Waiwaye: Ƙaruwar farashin man fetur da tuɓe hakimai shida a Bauchi

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi ranar Lahadi 16 ga watan Yuli zuwa Asabar 22 ga wata.

Farashin litar man fetur ya tashi zuwa naira 617 a Najeriya

A ranar Talata, ba zato babu tsammani ƴan Najeriya suka tashi da labarin ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar.

Farashin litar man fetur ya kai naira 617 a sassan ƙasar, ƙari a kan 540 da aka saba sayarwa a baya.

A jawabinsa na karɓar mulki, shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya ingiza farashin litar man daga kimanin naira 200 zuwa naira 600.

Cire tallafin man fetur dai na nufin za a riƙa samun hawa da saukar farashin litar mai domin kuwa kasuwa ce za ta tantance farashin.

Kuma hakan na nufin ƴan kasuwa za su iya shigar da man fetur daga ƙasashen waje kuma su sayar a farashin da suke so ta yadda za su mayar da uwar kuɗi kuma su samu riba.

Tun bayan cire tallafin man fetur ɗin farashin sufuri da kayan masarufi ya riƙa hauhawa.

Lamarin da ya sanya gwamnatin ƙasar ta ce za ta fito da wasu shirye-shiryen da za su sauƙaƙa wa mutane raɗaɗin cire tallafin.

Tinubu ya amince da kafa asusun gina ababen more rayuwa a jihohi

Shugaban Najeriya Bora Ahemd Tinubu ya amince ca kafa asusun gina ababen more rayuwa a jihohin ƙasar 36, a wani mataki na rage wa yan ƙasar raɗaɗin cire tarafın man fetur.

Shugaban ya amince da matakin ne a lokacin taron wata-wata na kwamitin kula da asusun raba kuɗin shiga na gwamnatin ƙasar (FAAC) da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake ya fitar, ya ce sabon asusun zai taimaka wa jihohin ƙasar wajen zuba jari a ɓangarorin sufuri da harkokin noma da gina tituna da kasuwanni da kiwon dabbobi da ɓangaren lafiya da ilimi musamman a matakin farko, da wutar lantarki da ruwan sha domin haɓaka tattalin arzki da samar da ayyukan yi ga ƴan ƙasar.

Kwamitin ya kuma amince da ajiye wani ɓangare na kuɗin da ake rabawa a kowane wata domin takaita tasirin aeruwar shiga da za a iya samu sakamakon matakan cire tallatin mai da daidata farashin dala tare da hauhawar farashin kayayyaki za su iya haifarwa.

Kwamitin ya ce daga cikin naira tiliyan 1.9 na kuɗin shigar da aka samu a watan Yunin 2023, naira biliyan 907 ne kawai za a raba tsakanin matakan gwamnatin ƙasar uku, yayin da za a ajiye naira biliyan 790 a asusun.

Waɗannan kuɗaɗen da za a riƙa ajiyewa za su taimaka wajen samar da asusun gina ababen more rayuwa tare da aiwatar da wasu abubuwa, domin tabbatar da an yi amfani da kuɗin tallafin wajen gina muhimman abubuwan ci gaba, domin inganta rayuwar yan ƙasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma kwamitin ya yaba wa shugaban ƙasar bisa matakin cire tallafin man tare da ɓullo da matakai daban-daban na tallafa wa 'yan ƙasar domin rage masu raɗaɗin cire tallafin.

Kyari ya maye gurbin Abdullahi Adamu a matsayin shugaban APC

Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara ɗaya da 'yan watanni yana jagorantar jam'iyyar.

Sabon shugaban riƙo na jam'iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus ɗin Adamu kwana guda bayan kafafen yaɗa labarai a Najeriya suka wallafa labarin cewa rashin jituwa tsakanin Sanata Adamu da shugaba Tinubu ya tursasa masa yar da ƙwallon mangwaro

Shugaban jam’iyyar ta APC ya bar muƙamin ne kimanin wata biyar bayan ya jagorance ta a zaɓen shugaban ƙasar, inda ta yi nasara.

Bayanai sun ce Adamu ya ajiye aikin ne tare da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore.

Akwai dai alamu na cewa an dinga samun takun-saka a cikin jam’iyyar tun bayan da shugaba Tinubu ya kama mulki, kimanin watanni biyu da suka gabata.

Ajiye muƙamin shugaban jam’iyyar zai iya alamta cewa akwai wani babban rikici ne tsakanin ƴaƴan jam'iyyar da aka kasa samun masllaha.

Shugaban riƙon jam’iyyar na ƙasa, Abubakar Kyari ya ce Sanata Adamu bai bayyana dalilin ajiye muƙamin nasa ba.

