Dalilai huɗu da ke haifar da rashin sha'awa tsakanin ma'aurata

Wasu ma'aurata kance a kan gado

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Raguwar sha'awa tsakanin ma'aurata wata matsala ce da ke neman zaman ruwan dare.

Hukumar Lafiyar Birtaniya, ta bayyana raguwar sha'awa matsala ce da ke shafar aya cikin maza biyar, haka ma tana shafar matan.

Akwai dalilai masu yawa da ke haifar da matsalar da suka haɗa da damuwa da kai wasu yanayi na rayuwa, kamar juna-biyu da haihuwa da kuma shayarwa.

Raguwar sha'awa tsakanin ma'aurata ba wata matsala ce a za a tashi hankali a kanta ba.

To amma ci gaba da ƙaruwar matsalar ka iya haifar da matsala, don haka yana da kyau ka binciki abin da ke haddasa maka matsalar.

"Da farko yana da muhimmanci ka san yanayin yadda sha'awarka da ta ragu,'' a cewar Catarina de Moraes, sakatariyar ƙungiyar likitocin jima'i da ƙwaƙwalwa ta Brazil.

Ta ƙara da cewa, "A wasu lokutan akwai ruɗarwa tsakanin rashin sha'awa da gamsar da juna a lokacin kwanciya da kuma raguwar sha'awa''.

Diego Fonseca, masanin mu'amalar aure ya ce kafin a tabbatar da cewa mutum na fama da matsalar raguwar sha'awa, dole sai ya shafe wata shida yana fama da matsalar.

Haka ma, Ribeiro Marisca, ƙwararriya a asibitin mata, ta yi imanin cewa ''bambamcin ya bambanta daga mutum zuwa mutum, ya danganta da halin da kowane marar lafiya ke ciki.''

Ta hanyar tattaunawa da masana, mun gano wasu dalilai huɗu da ke hadadsa raguwar sha'awa.

1. Samun sauyi a harkokin yau da kullum

Ma'aurata rungume da juna

Asalin hoton, Getty Images

A wasu lokuta akwai dalilai na bai ɗaya da ke haifar da matsalar, kamar gajiya da ƙaruwar tashin hankali da damuwa.

Haka ma akwai sauye-sauyen ayyukan yau da kullum tare da sauyawar lokacin da aka saba saduwar aure.

Sannan wata matsalar ita ce kula da yara.

A cewar Catarina de Moraes, "Idan kuka samu raguwar sha'awa saboda wani dalili, hakan ya nufin sha'awarku ta ragu.

A wasu lokutan sabawa da saduwa da mace guda ɗaya tsawon lokaci kan haifar da raguwar sha'awa.

Ya ƙara da cewa koda sha'awarku ta ragu, bai kamata ku damu ba, in dai kun samun gamsuwa a lokacin da kuka sadu.

"Haka ma, za ku kasance masu ƙarfin sha'awa, idan kun samu gamsuwa da juna kuma sha'awar ku yana raguwa, to ba ku buƙatar kowane irin gwaji."

2. Matsalar ƙwaƙwalwa

Wani miji na rarrashin matarsa

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar ƙwaƙwalwa, kamar damuwa da baƙin ciki na taka rawa wajen raguwar sha'awa.

A cewar likitan ƙwaƙwalwar, ''masu fama da lalurar damuwa da rashin daidaiton ƙwaƙwalwa, wanda shi ke haifar da matsalar shiga yanayin damuwa ka iya haifar da matsalar raguwar sha'awa.

Ya ƙara da cewa, "shan magani a wasu lokutan kan taimaka wajen ƙara sha'awa tsakanin ma'aurata."

A gefe guda kuma, wasu magungunan rage damuwa da zaƙuwa na shafar ƙarfin sha'awar mutum.

3. Sauyin sinadarin halitta

Mace sanye da jan tufafi ta dafa kafaɗar mijinta

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan mutum ba shi da matsalar ƙwaƙwalwa, kuma bai samu sauyi a harkokinsa na yau da kullum da zai sa ya samu matsalar raguwar sha'awa ba to wataƙila ya samu sauyi a sinadaran jikinsa.

Dr. Caroline Castro, masanin mu'amalar aure a asibitin São Camiro Hospital, ya ce sinadaran motsa sha'awa na maza da mata na iya haifar da matsalar.

Sinadaran Estrogen da ke tayar da sha'awar mata na da alaƙa da ƙwayoyin halittar gado da ni'ima a al'aurar mata da kuma jin daɗin rayuwa.

Haka shi ma sinadarin Testosterone na taimaka wa wajen samar da maniyyi, da sha'awar jima'i wanda kai-tsaye yake shafar lafiyar ƙwaƙwalwa, tare da ƙara sha'awa.

A cewar Diego Fonseca, gano matsalar a irin wannan yanayi na da tsauri sosai.

"Alal misali a maza, mukan duba ko yana fama da ƙarancin sinadarin testosterone. Mukan duba ko yana da wata rashin lafiya da ke haifar da sauyin sinadarai.''

Likitocin kuma kan duba wasu dalilan kamar juna biyu da shayarwa da ajiye teɓa da ka iya haddasa sauye-sauye a sinadaran halitta.

4. Wasu cutuka da mutum ke fama da su

Wani mutum riƙe da ƙwaya mai launin shuɗi

Asalin hoton, Getty Images

Akwai kuam wasu cutuka da mutane ke fama da su da ke haddasa matalar raguwar sha'awa, kamar yadda likitoci suka yi bayani.

Alal misali cutukan ƙwaƙwalwa kamar cutar laka da shanyewar ɓarin jiki da sauransu sukan shafi raguwar sha'awar mutum.

Haka ma cutar ciwon siga kan haddasa raguwar sha'awar mutum.

Sannan masu fama da cutukan da suka shafi zuciya ka iya fukantar matsalar raguwar sha'awa, sakamakon kasa buga jinin da jiki ke buƙata.

Haka kuma shan magungunan cutukan da suka shafi zuciya kan haifar sa matsalar.

Ta yaya za a kauce wa matsalar?

mata da miji riƙe da hannu

Asalin hoton, Getty Images

BBC ta tattauna da likita domin jin ta bakinsa, inda ya ce babu wani ƙayyadajjen maganin da za a sha domin magance matsalar raguwar sha'awa.

Akwai matsaloli da dama da ke haifar da ita, sannan kuma maganin matsalar ya danganta da abin da ya haifar da ita ga mutum.

Duka likitocin sun shawarci ma'aurata su tattaunawa da junansu dangane da dalilin da ke haifar musu da matsalar rashin sha'awar

Diego Fonseca ya ce "Yana da kyau a tattauna da juna kan batun, duk da cewa wani a cikinsu ba zai a hakan ba, tattaunawa za ta taimaka wajen warware wasu saɓani da matsalar ta haifar. Tattaunawa za ta ba ku dama ku fahimci halin da kowanenku ke ciki.''