Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda bukukuwan Kirsimeti suka gudana a faɗin duniya
A ranar Lahadin nan ne Mabiya addinin Kirista suke gudanar da bukukuwan Kirsimeti wadda ake yi kowace ranar 25 ga watan Disamba.
Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Mabiya addinin Kirista a wurare daban-daban a faɗin duniya na ci gaba da bayyana murna da yin shagulgula don nuna farin ciki da zagayowar wannan rana
Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Sarki Charles III ya gaisa da dandazon mutane a Sandringham bayan ya halarci addu'o'in Kirsimeti karon farko a matsayinsa na sarki.
Sarkin na tare ne da matarsa, da kuma Yarima mai jiran gado tare da sauran iyalan gidan sarautar.
Sarki Charles III ya hau kan karagar mulkin Birtaniya ranar 8 ga watan Satumba 2022, yayin da ake shirin yin bikin naɗinsa ranar 6 ga watan Mayun 2023.
Yarima William, da matarsa gimbiyar Wales, da 'ya'yansa Yarima George, da Gimbiya Charlotte, da Yarima Louis su ma sun halarci taron addu'o'in da aka gudanar.
Majami'ar Nativity kenan da ke Bethlehem a kudu da gaɓar yamma da kogin Jordan wurin da aka yi amanna cewa a nan ne aka haifi Yesu Almasihu.
Babban limamin Kiristocin birnin Jerusalem Pierbattista Pizzaballa ne ya jagoranci taron addu'o'in a majami'ar.
An gudanar da gasar ninƙaya ta (Christmas Cup) karo na 113, a birnin Barcelona na ƙasar Sifaniya.
Gasar wacce ake tseren ninƙayar mita 200 ana gudanar da ita ne a kowacce ranar Kirsimeti a birnin.
Wasu mata kenan a cocin St. John's Cathedral na ƙasar Pakistan.
Wasu mazu ziyarar ibada kenan daga wasu ƙasashe a lokacin da suka kai ziyarar ibada zuwa majami'ar da aka haifi Yesu a birnin Bethlehem na ƙasar Falasɗinu.
Limamin cocin Aya Yorgi, Patriarch Bartholomew ke jagorantar addu'o'i a birnin Satanbul na ƙasar Turkiyya.