Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan tawagar Trump na da manufofin da suka ci karo da juna
Idan da gaske yanayin ma'aikata shi ke nuni da yanayin manufofi, to babu shakka mun fahimci abubuwa da dama a wannan makon game da yadda Donald Trump ke da niyyar yin mulki a wa'adinsa na biyu.
Fiye da manyan muƙamai 12, waɗanda wasu daga cikinsu za su buƙaci amincewar majalisar dattawa, sun ba da ƙarin haske game da tawagar da aka ba wa alhakin tafiyar da manufofinsa yayin da yake shirin komawa fadar White House.
A fuska dai akwai alamun abin da ya haɗa su - aminci ga shi shugaban.
Amma a ƙarƙashin ƙasa, akwai wasu manufofin da ke cin karo da juna.
Ga wasu ɓangarori huɗu waɗanda ke bayyana burin Trump da kuma yadda za su iya kawo wa shugabancinsa ƙalubale
Waɗanda ke daburta masu tasiri kan gwamnati
Su waye? : Matt Gaetz da Tulsi Gabbard da RFK Jr
Manufofinsu: Waɗannan mutanen guda uku sun kasance daga cikin manyan ƴan siyasa masu adawa da wasu manufofin Amurka, musamman a ƙarƙashin Shugaba Biden.
Zaɓar Gaetz a matsayin babban lauyan gwamnati shi ne zaɓin da Trump ya yi da ya fi janyo ce-ce-ku-ce.
Gaetz ya wakilci gundumar majalisa ta farko ta Florida tun 2017. Ya kammala karatun digiri ɗinsa a jami’ar William and Mary Law School, ya jagoranci cire ɗan majalisar California Kevin McCarthy a matsayin kakakin majalisar a watan Oktoban 2023.
Kwamitin ɗa’a na majalisar wakilai ya shiga bincike a kan zargin biyan kuɗi don yin jima’i da wata yarinya mai ƙarancin shekaru, da amfani da muggan ƙwayoyi da kuma almubazzaranci da kuɗaden ya ƙin neman zaɓe.
Ya musanta aikata ba daidai ba kuma ba a shigar da wata ƙara kan waɗannan zarge-zargen ba.
Tulsi Gabbard, wadda aka zaɓa a matsayin darektar ofishin leken asirin ƙasa ta Trump, tsohuwar soja ce wadda ta yi aiki da sashen lafiya a Iraki.
Tsohuwar ƴar majalisar wakilai ce ta jam'iyyar Democrat daga Hawaii wadda ta sauya sheka don mara wa Trump baya.
Gabbard dai ta saba adawa da manufofin ƙasashen ƙetare na Amurka, inda ta ɗorawa ƙungiuyar tsaro ta NATO alhakin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine da kuma ganawa da shugaban Syria Bashar al-Assad - sannan kuma ta nuna shakku kan rahoton leƙen asirin Amurka da ke zargin Assad da amfani da makamai masu guba.
Robert F Kennedy Jr, wanda Trump ya zaɓa don kula da ɓangaren lafiya, lauya ne kuma mai kula da muhalli. Ya kuma yaɗa bayanan da ke sukar alluran rigakafi da kuma tasirin fasahar sadarwa ta 5G.
Abin da muka fahimta:
Kamar Trump, Gaetz da Gabbard da Kennedy masu ƙalubalantar halin da ake ciki ne. Dukkansu uku a lokuta da dama sun aikata abubuwan da kamanceceniya da yaɗa bayanan makirci.
Da yiwuwa waɗannan suna cikin ƙwararan masu goyon bayan shirin Trump na daburta “waɗanda ke tasiri kan gwamnati”. Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ƙalubalanci wasu manufofi na musamman a kowane fanni da zai sa ido a kai – harkar tsaro da batun leƙen asiri da kuma lafiya.
