Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Bruyne da Doku suna cikin tawagar Belgium zuwa Euro 2024
Ƴan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne da Jeremy Doku suna cikin tawagar Belgium da za ta je da su Euro 2024, amma ba golan Real Madrid, Thibaut Courtois a ciki.
Cikin ƴan wasa 25 da aka bayyana yawancinsu suna buga Premier League da ya hada da na Arsenal, Leandro Trossard da na Aston Villa, Youri Tielemans.
Sauran sun hada da na Everton, Amadou Onana da na Leicester City, Wout Faes da kuma na Fulham, Timothy Castagne.
An yi mamaki da aka ji an bayyana sunan ɗan wasan Atletico Madrid, Axel Witsel, mai tsaron baya mai shekara 35, wanda ya sanar da yin ritaya a bara.
Haka kuma tawagar ta gayyaci Romelu Lukaku, wanda ya buga wasannin aro a Roma daga Chelsea a bana.
Courtois, wanda ya buga wa kasar wasa 102 ya koma taka leda a baya, bayan da ya sha jinya, ana sa ran shi ne zai tsare ragar Real Madrid a Champions League.
Ranar 1 ga watan Yuni a Wembley za a buga wasan karshe a gasar ta zakarun Turai tsakanin Borussia Dortmund da Real Madrid.
Tun a watan jiya kociya, Domenico Tedesco ya ce ba zai gayyaci Courtois, mai shekara 32 ba, wanda ya kara da cewar ba zai je Jamus da wanda baya kan ganiya ba.
Hakan ya sa Tedesco ya zabi golan Wolfsburg, Koen Casteels da na Luton, Thomas Kaminski da kuma na Nottingham Forest, Matz Sels a matakin masu tsaron ragar ragar Belgium.
Belgium tana da damar kara ɗan wasa daya a cikin tawagar kafin ranar 7 ga watan Yuni
Tawagar Belgium tana rukuni na biyar da ya hada da Romania da Ukraine da kuma Slovakia. Za ta fara wasan farko da Slovakia ranar 17 ga watan Yuni a Frankfurt.
Ƴan wasan tawagar Belgium
Masu tsaron raga: Matz Sels (Nottingham Forest), Koen Casteels (Wolfsburg), Thomas Kaminski (Luton)
Masu tsaron baya: Wout Faes (Leicester), Timothy Castagne (Fulham), Arthur Theate (Rennes), Jan Vertonghen (Anderlecht), Axel Witsel (Atletico Madrid), Zeno Debast (Anderlecht), Thomas Meunier (Trabzonspor), Maxim De Cuyper (Club Brugge)
Masu buga tsakiya: Aster Vranckx (Wolfsburg), Youri Tielemans (Aston Villa), Orel Mangala (Lyon), Kevin De Bruyne (Manchester City), Arthur Vermeeren (Atletico Madrid), Amadou Onana (Everton)
Masu cin ƙwallaye: Romelu Lukaku (Roma), Charles De Ketelaere (Atalanta), Jeremy Doku (Manchester City), Lois Openda (Leipzig), Leandro Trossard (Arsenal), Johan Bakayoko (PSV Eindhoven), Dodi Lukebakio (Sevilla), Yannick Carrasco (Al-Shabab)