Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me kuke son sani kan Gasar Kofin Afirka ta Mata, Wafcon 2024?
An kusa fara Gasar Cin Kofin Afirka ta Mata (Wafcon), inda Morocco za ta karɓi baƙunci karo na biyu a jere.
Za a fara buɗe labulen wasannin daga ranar Asabar 5 ga watan Yuli, inda mai masauƙin baƙi, Morocco za ta fafata da Zambia a filin wasa na Olympic a birnin Rabat.
BBC Hausa za ta kawo muku sharhi da bayanan wasan farko tsakanin Morocco da Zambia da karawa tsakanin Mali da Tanzaniya da fafatawa biyu ta daf da ƙarshe da kuma wasan ƙarshe da za a yi ranar Asabar 26 ga watan Yulin 2025
Mai riƙe da kofin karo tara a tarihi, Najeriya tana cikin wasannin, wadda za ta fara kece raini da Tunisia a rukuni na biyu a makon farko.
Mai riƙe da kofin, Afirka ta Kudu za ta kara da Ghana a wasan farko a rukuni na uku ranar Litinin 7 ga watan Yuli.
To sai dai yaushe ne sauran ranakun wasannin? Wane tsari aka tanada a gasar? Yaushe za a fara wasannin cin kofin Afirka na mata a bana?
BBC ta tanadi dukkan abubuwan da ya kamata ku sani kan gasar ta 13 da za a buga a babbar harkar tamaular mata a Nahiyar Afirka.
Ya aka raba rukunonin gasar?
An raba tawagar 12 zuwa rukuni uku, inda kowane rukuni ke ɗauke da tawaga huɗu.
Mai masaukin baƙi Morocco tana da jan aiki a gabanta a rukunin farko, an kuma haɗa ta da Zambia, wadda ta doke a wasannin neman shiga Olympic 2024.
Haka kuma Atlas Lion za ta fuskanci Senegal da Jamhuriyar Congo, inda biyu ne za su kai zagaye na biyu a gasar.
Tawagar Najeriya na fatan kara lashe kofin, wanda rabonta da shi tun 2018, kuma ita ce kan gaba a taka leda a Afirka ta 36 a duniya.
Super Falcons za ta kece raini a rukuni na biyu da ya ƙunshi Tunisia da Algeria da kuma Botswana.
Rukuni na uku kuwa ya haɗa da mai riƙe da kofin, Afirka ta Kudu, wadda za ta fara fuskantar Ghana, sai kuma Mali, waɗanda za su yi wasannin a karo tun bayan 2018 da kuma Tanzania, wadda za ta buga gasar a karo na biyu tun bayan 2010.
Duk ƙungiya biyu da ta haɗa maki da yawa za ta kai zagayen gaba a kowanne rukuni da kuma biyu da suka sami maki mai yawa, amma suka kara a mataki na uku a cikin rukuni.
Rukunin farko: Morocco da Zambia da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo
Rukuni na biyu: Najeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana.
Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania.
Jadawalin gasar cin kofin Afirka Wafcon 2024 da lokutan da za a buga wasannin
Bayan karawar buɗe labulen gasar, aƙalla za a riƙa buga wasa bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli.
A lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT.
Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma'a 18 ga watan Yuli.
Filayen da za a buga gasar cin kofin Afirka Wafcon 2024
Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su, ba bu su daga cikin waɗanda za su karɓi bakuncin gasar bana.
Kasar dake Arewacin Afirka na ci gaba da yin tsare-tsare da gyare-gyare, wadda za ta karɓi bakuncin wasan cin kofin Afirka na maza da yin haɗakar gasar cin kofin duniya da za a buga a 2030.
Za a yi amfani da fili shida a birane biyar har da biyu a Casablanca:
- Olympic Stadium a birnin Rabat (Mai cin ƴan kallo 21,000)
- El Bachir Stadium a birnin Mohammedia (Mai cin ƴan kallo 15,000)
- Larbi Zaouli Stadium a birnin Casablanca (Mai cin ƴan kallo 30,000)
- Pere Jego Stadium a birnin Casablanca (Mai cin ƴan kallo 10,000)
- Honneur Stadium a birnin Oujda (Mai cin ƴan kallo 19,800)
- Berkane Stadium a birnin Berkane (Mai cin ƴan kallo 15,000)
Waɗanne ƙasashen ake hasashen za su lashe kofin
Daga tawaga 12 da za su buga gasar cin kofin Afirka a Morocco, Najeriya ce da Afirka ta Kudu ta taɓa ɗaukar kofin.
Super Falcons za ta fafata a wasannin karkashin koci, Justin Maduguwu.
Chiamaka Nnadozie daga Najeriya ita ce ta lashe ƙyautar fitatciyar mai tsaron raga a Afirka karo biyu, yayin da Asisat Oshoala za ta buga wasannin da ta dunga yin fice a baya.
Mai horar wa Desiree Ellis za ta yi kokarin kare kofin da yake hannun Banyana Banyana, wadda za ta buga karawar ba tare da Thembi Kgatlana, saboda wasu dalilai na gashin kai.
Haka ƴar wasan Afirka ta Kudu, Jermaine Seoposenwe tana taka rawar gani a Monterrey a Mexico da Hilda Magaia, waɗanda aka rabawa takalmin zinare a matakin kan gaba a cin ƙwallaye a Wafcon a 2022.
Morocco tana zuba hannun jari mai yawa a fannin ƙwallon kafa a ƴan shekaru da yawa, amma har yanzu tawagarta ta mata ta kasa ƙwaiƙwayon ta maza da ta taɓa taka matakin farko a taka leda a Afirka.
