Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas da Isra'ila ta kashe?

Asalin hoton, EPA
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kisan jagoran ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, IDF ta ce dakarunta sun kashe Mista Sinwar a wani hari da suka kai kudancin Gaza ranar Laraba.
"An kashe Yahya Sinwar ne bayan ya kwashe aƙalla shekara guda yana ɓuya cikin fararen hula a Gaza, a cikin hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da Hamas ta gina da kuma saman tudu a Zirin Gaza,'' in ji sanarwar sojojin.
Sojojin na Isra'ila sun ce sun tsananta hare-hare a kudancin Gaza bayan samun cikakkun bayanan sirri '' da suka ƙunshi bayanan wuraren da manyan shugabannin Hamas ke ɓoye.
''Sojojin Isra'ila da ke aiki a yankin sun ''gano tare da kashe wasu mutum uku, kuma bayan zuzzurfan bincike an tabbatar da cewa ɗaya daga cikin Yahya Sinwar ne'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Sanarwar IDF ɗin na zuwa ne jim kaɗan bayan da ministan harkokin wajen ƙasar, Israel Katz, ya shaida wa takwarorinsu labarin kisan jagoran na Hamas.
Mista Katz, ya bayyana Sinwar a matsayin wanda ya ''kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023' da Hamas ta ƙaddamar cikin Isra'ila da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 250.
Ministan ya ƙara da cawa mutuwar Yahya Sinwar ''wani gagarumin ci gaba ne ga Isra'ila da sojojinta kan abin da ya kira ''yaye wa duniya miyagun ayyukan masu iƙirarin jihadi da ke samun goyon bayan Iran''.
"Kisan Sinwar zai buɗe ƙofar gaggauta sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza, da kuma buɗe hanyar samar da cikakkiyar Gaza ba tare da Hamas ko hannun Iran ba'', in ji ministan.
Wane ne Yahya Sinwar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Sinwar a sansanin 'yan gudun hijira da ke Khan Younis a cikin Gaza a 1962.
Shekara ɗaya bayan kafa Hamas a 1987, ya kafa sashen tsaron ƙungiyar, wanda ya dinga kai farmaki ga masu haɗa kai da Isra'ila a cikin Falasɗinawa.
Isra'ila ta kama Sinwar sau uku a baya. An yanke masa ɗaurin rai da rai har sau huɗu a 1988 saboda kitsa garkuwa da kuma kashe Isra'ilawa biyu da kuma kashe Falasɗinawa huɗu.
Sai dai kuma a 2011, yana cikin Falasɗinawa 1,027 da Isra'ila ta saki a matsayin musayar sojanta da Hamas take tsare da shi a Gaza tsawon shekara biyar.
Ya koma Hamas a matsayin babban jagora kuma aka naɗa shi shugaban sashen siyasa a Gaza a 2017.
A 2015, Amurka ta saka Sinwar cikin baƙin littafinta na "yan'ta'addan duniya".
Ba a taɓa ganin Sinwar ba tun bayan fara yaƙin na watan Oktoba.
A watan Agustan da ya gabata ne aka ayyana Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaban Hamas bayan kisan tsohon jagoran ƙungiyar, Ismail Haniyeh a birnin Tehran.











