Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon mai tsaron ragar Super Eagles ta Najeriya Peter Rufai ya rasu
Tsohon dan wasan Najeriya mai tsaron gida na kungiyar Super Eagles Peter Rufa’i ya rasu.
Kungiyar Super Eagles ta tabbatar da labarin rasuwar tasa, bayan shekara 61 a duniya.
Rahotanni sun ce golan ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Juli.
Labarin rasuwarsa na zuwa ne bayan na rasuwar dan wasan Liverpool da Diogo Jota sanadiyyar hatsarin mota.
Bayanai sun ce Peter Rufa’i ya shafe makonni yana fama da rashin lafiya kafin rasuwar tasa a wata asibiti da ke birnin Legas.
A sakon da ta wallafa a shafin sada zumunta, kungiyar Super Eagles ta yaba wa marigayin, sannan ta ce “ba za a taba mantawa da shi ba”.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ma NFF, wadda ita ma ta tabbatar da rasuwar marigayin, ta ce “tarihin da ya bari zai dade ba a manta da shi ba.”
“Abu ne na jimami,” in ji shugaban NFF Mohammed Sanusi, kamar yadda ya fada a Abuja.
“Muna rolon Allah ya yi masa rahama ya kuma bai wa na kusa da shi da kuma al’ummar Najeriya juriyar rashin,” in ji Sanusi.
Wane ne Peter Rufai?
Peter Rufa’i ya rasu ne yana da shekara 61 a duniya.
A lokacin da yake ganiya, Rufa’i shi ne mai tsaron raga na kungiyar Super Eagles a gasar cin kofin duniya ta 1994 da 1998.
Haka nan shi ne ya taimaka wa Najeriya ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka (AFCON) a 1994.
Ya shafe shekara 17 yana buga wa Najeriya wasa a kai a kai.
Peter Rufa’i ya fara buga wa Najeriya wasa ne a wani wasan sada zumunta a watan Disamban 1981.
Yana cikin tawagar Najeriya da ta zo ta biyu a gasar cin kofin Afirka a 1984 da 1988 kafin su samu nasarar lashe kofin a 1994 a Tunisia.
Haka nan Rufa’i ya taimaka wa Najeriya a gasar cin kofin duniya ta 1994 da kuma 1998 lokacin da Super Eagles ta kai zagsyen ‘yan 16.
Bayan daina wasa, Peter Rufa’i ya shafe wani bangare na rayuwarsa yana tallafa wa matasan da ke son shahara a fagen kwallon kafa.
Haka nan ya taba rike mukamin mai kula da taare-tsare na kungiyar kwallaon kafa ta Najeriya ta yan kasa da shekara 23.
Rufa’i ya yi wasa a kungiyoyi a kasashen Belgium, Netherlands, Portugal da Spain.