An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh a Tehran

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar Hamas ta ce an kashe shugaban ta Ismail Haniyeh a birnin Tehran na Iran.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar yau da safe ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da yake domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.
Ƙungiyar falasɗinawan mai riƙe da iko a Gaza ta ce Isra’ila ce ta kashe shugaban nata, Ismail Haniyeh, yayin da yake halartar rantsar da sabon shugaban Iran.
Ƙungiyar Hamas ta bayyana kisan a matsayin babban laifi wanda martanin sa ba zai zo da daɗi ba.
Ta kuma ce Isra’ilan ta kashe ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar Haniyeh, a lokacin samamen da ta kai.
Hamas ta kuma yi ta’aziyya ga Falasdinawa da Larabawa da kuma Musulman duniya da kuma a kan rashin jagoran nata.
Mafi yawan shugabannin ƙungiyar Hamas dai ba su fitowa fili su bayyana kansu, yayin da a gefe guda kuma, duk waɗanda suka bayyana kansun to za su gama rayuwar su ne suna wasan boyo da Isra’ila, mai neman rayuwar su ruwa a jallo.
Kafin wannan lokaci dai ana dai ganin Ismail Haniyeh a matsayin babban jagoran kungiyar Hamas, kuma yana cikin kungiyar tun daga 1980.
Ya taɓa zama firaiministan Falasɗinawa na ƙanƙanin lokaci a 2006, amma daga baya aka sauke shi bayan Hamas ta ƙwace mulkin Zirin Gaza daga hannun jam’iyyar Fatah.
A 2017 aka zaɓe shi shugaban ɓangaren siyasa na kungiyar kuma bayan shekara ɗaya Amurka ta sanya sunansa a cikin ƴan ta’addan da ta ke nema ruwa a jallo.
Ya shafe shekaru yana zaune a Qatar.
Isra’ila ba ta fitar da sanarwa a game da wannan batun ba kawo yanzu, amma ministan al’adunta ya wallafa a shafinsa na X cewa ‘’kisan Haniyeh za ta tsaftace duniya’’
Hamas dai ta sha alwashin ɗaukar fansa.
Wane ne marigayi Ismail Haniyeh?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ismail Abdel Salam Haniyeh, wanda ake yi wa laƙabi da Abu Al-Abd, an haife shi ne a sansanin ƴan gudun hijira.
Shi ne shugaban harkokin siyasa na ƙungiyar Hamas kuma ya zama firaiministan gwamnatin Falasɗinawa ta goma.
Ya riƙe muƙamin firaiminista ne a shekarar 2006.
Isra’ila ta garƙame shi a gidan yari na tsawon shekara uku a shekarar 1980, inda bayan nan ne ya yi gudun hijira zuwa Marj al-Zuhur, wani yanki da ba ya ƙarƙashin ikon kowa da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon.
Ya zauna a yankin tare da wasu shugabannin Hams a cikin mawuyacin hali.
Bayan shekarar ɗaya yana gudun hijira, ya koma Gaza, inda a shekarar 1997 aka naɗa shi a matsayin shugaban ma’aikata na babban malamain ƙaungiyar Hamas, Sheikh Ahmed Yassin, lamarin da ya ƙara masa gogewa a harkar mulki.
An naɗa shi muƙamin firaiminista ne a ranar 20 ga watan Fabarairun 2006.
Bayan shekara ɗaya a kan muƙamin, shugaban hukumar tafiyar da yankin Falasɗinawa, Mahmoud Abbas ya sauke shi daga kan muƙamin, bayan da dakarun Izz al Din al-Qassam suka ƙwace iko da Zirin Gaza, inda suka kori wakilan ƙungiyar Fatah, bayan wani artabu da aka yi na tsawon mako ɗaya.
Haniyeh ya yi watsi da tsige shi daga kan muƙamin, tare da bayyana matakin a matsayin wanda ya “saɓa wa doka”.
Kuma tun daga wancan lokacin Haniyeh ya sha yunƙurin ganin an sasanta tsakanin Fatah da Hams.
An zaɓe a matsayin shugaban ɓangaren siyasa na Hamas ne a ranar 6 ga watan Mayun 2017.
A shekarar 2018 kuma Amurka ta ayyana Haniyeha matsayin ɗan ta’adda.










