Zaɓen Ghana: Manyan alƙawurra huɗu da Bawumia da Mahama suka yi wa masu zaɓe

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Accra, Ghana
- Lokacin karatu: Minti 4
Kusan dai za a ce dukkannin ‘yantakarar guda 12 na da muradai masu kama da juna a fannin lafiya da tattalin arziki da ilimi da samar da ayyukan yi ga al’ummar kasa musamman matasa.
To sai dai an fi mayar da hankali kan alkawurran manyan ‘yantakarar guda biyu wato mataimakin shugaban kasa, Mahamudu Bamuwua na jam’iyyar NPP da tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahma na jam’iyyar NDC kasancewarsu gaba-gaba a takarar.
Ƙasar Ghana dai na cikin yanayin matsin tattalin arziƙi inda a yanzu haka take da nauyin bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 51.67, baya ga rashin aikin yi da kuma rashawa da cin hanci da suka yi wa ƙasar kakatutu.
Bisa waɗannan alƙawurra ne da manufofin 'yantakarar, masu zaɓe a Ghana kimanin miliyan 19 za su yi zaɓe su darje domin duk inda ka je tattaunawar da ake yi kenan.
Tattalin arziƙi
Yayin da Mahmudu Bawumia ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin Ghana ta hanyar rage amfani da garin kudi inda ya ce zai soke harajin da ake cirewa mutane idan suka yi hada-hadar kudi ta intanet da ake kira e-levy.
Shi kuwa John Dramani Mahma ya yi alkawarin dawo da martabar tattalin arzikin kasar ne ta hanyar tabbatar da gaskiya da rikon amana a kashe kudaden gwamnati da kuma yi wa babban bankin Ghana garanbawul.
To sai dai manufar da John Dramani Mahma ya fi shahara da ita ita ce ta tattalin arziki mai gudana na awa 24 ba tare da kakkautawa ba da ake kira 24 hour economic policy mai cike da takaddama.
"A duk lokacin da na yi magana kant sarin tattalin arziki maigudana a awa 24, akwai bukatar fahimtar dalilin wannan kudiri, za um samar da tattalin arzikin da zai samar mana da abinci da abin sha da magani da tufafin da muke bukata ta yadda za um magance matsalar hauhawar kudaden kasashen waje sakamakon shigo da kayan da ba a da bukatasu." In ji John Dramani Mahma na jam'iyyar NDC.
Shi kuma mataimakin shugaban Ghana, Mahamudu Bawumia ana yi masa lakabi da Mr Digital saboda irin tagomashin da yake bai wa harkar fasahar zamani.
"Idan har muna bukatar samun masu zuba jari to akwai bukatar bin tsari saboda haka ne muka rungumi tsarin digital domin yi wa tattalin arzikin Ghana garanbawul. A yanzu haka tsarin digital na tafiya a ƙasar nan." In ji Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP mai mulki.
Rashawa da cin hanci
Dangane kuma da yaki da rashawa da cin hanci, John Dramani Mahma ya ce zai bai wa hukumomi masu yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansu.
To amm Mahamudu Bawumia ya jaddada manufarsa ta mayar da hada-hadar kudade ta intanet domin rage sata da zamba da sauransu.
Dangane kuma da abin da ya shafi tsarin gudanarwa, dantakarar NPP ya ce zai yi wa kundin ƙasar na 1992 kwaskwarima domin tunkarar wasu matsaloli ciki har da rage kuɗaɗen da ake bai wa shugabanni da kuma rage wa shugaban kasa iko.
Shi ma John Dramani na jam’iyyar NDC ya sha alwashin yi wa kundin tsarin mulkin garambawul wajen rage kuɗaɗen da ake bai wa shugabanni da rage yawan masu muƙamin siyasa da kuma samar da daidaito a albashin dukkanin ma’aikatan gwamnati.
Samar da ayyukan yi
Wani ɓangaren na tattalin arziƙin shi ne samar da ayyukan yi inda Bawumia ya lashi takobin samar da sabbin guraben ayyuka ga matasa miliyan daya a fannin fasahar zamani.
Shi kuma John Mahma ya mayar da hankali wajen ganin an dama da ‘yan kasa a fannoni sadarwa da noma da hakar ma’adanai da masana’antu.
Ƙasar Ghana dai na fama da matsalar rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa sakamakon ficewar masu zuba jari saboda rashin tabbas kan tattalin arziƙin da kuma dogaro ga kayan da ake ƙerawa a ƙasashen waje.
Ilimi
A fannin ilimi kuma Mahamudu Bawumia ya ce zai bai wa fannin ƙirƙirarriyar basira da ta mutum-mutumi fifiko ƙari a kan ilimin sakandire kyauta na SHS da gwamnati mai ci ke bayarwa a kasar.
Sai dai John Dramani Mahma ya ce nasa tsarin a fannin ilimi zai karkata ne ga bai wa daliban da suka kammala karamar sakandire zabin babbar sakandiren da suke son shiga.
Sharhin masana
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Malam Bello Ɗan Rakiya masanin kimiyyar siyasa a birnin Accra, ya ce waɗannan manufofi na ƴantakarar guda biyu ne za su tasiri wajen zaɓen shugaban ƙasar a ranar Asabar mai zuwa.
Sai dai ya ce kowanne a cikin ƴantakarar na da makusa da abun yabo.
"Idan ka dubi Mahmudu Bawumiya za ka fahimci cewa akwa matsala inda yake batun amfani da digital wajen sauya tattalin arziƙin ƙasar Ghana.
Za mu iya mu tambaya me ya sa yanzu gwamnatinsu ba ta yi hakan ba tunda dai dole ana yi masa kallon cigaban gwamnatin Nana Addo duk da dai yana ƙoƙarin nesanta kansa da gwamnatin." In ji masanin.
Dangane kuma da Dramani Mahma, Ɗan Rakiya ya ce " shi kuma Mahma yana fuskantar suka daga jama'a dangane da wannan tsarin nasa na tattalin arziƙi mai gudana na awa 24 ba tare da ƙaƙƙautawa ba.
Mutane sun kasa fuskantar tsarin saboda kamar suna ganin tsari ne da zai wahalar da ƴan ƙasa.
Sannan wasu na ganin me ya sa ya nace sai ya dawo mulki? Ta yaya zai iya gyara tattalin arziƙin nan da wannan gwamnatin ta lalata a shekara takwas cikin shekaru hudu?." Ɗan Rakiya ya yi ƙarin haske.











