Yadda bukukuwan Kirsimeti suka gudana a faɗin duniya

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Francis na gabatar da jawabi ga taron mabiya a ranar Kirsimeti

A ranar Lahadin nan ne Mabiya addinin Kirista suke gudanar da bukukuwan Kirsimeti wadda ake yi kowace ranar 25 ga watan Disamba.

Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.

Mabiya addinin Kirista a wurare daban-daban a faɗin duniya na ci gaba da bayyana murna da yin shagulgula don nuna farin ciki da zagayowar wannan rana

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka shirya wata majami'a a unguwar Staverton da ke Ingila, da safiyar ranar Kirsimeti, gabanin karasowar mutane domin fara addu'o'i.

Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.

Sarki Charles III

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Charles III tare da iyalansa lokacin da suka halarci bikin Kirsimeti

Sarki Charles III ya gaisa da dandazon mutane a Sandringham bayan ya halarci addu'o'in Kirsimeti karon farko a matsayinsa na sarki.

Sarkin na tare ne da matarsa, da kuma Yarima mai jiran gado tare da sauran iyalan gidan sarautar.

Sarki Charles III ya hau kan karagar mulkin Birtaniya ranar 8 ga watan Satumba 2022, yayin da ake shirin yin bikin naɗinsa ranar 6 ga watan Mayun 2023.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima William tare da iyalansa a lokacin da suke halarci addu'o'in Kirsimeti a majami'a

Yarima William, da matarsa gimbiyar Wales, da 'ya'yansa Yarima George, da Gimbiya Charlotte, da Yarima Louis su ma sun halarci taron addu'o'in da aka gudanar.

Mabiya Addinin Kirista

Asalin hoton, Getty Images

Majami'ar Nativity kenan da ke Bethlehem a kudu da gaɓar yamma da kogin Jordan wurin da aka yi amanna cewa a nan ne aka haifi Yesu Almasihu.

Limamin Majami'a

Asalin hoton, Getty Images

Babban limamin Kiristocin birnin Jerusalem Pierbattista Pizzaballa ne ya jagoranci taron addu'o'in a majami'ar.

Masu gasar ninƙaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu gasar ninkaya ta (Christmas Cup) kenan a birnin Barcelona na ƙasar Sifaniya

An gudanar da gasar ninƙaya ta (Christmas Cup) karo na 113, a birnin Barcelona na ƙasar Sifaniya.

Gasar wacce ake tseren ninƙayar mita 200 ana gudanar da ita ne a kowacce ranar Kirsimeti a birnin.

Mata suna addu'o'oi

Asalin hoton, Getty Images

Wasu mata kenan a cocin St. John's Cathedral na ƙasar Pakistan.

Masu ziyarar ibada

Asalin hoton, Getty Images

Wasu mazu ziyarar ibada kenan daga wasu ƙasashe a lokacin da suka kai ziyarar ibada zuwa majami'ar da aka haifi Yesu a birnin Bethlehem na ƙasar Falasɗinu.

Limamin Santanbul

Asalin hoton, Getty Images

 Limamin cocin Aya Yorgi, Patriarch Bartholomew ke jagorantar addu'o'i a birnin Satanbul na ƙasar Turkiyya.