Amma masu tayar da hayaniya na iya zama mabiya masu wuce gona da iri. Kennedy yana son ƙaƙaba tsauraran ƙa'idoji a fannin samar da abinci da noma, waɗanda za su iya cin karo da manufar gwamnatin Trump.
Ra'ayin Gaetz kan wasu batutuwa - yana goyon bayan halasta amfani da ganyen wiwi – lamarin da ba ya cikin tsarin jam’iyyar Republican.
Kuma Gabbard, mai tsananin sukar ikon Amurka, za ta yi aiki ga shugaban da ba ya tsoron amfani da shi - alal misali, kan Iran.
Masu tsaurin ra’ayi kan batun iyaka
Su waye? : Tom Homan da Stephen Miller da Kristi Noem
Manufofinsu:
Masu tsattsauran ra'ayi guda uku da aka ɗorawa alhakin aiwatar da tsare-tsaren Trump da suka jiɓanci iyakoki da shige da fice sun sha alwashin ƙarfafa tsaro tare da daƙile kwararar baƙin da ba su da takardun izinin ƙetara iyakar Amurka da Mexico.
A cikin gida, su - da kuma mafi yawan ƴan gwamnatin Trump mai shigowa - sun yi kira da a tashi tsaye kan korar baƙi, farawa daga kan waɗanda ake ganin suna barazana ga tsaron ƙasa ko ga lafiya da walwalar al’umma, da kuma komawa kan matakin tsaurara bincike a wuraren aiki wanda gwamnatin Biden ta dakatar.
Abin da muka fahimta :
Baya ga tattalin arziki, ƙuri'un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar akai-akai sun nuna cewa shige da fice da batun tsaron kan iyaka da Mexico su ne abubuwan da suka fi ɗaukar hankalin yawancin masu jefa ƙuri'a.
Yiwuwar ƙara yawan korar baƙi da kai hare-hare a wuraren aiki, na iya sanya Trump kan hanyar cin karo da jihohin da ke ƙarkashin jami’iyyar Democrat waɗanda za su iya yanke shawarar nuna turjiya a maimakon ba da haɗin kai.
Wasu jihohin Republican – waɗanda tattalin arzikinsu ya dogara, a wani ɓangare, kan aikin baƙin haure - na iya ƙin amincewa.
Masu mu’amalla da ɓangaren fasaha
Su waye?: Elon Musk da Vivek Ramaswamy
Manufofinsu:
Trump ya bayyana sunan mutumin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, a matsayin wanda zai jagoranci wani yunƙurin rage tsadar gudanar da al’amuran gwamnati inda aka ƙirƙiro wata sabuwar ma’aikata da aka yi wa laƙabi da ''Ma'aikatar Inganta Harkokin Gwamnati''
Zai gudanar da aikin ne tare da fitaccen mai saka hannun jari mai shekara 39 kuma ɗan siyasa Vivek Ramaswamy, wanda ya zama ɗan ga-ni-kashe-nin Trump bayan da ya sauka daga matsayin ɗan takara a jam'iyyar Republican.
Mutanen biyu suna daga cikin waɗanda suka fi janyo ce-ce-ku-ce a ɓangaren fasaha, ɓangaren da ya koma bin bayan Trump a wannan shekarar, tana neman zakara don daƙile zuzuta daidaiton siyasa tare da rungumar batun gwamnati madaidaiciya da rage yawan haraji da kuma taƙaita ƙa'idoji a ɓangaren kasuwanci.
Musk ya yi iƙirarin rage dala tiriliyan 2 cikin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, yana mai alƙawarin cewa zai “girgiza” ɓangarorin gwamnati.
Ramaswamy, wanda ya goyi bayan kawar da hukumar tattara haraji, IRS, da Ma'aikatar Ilimi, da sauransu, ya wallafa wani saƙo bayan sanarwar: inda ya ce "A rufe komai."
