Arsenal na son Mendoza,Semenyo ya ja hankalin Man City

Rodrigo Mendoza

Asalin hoton, others

Bayanan hoto, Rodrigo Mendoza
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na zawarcin dan wasan kungiyar Elche na kasar Sfaniya Rodrigo Mendoza, mai shekara 20, wanda za ta sayar a kan fam fiye da miliyan 17. (Telegraph - subscription required), external

Manchester United na son ta dauko sabon dan wasan a bazarar badi amma ta na son dan wasanta Harry Maguire mai shekara 32 ya tsawaita kwantaraginsa a Old Trafford.(Teamtalk), external

Roma na sha'awar daukar dan wasan Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, aro daga Manchester United a watan Janairu. (Il Messaggero - in Italian), external

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya damu matuka a kan yadda suka dogara kan dan wasan Norway Erling Haaland, mai shekara 25, a dan haka ya fara tunanin fafatawa da Liverpool wajan zawarcin dan wasan Bournemouth watau Semenyo mai shekara 25. (Talksport), external

Nottingham Forest ta bayyana dan wasan Brighton dan kasar Ingila Jack Hinshelwood, mai shekara 20, a cikin 'yan wasan da ta ke son ta saya a kasuwa a watan Janairun badi . (Mail), external

West Ham na kokarin ganin ganin cewa dan wasan Jamus Niclas Fullkrug ya bar kungiyar a watan Janairu kuma tana son ta yi amfani da kudi da za ta samu daga siyar da dan wasan mai shekaru 32 a kan sabbin 'yan wasan guda biyu. (Florian Plettenberg), external

West Ham ta na da zabin daukar dan wasan Union Saint-Gilloise ,Promise David kuma za su iya sayan dan wasan mai shekara 24 dan Kanada kan fam miliyan 17 . (GiveMeSport), external

Sunderland da Brentford na zawarcin dan wasan AC Milan da Mexico Santiago Gimenez. (Calciomercato - in Italian), external

Kocin Everton David Moyes na son James Garner ya ci gaba da taka leda da su duk da cewa Manchester United da Aston na zawarcinsa .Villa da Nottingham Forest su ma su na sha'awar dan wasan mai shekara 24 (Talksport), external

AC Milan na son ta sake tattaunawa da golan Faransa Mike Maignan kan sabon kwantaragi ya yin da Juventus da wasu kungiyoyin firimiyar na son daukar dan wasan mai shekara 24 . (Gazzetta dello Sport - in Italian)