Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fifa ta tabbatar Saudiyya ce za ta karɓi baƙuncin Kofin Duniya na 2034
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta tabbatar cewa ƙasar Saudiyya ce za ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya ta 2034.
Kazalika, ƙasashen Sifaniya da Portugal da Moroko ne za su haɗa gwiwa wajen karɓar baƙuncin gasar ta 2030, in ji hukumar.
Haka nan, za a buga wasanni uku a ƙasashen Argentina da Paraguay da Uruguay na gasar ta 2030 a matsayin bikin cikar gasar shekara 100 da farawa.
An tabbatar da waɗanda za su karɓi baƙuncin gasar biyu ne a babban taron Fifa ranar Laraba bayan kammala kaɗa ƙuri'a.
Duka mambobin Fifa 211 sun halarci taron da aka yi ta bidiyo, inda suka dinga kaɗa ƙuri'unsu ta hanyar yin tafi daga allon da ke nuna fuskokinsu.
Ƙasar Norway ta janye daga kaɗa ƙuri'arta kan baƙuncin gasar ta 2034 saboda tsarin kaɗa ƙuri'ar, ba don an bai wa Saudiyya ba.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam na zargin Saudiyya da amfani da harkokin wasanni wajen ɓoye take haƙƙin dan'adam a ƙasar ta hanyar zuba maƙudan kuɗaɗe a ɓangaren.