Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Najeriya shida da suka lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka
Ademola Lookman, shi ne ɗanwasan Najeriya na shida jimilla da ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na hukumar Caf a tarihi.
Lookman ya jinjina kyautar da aka ba shi ne a birnin Marrakech na Morocco a daren Litinin, kuma karo na bakwai kenan da ɗan Najeriya ke lashe ta.
Mai shekara 27 ɗin ya bi sawun Victor Osimhen, wanda ya ci kyautar a 2023, inda ya zama karo na biyu kenan da 'ɗan Najeriya ya karɓe kambin daga hannun ɗan Najeriya bayan Nwankwo Kanu (1996) da Victor Ikpeba (1997).
"Wannan babbar lamari ne kuma lokaci mai muhimmanci sosai," a cewar Lookman bayan ya karɓi kambin nasa. "Abin farin ciki ne shiga jerin ƙwararrun 'yan wasa da suka yi nasara sosai a wasan ƙwallo."
Duk da cewa Yaya Toure na Ivory Coast ya lashe kyautar har sau huɗu a jere, 'yan Najeriya ne suka fi yawa wajen lashe ta a tarihi.
Lookman mai buga wa Atalanta wasa a gasar Serie A ta Italiya ya bi sawun 'yan Najeriya biyar da suka yi nasarar lashe kyautar a tarihi tun daga 1992.
'Yan Najeriya da suka lashe kyautar:
- Rashidi Yekini - 1993
- Emmanuel Amunike - 1994
- Kanu Nwakwo - 1996
- Victor Ikpeba - 1997
- Kanu Nwakwo - 1999
- Victor Osimhen - 2023
- Ademola Lookman - 2024
Jerin 'yanwasan da suka lashe kyautar a tarihi:
2023: Victor Osimhen, Nigeria - Napoli (ITA)
2022: Sadio Mané, Senegal - Liverpool (ENG)
2021: Ba a bayar ba
2020: Ba a bayar ba
2019: Sadio Mané, Senegal - Liverpool (ENG)
2018: Mohamed Salah, Egypt - Liverpool (ENG)
2017: Mohamed Salah, Egypt - Liverpool (ENG)
2016: Riyad Mahrez, Algeria - Leicester City (ENG)
2015: Pierre-Emerick Aubameyang, Gabon - Borussia Dortmund (GER)
2014: Yaya Touré, Cote d'Ivoire - Manchester City (ENG)
2013: Yaya Touré, Cote d'Ivoire - Manchester City (ENG)
2012: Yaya Touré, Cote d'Ivoire - Manchester City (ENG)
2011: Yaya Touré, Cote d'Ivoire - Manchester City (ENG)
2010: Samuel Eto'o, Cameroun - Inter Milan (ITA)
2009: Didier Drogba, Côte d'Ivoire - Chelsea (ENG)
2008: Emmanuel Adébayor, Togo - Arsenal (ENG)
2007: Frédéric Kanouté, Mali - Sevilla FC (ESP)
2006: Didier Drogba, Côte d'Ivoire - Chelsea (ENG)
2005: Samuel Eto'o, Cameroun - FC Barcelona (ESP)
2004: Samuel Eto'o, Cameroun - FC Barcelona (ESP)
2003: Samuel Eto'o, Cameroun - Real Mallorca (ESP)
2002: El Hadji Diouf, Sénégal - Liverpool (ENG)
2001: El Hadji Diouf, Sénégal - Lens (FRA)
2000: Patrick Mboma, Cameroon - Parma (ITA)
1999: Nwankwo Kanu, Nigeria - Arsenal (ENG)
1998: Mustapha Hadji, Maroc - Deportivo La Coruna (ESP)
1997: Victor Ikpeba, Nigeria - AS Monaco (FRA)
1996: Nwankwo Kanu, Nigeria - Inter Milan (ITA)
1995: George Weah, Liberia - AC Milan (ITA)
1994: Emmanuel Amunike, Nigeria - Sporting Lisbon (POR)
1993: Rashidi Yekini, Nigeria - Vitória FC (POR)
1992: Abedi Pelé, Ghana - Olympique de Marseille (FRA)