Sai dai Atlas Lionesses tana da mai horar wa Jorge Vilda, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Sifaniya a 2023.
Zambia ta kare a mataki na uku a gasar baya da aka yi, tana kuma tare da wadda ta yi fice a fannin taka ledar mata a Afirka a shekara, Barbra Banda, wadda ba ta buga gasar 2022 ba.
Mai taka leda a Orlando Pride tana kan ganiya, wadda take wasa tare da Racheal Kundananji, waɗanda suna daga cikin ƴan wasa huɗun da aka saya mafi tsada a tarihi.
Ita kuwa ƴar kasar Swistzerland, Nora Hauptel za ta ja ragamar Copper Queens a fatan da Ghana ke yi na lashe Wafcon karon farko a tarihi.
Bayan Najeriya da Afirka ta Kudu da suke da tarihin lashe gasar kofin Afirka, Ghana tana da kwarewar halartar wasannin da ta yi a 1998 da 2002 da kuma 2006.
Wasannin cikin rukuni
Asabar 5 ga watan Yuli
Rukunin farko: Morocco da Zambia, Olympic Stadium, Rabat (20:00) - Wasan da BBC za ta kawo sharhi da bayanai.
Ranar Lahadi 6 ga watan Yuli
- Rukunin farko: Senegal da Ivory Coast, El Bachir Stadium, Mohammedia (14:00)
- Rukunin na biyu: Najeriya da Tunisia, Larbi Zaouli Stadium, Casablanca (16:00)
- Rukunin na biyu: Algeria vs Botswana, Pere Jego Stadium, Casablanca (19:00)
Ranar Litinin 7 ga watan Yuli
- Rukunin na uku: Afirka ta Kudu da Ghana, Honneur Stadium, Oujda (16:00)
- Rukunin na uku: Mali da Tanzania, Berkane Stadium, Berkane (19:00) - wasan da BBC za ta kawo sharhi da bayanai kai tsaye.
Ranar Laraba 9 ga watan Yuli
- Rukunin farko: Zambia da Senegal, Mohammedia (16:00)
- Rukunin farko: Jamhuriyar Congo da Morocco, Rabat (19:00)
Ranar Alhamis 10 ga watan Yuli
- Rukunin na biyu: Botswana da Najeriya, Larbi Zaouli Stadium, Casablanca (16:00)
- Rukunin na biyu: Tunisia da Algeria, Pere Jego Stadium, Casablanca (19:00)
Ranar Juma'a 11 ga watan Yuli
- Rukunin na uku: Ghana da Mali, Berkane (16:00)
- Rukunin na uku: Tanzania da South Africa, Oujda (19:00)
Ranar Asabar 12 ga watan Yuli
- Rukunin farko: Morocco da Senegal, Rabat (19:00)
- Rukunin farko: Zambia da Jamhuriyar Congo, Mohammedia (19:00)
Ranar Lahadi 13 ga watan Yuli
- Rukunin na biyu: Najeriya da Algeria, Larbi Zaouli Stadium, Casablanca (19:00)
- Rukunin na biyu: Tunisia da Botswana, Pere Jego Stadium, Casablanca (19:00)
Ranar Litinin 14 ga watan Yuli
- Rukunin na uku: Afirka ta Kudu da Mali, Oujda (19:00)
- Rukunin na uku: Ghana da Tanzania, Berkane (19:00)
Zagayen kwata fainal a Wafcon 2024
Ranar Juma'a 18 ga watan Yuli
Kwata fainal na farko: Wadda ta yi ta ɗaya a rukunin farko da ta farko a rukuni na uku ko wadda ta yi ta uku a rukuni na biyu, za su yi wasa a Rabat
Kwata fainal na biyu: Wadda ta yi ta farko a rukuni na biyu da wadda ta yi ta biyu a rukunin farko, za su kece raini a Larbi Zaouli Stadium a Casablanca.
Ranar Asabar 19 ga watan yuli
Kwata fainal na uku: Wadda ta yi ta farko a rukuni na uku da ta ɗaya a rukunin farko ko wadda ta kare a mataki na uku a rukuni na biyu, za su kara a Oujda
Kwata fainal na huɗu: Wadda ta yi ta biyu a rukuni na biyu da wadda ta kare a mataki na biyu a rukuni na uku, za su yi wasa a Berkane
Wasannin daf da ƙarshe a Wafcon 2024
Ranar Talata 22 ga watan Yuli
Wasan daf da karshe na farko: Wadda ta ci zagayen kwata fainal a wasan farko za ta fuskanci wadda ta yi nasara a zagayen kwata final karawa ta huɗu, za su kara a birnin Rabat.
Wasan daf da karshe na biyu: Wadda ta lashe zagayen kwata fainal wasa na biyu da wadda ta yi nasara a karawar kwata fainal na uku, za su kece raini a Larbi Zaouli Stadium a Casablanca.
Wasan neman mataki na uku da na huɗu
Ranar Juma'a 25 ga watan Yuli
Wadda ta yi rashin nasara a daf da karshen farko da wadda aka doke a zagayen daf da karshe wasa na biyu, za su fafata a Larbi Zaouli Stadium a birnin Casablanca.
Wasan ƙarshe na Wafcon 2024
Ranar Asabar 26 ga watan Yuli
Wadda ta lashe wasan farko na daf da karshe da wadda ta yi nasara a daf da karshe na biyu, inda za su fafata a Olympic Stadium a birnin Rabat.