Barca da Atletico na hammaya kan Senesi, Man Utd na sa ido kan Diomande

Asalin hoton, @futbolarena
Barcelona da Atletico Madrid na hamayya kan ɗanwasan baya na Bournemouth da Argentina Marcos Senesi, mai shekara 28, wanda ya sanar da ƙungiyarsa cewa zai tafi a 2026. (Teamtalk)
Manchester United na sa ido kan matashin ɗanwasan gaba mai shekara 19 Yan Diomande, na Ivory Coast wanda RB Leipzig ke neman fam miliyan 80. (Talksport)
Har yanzu Manchester United ba ta tattauna da Atletico Madrid ba kan ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekara 25 Conor Gallagher. (Mail - subscription required)
Manchester United za ta jinkirta sayar da ɗanwasanta Joshua Zirkzee yayin da take fama da masu rauni da kuma gibin ƴanwasan Afrika da suka tafi gasar cin kofin nahiyar. (ESPN)
Liverpool na sa ido kan ɗanwasan gaba na Brentford Igor Thiago, mai shekara 24, yayin da ƙungiyar ke ƙoƙarin ƙara ƙarfin gabanta. (CaughtOffside)
Newcastle da Nottingham Forest da Crystal Palace na ribibin ɗanwasan baya na Ajax mai shekara 22 Youri Baas. (Teamtalk)
Arsenal na son ɗanwasan baya na AC Milan da Italiya, Davide Bartesaghi, mai shekara 19 wanda ke taka rawar gani a Seria A. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Bayern Munich na sa ido kan ɗanwasan Cardiff Dylan Lawlor. wanda zai cika shekara 20 a 1 ga Janairu. (Talksport)
Chelsea da Arsenal da Newcastle dukkaninsu sun nuna suna son ɗanwasan tsakiya na Marseille da Faransa Darryl Bakola, mai shekara 18. (Footmercato - in French)
Rennes na nazarin karɓo aron ɗanwasan tsakiya na Manchester City da Argentina mai shekara 19 Claudio Echeverri, kodayake Villarreal da Girona na hamayya kan ɗanwasan. (Ouest-France - in French)