Abin da muka fahimta:
Naɗe-naɗen na nuni ne ga taimakon da Trump ya samu a lokacin yaƙin neman zaɓe daga Ramaswamy da Musk, inda Musk ya kwarara sama da dala miliyan 100 a asusun yaƙin neman zaɓen.
Amma lokaci zai nuna irin tasirin da wannan ɓangaren zai ci gaba da yi.
Duk da sunansa, sabuwar ma’aikatar ba hukuma ba ce. Hukumar za ta kasance daga wajen gwamnati don ba da shawara kan kashe kuɗi, wanda wani ɓangare ne da ke ƙarƙashin majalisa.
Trump, wanda ya samu giɓin kasafin kuɗi a wa'adinsa na farko, bai nuna alamun rage kashe kuɗaɗe ba.
Ya yi alƙawarin ƙyale ɓangaren jin daɗin al’umma da na lafiya (Medicare)- biyu daga cikin manyan wuraren kashe kuɗin gwamnati - ba tare da an taɓa su ba, wanda hakan zai iya kawo cikas a yunƙurin rage kashe kuɗaɗen.
Alƙawarin RFK Jr na haɓaka ƙa'idoji a fannin kayan sarrafa abinci na iya cin karo da burin Musk da Ramaswamy na rage tafiyar hawainiya a lamuran gwamnati.
Masu adawa da China
Su waye? : Marco Rubio da Mike Waltz da John Ratcliffe.
Manufofinsu:
Waɗannan mutanen za su gudanar da manufofin ƙasashen waje na "Amurka Farko" na Trump. Dukkansu masu adawa ne da China.
Rubio, wanda aka zaɓa a matsayin sakataren harkokin waje, na daga cikin masu sukar lamirin China, bayan da ya bayar da hujjar hana tafiye-tafiye kan wasu jami'an ƙasar ta China da kuma rufe ofisoshin kasuwanci na Hong Kong da ke Amurka.
Akwai yiwuwar su ukun za su goyi bayan alƙawarin da Trump ya yi na ƙara haraji kan kayayyakin da China ke shigowa da su Amurka.
Suna kallon Beijing a matsayin babbar barazanar tattalin arziki da tsaro ga Amurka. Waltz - wanda aka zaɓa a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tsaro - ya ce Amurka na cikin "Yaƙin cacar baka" tare da jam'iyyar gurguzu mai mulki.
Ratcliffe, wanda Trump ya naɗa a matsayin darektan hukumar CIA wanda ya yi aiki a matsayin babban jami'in leƙen asiri a wa'adinsa na farko, ya kwatanta fuskantar bunƙasar da China ke yi da yanƙurin da aka yi na durƙusar da tasirin Tarayyar Soviet.
Abin da Muka fahimta:
Duk da yake sau da yawa Trump yana nuna nasa tsattsauran ra'ayin tattalin game da China, shi ma ya ɗan yi kwan-gaba -kwan-baya wanda zai iya haifar da saɓani da manyan ƴan tawagarsa kan manufofin ƙasashen ƙetare.
A cikin wa'adinsa na farko, Trump ya ƙaddamar da yaƙin kasuwanci da Beijing (yunƙurin sassauta wannan lamari ya fuskanci tazgaro a lokacin ɓarkewar cutar Korona) kuma dangantakar ta ƙara yin tsami lokacin da ya yi wa cutar Korona laƙabi da "Cutar ƴan China".
Amma ya kuma yaba wa Shugaba Xi Jinping a matsayinsa na shugaba mai hazaƙa da ke mulki da "takalmin ƙarfe".
Wannan rashin tabbas ɗin na iya ƙara kawo cikas a yunƙurin daidaita dangantakar da ke da muhimmanci ga Amurka.
Rubio na iya cin karo da Gabbard, wanda Trump ya zaɓa a matsayin daraktan sashen leken asiri, wanda a baya ya soke shi kan manufofin ƙasashen waje, yana mai cewa "yana wakiltar ɓangaren da ke rura wutar yaƙi".