin farin ciki da kuma alhini lokacin bakin ciki.

A ranar da BBC ta kai ziyara, dattijan ƙauyen na zaɓen shugaban kwamitin zakka na yankin, wanda ke da alhakin karɓa da kuma rarraba zakkar da aka bayar.

Ƴan Sunni ne ke rike da muƙamin a tsawon shekaru da dama, sai dai a wannan karon, ɗan Shi’a ne ya samu nasara.

Malamin Shi’a Mazhar Ali ya ce iyalansa sun mara wa ɗan takarar da ya sha kaye - wanda ya kasance Sunni.

"Ba mu taɓa mara wa wani ko kuma yi masa adawa a zaɓe saboda addini ba. Muna zaɓar mutumin da muka yi imanin zai yi wa al'ummar mu aiki," in ji shi.

Namiji da mace na tafiya riƙe da jakukkuna.
Bayanan hoto, A Pira, ba masallaci kaɗai ƴan Sunni da Shia ke amfani da shi a junansu ba, hatta auratayya ma suna yi, don samar da ƙauna da haɗin kai.

An taɓa yin wani yunkuri sau ɗaya tsawon shekara 20 da suka wuce na son janyo rarrabuwar kawuna - ba a ƙauyen Pira kaɗai ba, amma a ɗaukacin yankin da ya ke kunshe da ƙauyuka 11.

Yayin da ƴan Sunni da Shi’a ke zaune a ƙauyen Pira, sauran ƙauyukan cike suke da ƴan Sunni, sai dai wani ɗan takarar ɓangaren Shi’a Syed Hussain Shah, na fafatawa a zaɓe domin wakiltar dukansu a matakin karamar hukuma.

Ɗaya daga cikin abokan karawarsa ya yi ƙoƙarin bayyana lamarin.

"Sun kawo wani mutum daga Karachi wanda aka sani a faɗin ƙasar saboda irin yadda yake adawa da Shia. Ya gabatar da jawabai lokacin kamfen, inda ya buƙaci mutane kada su zaɓi ɗan takarar da ya fito daga ɓangaren Shia," in ji Munir Shah.

Hakan bai yi aiki ba. Mutane sun zaɓi Munir Shah.

"Yawancin mutane sun ce ba za su zaɓi malami ba, amma za su zaɓi wanda ya cancanta domin ya magance musu matsalolinsu - ba tare da duba daga wani ɓangare ya fito ba," in ji shi.

Ya yi imanin cewa masallacin da ɓangarorin biyu ke amfani da shi tare ne ya kawo haɗin kai tsakaninsu.

Masallata lokacin da suke yin sallah
Bayanan hoto, Masallata lokacin da suke yin sallah

Ta yaya suka fara amfani da masallacin a tsakaninsu?

Kusan shekaru 100 da suka wuce, yawan al'ummar Pira sun kasance mabiya Sufaye ƴan Sunni, waɗanda jikoki ne da suka fito daga wajen mutumin da ya kirkiro da ƙauyen a ƙarni na 17.

Sai dai wani masanin tarihi Dr Sibtain Bukhari ya ce sannu a hankali wannan zuri'ar ta sauya zuwa Shia. Sauran al'ummomin sun ci gaba da kasancewa Sunni - sai dai, dukkan ƙungiyoyin sun ci gaba da amfani da masallacin.

A shekarun 1980, wani jagoran ƴan Shia ya gabatar da buƙatar sake gina masallacin, inda wani malamin Sunni Molvi Gulab Shah ya amince amma da sharaɗin duka ɓangarorin za su ci gaba da amfani da masallacin.

Jagororin ɓangaren Shiar sun biya kuɗin aikin, inda masallacin ya zama nasu a hukumance - sai dai idan aka zo ibada ba haka batun yake ba, saboda abin da ake gani shi ne jajirtacciyar al'umma da ta haɗe kanta.