Gwamnatin Bauchi ta sanar da tuɓe masu sarauta shida a jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da korar hakimai da dagatai shida saboda a cewarta an same su da shiga harkokin siyasa da cin iyakar gandun dazuka ba bisa ƙa'ida ba.

Matakin korar wanda ya shafi masu riƙe da sarauta a masarautun Bauchi da Katagum, yana ƙunshe ne a sanarwar da Babban Sakataren riƙo a hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomi, Nasiru Ibrahim ya fitar.

Mutanen da lamarin ya shafa a cewar sanarwar, sun haɗar da Hakimin Udubo, Alhaji Aminu Muhammad Malami da Hakimin Azare Alhaji Bashir Kabir Umar da Dagacin Gadiya, Umar Omar da Dagacin Tarmasawa, Umar Bani dukkansu a masarautar Katagum.

Sai kuma Dagacin Beni Bello Suleman da Dagacin Badara, Alhaji Yusuf Aliyu Badara a masarautar Bauchi.

Sanarwar ta ambato hukumar na cewa ta amince da korar masu riƙe da sarautun ne saboda shiga harkokin siyasar jam'iyya da aikata ba daidai ba da cin iyakar dazuka ba bisa ƙa'ida ba da sare itatuwa da ɓarnatar da dukiyar jama'a da rashin biyayya, waɗanda suka saɓa da dokokin aikin gwamnati.

Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya N2m ga mutanen da aka yi yunƙurin rusawa gidaje

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta umarci gwamnatin jihar da sauran waɗanda aka yi ƙara, su biya wasu mazauna unguwar Salanta, kuɗi naira miliyan ɗaya kowannensu akan yunƙurin rusa musu kadarori ba bisa ƙa'ida ba.

Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya yanke hukuncin cewa yunƙurin gwamnatin Kano da jami’anta na sanya wa gidan Saminu Shehu Muhd ​​da na Tasiu Shehu Muhd ​cikin ​jerin gidajen da za a iya rushewa bayan an buga musu lambar jan fenti ba tare da bin ƙa’ida ba, tauye ƴancinsu ne na mallakar kadara kamar yadda sashe na 43 da 44 na tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tabbatar musu.

Jaridar Daily Trust ta ambato Barista Bashir Ibrahim, wanda ya shigar da karar a madadin Saminu da Tasiu, bayan yanke hukuncin yana yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama ta kare haƙƙi da martaba ƙimar ɗan adam.

A nasa ɓangaren, lauyan gwamnatin jihar Kano da sauran waɗanda aka yi ƙara a shari’ar, Barista Musa Dahuru Muhd ​​daraktan shari’a a ma’aikatar shari’a ta Kano, ya ce za su yi nazari a kan hukuncin tare da bai wa gwamnati shawara game da mataki na gaba.

Tinubu ya buƙaci a sauya dokokin aikin soji a Najeriya da makwabtanta

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya Stella Oduah, tare da wasu mutum takwas a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.

An gurfanar da mutanen ne kan zarge-zarge 25 da suka haɗa da halasta kuɗin haram, da haɗin baki, tare da amfani da wani asusun ajiyar banki marar suna a bankin First Bank da aka samu kimanin naira biliyan biyar a cikinsa.

Sai dai bayan karanto musu zarge-zargen Oduah tare da sauran mutanen takwas ciki har da wata tsohuwar hadimarta, sun musanta duka zarge-zargen da hukumar ke yi musu.

Alkalin kotun, Mai shari'a Inyang Ekwo ya umarci ofishin babban Atoni-Janar na ƙasa da ya karbi hurumin shigar da ƙarar daga hannun hukumar ta EFCC.

Stella Oduah ta riƙe muƙamin ministar sufurin jiragen sama a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014.

FIRS ta tara harajin naira tiriliyan 5.5 cikin wata shida

Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Najeriya (FIRS) ta bayyana karɓar harajin naira tiriliyan 5.5 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Shugaban hukumar Muhammad Nami ne ya bayyana haka a lokacin taron Majalisar tattalin arzikin ta ƙasar da ya gudana ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar de ke Abuja.

Wannan ne karo na farko da hukumar ta tara adadi mafi yawa na kuɗin haraji a cikin wata shida, kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar ya nuna.

Rahoton da Muhammad Nami ya gabatar wa majalisar tattalin arzikin, ya nuna cewa abin da hukumar ta tara ya zarta abin da ta ƙiyasta samu a cikin rabin shekarar.

Tun da farko hukumar ta ƙiyasta tara naira tiriliyan 5.3 a cikin wata shidan farko na shekarar.

Rahoton ya kuma nuna cewa kuɗin harajin da hukumar ta tara a ɓangaren man fetur, naira tiriliyan 2.03 ne ya fi yawa cikin harajin da hukumar ta tara.

Sai kuma naira tiriliyan 3.76 da hukumar ta tara daga sauran bangarori.