Ƙasashe huɗu da suka sauya yadda za su bai wa ƴan Najeriya biza

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta buƙaci Amurka da ta sake yin duba dangane da sabbin ƙa'idodjin tafiye-tafiye da ƙasar ta saka kan ƴan Najeriyar da ta taƙaita bizarsu zuwa ta shiga Amurkar sau ɗaya sannan kuma sai an sabunta bayan watanni uku.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce taƙaita bizar ya saɓa da "tsarin ƙwaryar da ta je ta zo da kuma mutunta juna da ke yin jagora ga ƙasashe ƙawaye guda biyu." In ji wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen ƙsar.
A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, Najeriya ta ce sabuwar ƙa'idar taƙaita bizar za ta shafi ƴan ƙasar da ke burin yin karatu a Amurkar da ƴan kasuwa da ma masu ziyarar ƴan uwa da abokan arziƙi.
Ƙasashen Amurka da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da Canada da Burtaniya na daga cikin jerin ƙasashen da suka taƙaita bai wa ƴan Najeriyar biza bisa dalilan maƙalewa a ƙasashen da tsaro da dalilan tattalin arziƙi da na lafiya.
Amurka

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 8 ga watan Yulin nan ne Amurka ta sanar da wasu jerin tsauraran sauye-sauye a tsarin bayar da takardar izinin shiga ƙasarta ga masu zuwan wucin-gadi daga Najeriya.
A yanzu ƙasar ta zaftare wa'adin bizar da kuma dalilan bayar da bizar ga yawancin ƴan Najeriya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce manufofi da tsare-tsaren bayar da biza na daga abubuwan da ake iya sauyawa a kodayaushe - wanda kuma za a iya sauya shi la'akari da yanayin alaƙar diflomasiya da tsaro da ƙa'idoji ko yanayin shige da fice.
A sanarwar gwamnatin Amurka ta ce tana aiki ƙut-da-ƙut da hukumomin Najeriya domin tabbatar da ganin Najeriya ta daidaita al'amuranta kamar yadda ya dace da tsarin manyan ƙasashen duniya - ta fannin :
- Bayar da takardun tafiye-tafiye masu tsaro
- Da hana wuce wa'adin da aka ɗiba wa mutum a biza
- Da kuma musayar bayanan da suka shafi tsaro ko wani mugun laifi saboda dalilai na kare lafiyar jama'a.
Ƴan Najeriya masu yawon buɗe idanu da ƴan kasuwa masu tafiye tafiye na daga cikin waɗanda wannan sauyi mai tsauri na bayar da bizar Amurkar zai shafa.
Cikin sanarwar ɗaukar matakin da amurka a fitar ta ce ta yi hakan ne saboda ita ma Najeriya, abin da take yi wa Amurkawa kenan.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE)

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita ma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da sabbin ƙa'idojin biza ga ƴan Najeriya masu son shiga ƙasar da suka haɗa da hana bayar da bizar shiga ƙasar a fita da kuma sharuɗɗa masu tsauri ga masu yawon buɗe ido.
Bayanai sun nuna cewa sabon tsarin bizar a yanzu zai hana ƴan Najeriya masu shekara 18 zuwa 45 neman bizar yawon buɗe ido sai dai idan za su yi tafiyar ne a tawaga ko kuma tare da iyalansu.
Sabon tsarin ya nuna cewa waɗanda suke sama da shekaru 45 da haihuwa ka iya neman bizar, amma bisa sharaɗin za su nuna abin da suke da shi a asusunsu da ke ɗauke da aƙalla dalar Amurka 10,000 a ƙarshen kowane wata na tsawon watanni shida.
Ƙasar ta UAE dai bata bayar da dalilan taƙaita bizar ba amma ana hasashen cewa ta yi hakan ne da manufar takaita yawan ƴan Najeriya da ke tururuwa zuwa ƙasar da masu yawon buɗe ido da ƴan kasuwa ke zuwa.
Kamfanonin da ke shirya tafiye-tafiye suna shawartar ƴan Najeriya da su fahimci sabbin sharuɗɗan kafin su nemi bizar, ƙari a kan miƙa dukkannin takardun da ake buƙata kamar neman otal da fasfo.
Canada

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Canada ma ta bi sahun sauran ƙasashen inda a ranar Larabar nan ta ƙara yawan kuɗin da ya kamata ƴan Najeriya su zamo suna da su a asusunsu domin samun biza.
Gwamnatin ta Canada ta ce daga ranar 7 ga watan Yulin 2025 duk mai son neman bizar gaggawa ta cirani sai yana da naira miliyan 17 a asusunsa.
Bayanai daga rumbum bayanai na jami'an hukumar shigi da fici na ƙasar sun nuna cewa masu neman bizar shiga ƙasar ta karo ɗaya dole ne sai yana da naira miliyan 17 a asusunsa, inda mutum biyu iyalai dole ne su nuna asusun nasu mai ɗauke da naira miliyan 21.2.
Canada ta ce ta yi ƙarin ne bayan sake yin nazari kan kuɗaɗen da ya kamata masu ziyarar su mallaka domin riƙe kansu a yayin zamansu a ƙasar.
Har wayau, gwamnatin ta Canada ta ce matakin ya faru ne sakamakon rage yawan masu shigi da fici a ƙasar ta hanyar rage yawan ma'aikatan wucin gadi na ƙasashen waje da ɗalibai zuwa ƙasa da kaso biyar na yawan ƴan ƙasar tata ya zuwa 2027.
Burtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Ita kuwa Burtaniya ta sanar da cewa daga ranar 15 ga watan Yulin nan za ta fara bayar da biza ta intanet ga ɗalibai da masu son yin aiki a ƙasar maimakon a manna musu bizar a fasfo ɗinsu.
Ofishin jakadancin Burtaniya a Abuja ne ya sanar da hakan ranar Larabar nan.
Ofishin jakadancin ya ce an ɓullo da tsarin ne a shirye-shiryen Burtaniyar na mayar da aikin shigi da ficinta zuwa na zamani
Jakadar Burtaniyar, Gill Lever ya ce sauyin zai samar da tsarin bai wa ƴan Najeriya bizar shiga Burtaniya ba tare da ɓata lokaci ba.











