Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta lallasa Afirka ta Kudu ta kai wasan ƙarshe a gasar cin kofin Afirka ta mata
Najeriya ta samu nasarar zura ƙwallo ta biyu gab da za a tashi wasa, lamarin da ya kawo ƙarshen mafarkin Afirka ta Kudu na kare kambinta, inda aka tashi Najeriya na da ci biyu Afirka ta Kudu kuma na da ɗaya.
Hakan ya sanya a yanzu tawagar matan Najeriya ta Super Falcons za ta buga wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata a ranar Asabar.
Najeriyar za ta kara ne da mai masaukin baƙi Morocco wadda tsallake rijiya da baya a karawarta da Ghana.
Najeriya ta fara zura ƙwallo a raga ne kafin tafiya hutun rabin lokaci ta ƙafar Rasheedat Ajibade ta hanyar bugun fenariti bayan an kama ƴar wasan Afirka ta Kudu Bambanani Mbane da laifin taɓa ƙwallo da hannu.
Sai dai masu riƙe da kambin sun farke ƙwallon bayan hutun rabin lokaci, su ma ta hanyar bugun fenariti, bayan an kama ƴar Najeriya Osinachi Ohale da laifin ƙeta.
Daga nan ne ƴar wasa Linda Motlhalo ta zura ƙwallo ɗaya tilo da ƴan Afirka ta Kudun suka ci a wasan.
Sai dai jim kaɗan gabanin kammala wasan a minti na 94, ƴar wasan Najeriya Michelle Alozie ta zura ƙwallo ta biyu a ragar Afirka ta Kudu, inda aka shafa fatiha.
Wannan wasa ne da ya ja hankali kuma ya yi armashi, ganin yadda dama wasa tsakanin ƙasashen biyu ke ɗaukar hankalin ƴan kallo a kowane lokaci idan suka haɗu.
Najeriya ta kayatar matukar gaske a gasar: Ta yi nasara huɗu, inda ta ci kwallo shida, kuma sai a wannan karawar ce aka zura mata ƙwallo ɗaya.
Wasan da ya fi kayatarwa ya kasance wanda Super Falcons ɗin suka lallasa Zambiya da ci 5-0.
Ƴan wasan Najeriya da suka fi haskawa a gasar sun haɗa mai buga baya Michelle Alozie da ƴar wasan tsakiya Rasheedat Ajibade, yayin da Esther Okoronkwo ta kasance wadda ta fi ba da kwallo a ci a gasar (ta bayar da kwallo uku aka ci) - tana kuma ci gaba da haskawa.
Morocco ta ragargaji Ghana
Morocco a nata ɓangaren ta kai wasan ƙarshe ne bayan ta yi nasara kan Ghana a bugun fenariti bayan an tashi canjaras - 1-1.
A lokacin da ake je bugun fenariti ne Morocco ta zura ƙwallo huɗu yayin da Ghana ta zura biyu.
Duk da cewa Morocco ta yi ƙoƙari a lokacin wasan amma ta ɓaras da damar zura ƙwallaye.
Hakan na nufin Morocco ta je wasan ƙarshe na gasar sau biyu a cikin shekara uku, inda a 2022 ta yi rashin nasara hannun Afirka ta Kudu a wasan na ƙarshe.
Tawagar ta Morocco ba ta taɓa lashe gasar ba, saboda haka wannan wata dama ce da ta samu idan za ta iya murƙushe tawagar Najeriya wadda ta lashe kofin har sau 9 kuma take harin na 10