Yadda shugabannin duniya suka cika fadar Vatican a jana'izar Fafaroma Francis

Lokacin karatu: Minti 5

Shugabannin ƙasashen duniya da sarakuna sun cika birnin Vatican domin shaida jana'izar Fafaroma Francis.

Daga cikin fitattu a dandalin St Peter da safiyar ranar Asabar akwai Yarima William na Birtaniya da shugaban Amurka Donald Trump da wanda ya gada, Joe Biden da Firaiministan Birtaniya Sir Keir Starmer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Halartar shugabannin na zuwa ne a daidai lokacin da diplomasiyyar duniya ke cikin garari, yayin da Trump ya gana da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky gabanin fara jana'izar.

Ko ya zaman ya kasance tsakanin manyan mahalartan?

Kujeru goma ne tsakanin Trump da Zelensky

Trump na sahun gaba dab da akwatin gawar, kusa da matarsa Melania daga tsallaken inda Macron da matarsa Brigitte suke zaune.

Abin mamaki yadda Trump da matarsa Melania suka zauna tsakanin magoya bayan Ukraine.

Shugaban Estonia Alar Karis na daga hannun hagun ɗin Melania yayin da Alexander Stubb na Finland ke zaune daga ɓangaren hannun daman Trump.

Estonia da Finland dukkansu magoya bayan Zelensky ne wanda fuskarsa ke cike da alhini a Vatican, kuma yana zaune ne layi ɗaya da Macron yayin da wasu manyan baƙi suke tsakaninsu.

Zelensky wanda ke tattauna batun yarjejeniya da Trump a baya-baya nan ya zauna a layi ɗaya tare da Trump amma akwai kujeru goma a tsakaninsu.

Gabanin taron an ga yadda shugabbannin biyu suke tattaunawa tsakanisu.

Fadar White House ta bayyana tattaunawar ta minti 15 a matsayin mai amfani sannan Zelensky ya ce akwai yiwuwar ganawar tasu zata zama tarihi.

Shirin zaman

An ware manyan baƙi daga dubban mutanen da suka cika birnin Rome saboda jana'izar.

Manyan mutane na zaune a gefen dama a dandalin St Peters kusa da Basilica

Waɗanda aka bai wa kujerun alfarma sun haɗa da, shugaban ƙasar Argentina, Javier Milei da Firaiministar Italiya, Giorgia Meloni da shugaban ƙasar Italiya, Sergio Mattarella wanda ya wakilci ƙasar da ta kewaye birnin Vatican.

Daga bayansu kuwa sauran shugabanni ne da wakilai da aka ajiyewa kujeru daidai da haruffan sunayensu a harshen Faransanci.

Wakilin Masarautar Birtaniya Yariman Wales.

Starmer ya zauna a layi na biyar tare da matarsa Victoria.

Shugaban Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus zaune daga bayan Firaiministan Birtaniya

Tsohon shugaban Amurka Joe Biden tare da matarsa Jill. Ya zauna a layi na huɗu daga bayan Trump.

Shugabannin Turai da Sarakuna

Shugabanni da Sarakunan Turai da dama sun halarci jana'izar da aka gudanar a fadar Vatican.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen na tattaunawa da Macron.

Sauran Ƴan Siyasa da sarakuna da suka halarci Jana'izar Fafaroma sun haɗa da:

Shugaban Poland Andrzej Duda

Shugaban Jamhuriyar Dominican Luis Abinader

Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier

Shugaban Croatia Zoran Milanovic

Shugaban Ecuador Daniel Noboa

Firaiministan Ireland Taoiseach Micheál Martin

Shugaban Moldova Maia Sandu

Shugaban Latvia Edgars Rinkevics

Firaiministan New Zealand Christopher Luxon

Sarkin Sweden Carl na goma sha shida da Sarauniya Silvia

Sakatare Janar naMajalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres

Sarauniya Mary ta Denmark

Sarkin Jordan Abdullah na biyu da sarauniya Rania

Shugaban Hungary Tamas Sulyok da firaiminista Viktor Orban

Shugabar Majalisar Turai Roberta Metsola