Haaland zai ga ƙwararren likita saboda rauni a ƙafarsa

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaban ƙungiyar Manchester City, Erling Haaland zai ga ƙwararren likita saboda raunin da ya ji rauni a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta buga da Bournemouth a ranar Lahadi.
Sai dai ƙungiyar ta ce tana sa ran zai warware ya cigaba da taka leda a wannan kakar da ake ciki.
Ɗanwasan na ƙasar Norwey bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti 61 da fara wasan bayan ya farke ƙwallo ɗaya, kafin daga bisani City ta doke Bournemouth da ci biyu da ɗaya domin zuwa wasan kusa da ƙarshe.
Man City ta ce tana fata ɗanwasan zai warware, domin ƙarasa wasannin wannan kakar da ake ciki.
Ƙungiyar ta ce an yi wa Haaland, wanda ya zura ƙwallo 30 wasa 40 zuwa yanzu gwaje-gwaje, kafin aka tura shi ganin ƙwararren likita.
Haaland ya ɓarar da bugun fanareti a farkon wasan, kafin ya ci ƙwallo ɗaya kafin ya fita daga wasan.
Kofin FA ne kaɗai ya rage da ake ganin Manchester City za ta iya lashewa a kakar bana.







