Dalilin da ya sa na yi calikanci a bidiyon London - Doguwa

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban masu rinjaye na majalisar Wakilan Najeriya, Hon Alhassan Doguwa ya shaida wa BBC cewa kaikomo tare da yin ƙwambo da aka ga yana yi a cikin wasu bidiyoyin da suka bayyana a soshiyal midiya, ya yi su ne domin aikewa da saƙo ga abokan hamayyarsa na siyasa.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC a birnin Landan, Alhassan Doguwa ya ce

"Na zo Landan a daidai wata gaɓa da nake son na aika wa ƴan siyasa wani saƙo musamman maƙiyanmu da suka mayar da siyasa ta koma gaba da ƙiyayya. Musamman ƴansiyasarmu na Doguwa da Tudunwada waɗanda ke siyasa idanunsu a rufe."

Saboda haka na zo Ingila ina yin waɗannan hotunan ne domin na yi walwala na wataya nuna wa ƴan jihar Kano maƙiyana da waɗanda suka fito daga Doguwa da Tudun Wada maƙiyana cewa gani dai ni ne dai wakilin Doguwa da Tudun Wada da an ƙi da an so Allah ya yarda, kuma ga ni a Ingila, to abu ne nake yin shi kamar wani cali-cali kuma saƙon ya je" in ji Doguwa.

Ɗan majalisar ya kuma yi ƙarin haske dangane da dalilin da ya sa ya rinƙa ƙwambo a cikin bidiyoyin.

"Ni ba baƙon zuwa London ba ne ko kuma ƙasashen wajen. Amma a wannan lokacin ne kawai na ga ya dace na aika wa maƙiya wannan saƙon su gan ni a kaikaice, su gan ni a tsaye, su gan ni ta gaba su kuma gan ni ta baya ga Alasan Ado ya gagari..."

..

Asalin hoton, Doguwa/Facebook

Ko Doguwa ba ya kunyar iyalinsa?

..

Asalin hoton, Doguwa/Grab

Da BBC ta tambayi Alhassan Doguwa cewa bisa la'akari da gogewarsa sannan kuma iyalinsa za su ga abin da yake, ko ba ya jin kunyar hakan? Sai ya ce:

"Su iyalaina ai sun halina. Sun san halina na barkwanci da tarairayar mutane. Saboda haka idan suka ga bidiyon za su yi dariya ne kawai saboda sun san cewa saƙo na aika."

"Ita ai siyasa wasanta ana buga shi daga tushe ne kamar yadda Bature ya ce "politics is always local. Ita siyasa ana yin ta ne ta dace da irin tunanin mutanen da ka fito daga cikinsu. Saboda haka yanzu ko dama aka ba ni zan yi magana da irin waɗannan mutanen to zan yi wadda ta dace da tunaninsu.

"Haka kuma idan aka ba ni dama ta magana kan al'amuran nutuswa kamar yadda aka ba ni dama na yi magana da Turanci a na wakilci Najeriya, ai ka ga yadda na yi ta Turanci."

Alhassan Ado Doguwa ya alaƙanta nasarorin da ya samu a rayuwa da irin dagewar da mahaifansa suka yi na ganin ya samu ilimi.

"Na gode wa iyayena da su kai ni makaranta na yi karatun zamani da na addini sannan kuma gogewata da duk wani mutumin da yake jin Turanci ta fi ƙarfin wani mutum ya yi min dariya. A yau ina alfahari ina cikin ƴan siyasa kaɗan daga jihar Kano da za su iya shiga ko'ina a jihar Kano su yi magana da Turanci ba tare da yadda za a yi musu dariya ba."

Me bidiyoyin suka ƙunsa?

..

Asalin hoton, Doguwa/Grab

A farkon makon nan ne waɗansu bidoyoyi na Alasan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya suka yi ta yawo a kafafen sada zumunta, inda aka yi sukar abubuwan da ya yi a cikin bidiyoyin.

A ɗaya daga cikin bidiyon, Hon Alhassan Doguwa ya sa ana ɗaukar sa a bidiyo yana karakaina daga bakin otal zuwa gindin fulawa yana riƙe da malafa da carbi yana taku ɗaiɗai.

A wani bidiyon kuma sai aka ga ɗan majalisar yana yawo a ɗakin otal ɗinsa inda har ya je ya ɗauki tufa ya gatsa yana ci.

Waɗannan bidiyoyin dai da alama ba su yi wa ƴan Najeriya daɗi ba musamman al'ummar jihar Kano, kasancewar yadda wasu daga wasu jihohin arewacin ƙasar da ke ƴar wasa da Kanawa suka rinƙa toskanar abokan nasu Kanawa cewa abin da ɗan majalisar daga jiharsu ya yi "ƙauyanci" ne.