An ɗaure matashin da ya kashe malamarsa a kan ƙwauron maki

Malama

Asalin hoton, POLICE HANDOUT

Bayanan hoto, ...

An yi wa wani matashi a jihar Amurka ta Iowa ɗaurin rai-da-rai bayan ya yi wa malamarsa dukan kawo wuƙa da sanda, har ya zama ajalinta.

Willard Miller, ɗan shekara 17, ya amsa laifin aikata kisa a watan Afrilu saboda hannun da yake da shi wajen kashe Nohema Graber, wata malamar harshen Sifaniyanci a ranar 2 ga watan Nuwamban 2021.

Miller da abokin da aka zarge su tare, Jeremy Goodale, wanda yanzu ya cika shekara 18, sun auka wa Nohema Graber mai shekara 66, bayan ta bai wa Miller maki kaɗan a makaranta.

Yana da shekara 16 lokacin da suka aikata kisan kan, amma an tuhume su a matsayin baligai.

Sai a watan Agusta za a yanke wa Jeremy Goodale hukunci.

A ranar Alhamis ne, aka yanke wa Miller hukuncin ɗaurin rai-da-rai, da yiwuwar samun sakin afuwa bayan ya shafe shekara 35 a ɗaure.

...

Asalin hoton, POLICE HANDOUT

Bayanan hoto, Willard Miller da Jeremy Goodale

An kuma umarci ya biya aƙalla $150,000 (kwatankwacin naira miliyan 112) a matsayin diyya ga dangin mai mutuwar.

Kafin ya gabatar da hukuncinsa, Mai shari'a Shawn Showers ya yi watsi da bahasin wanda aka yi ƙara na cewa Miller ya yi yarinta sosai a lokacin, don haka ba ma zai iya fahimtar girman abin da ya aikata ba.

Sai dai alƙalin ya ce: "Mugu ba shi da kaɗan".

Dangin malama Nohema Graber sun faɗa wa kotun cewa ba su yarda Miller ya yi nadama kan abin da ya aikata ba.

Da yawan dangin nata sun kuma bayyana cewa mutuwar matar ta yi sanadin ƙarar kwanan mai gidanta, Paul. An yi jana'izarsa, kwana guda kafin ranar Alhamis da aka yanke hukuncin a kan kisan.

Miller ya nemi gafarar al'ummar yankin kuma ya juya ga dangin Nohema Graber da ke zaune a bayansa, inda ya yi musu jawabi.

"Ina matuƙar ba ku haƙuri saboda tashin hankalin da na jefa ku da dugunzumar da na haddasa wa miji da 'ya'yan mai mutuwa," in ji shi.

Da yake roƙon alƙali a kan ya haƙura da batun yanke masa hukunci mafi tsanani, Miller ya ce: "Ba zan so a turke ni tsawon lokacin da har zan mance wane ne ni da kuma ko daga ina na fito ba."

Masu gabatar da ƙara sun ce shaida ta nuna cewa Miller da Goodale sun yi ta shirga wa Nohema Graber gora, lokacin da suka far mata a Fairfield, wani gari mai adadin mutanen da suka gaza 10,000 da ke da nisan mil 100 (160km) kudu maso gabashin babban birnin jihar, Des Moines.

Kwana guda bayan harin ne, 'yan sanda suka gano gawar mahaifiyar 'ya'ya ukun ɓoye a cikin wata kura an lulluɓe da tamfol a kan titin jirgin ƙasa kusa da wani dandali inda ta saba zuwa yin tattaki, bayan ta tashi daga makaranta.

Da yake maida jawabi a hannun 'yan sanda, Miller ya bayyana damuwar da yake da ita ga yadda Nohema Graber ta koyar da shi harshen Sifaniyanci.

Ya ce makin da yake samu a ajinta ne ya mayar da shi baya a jimillar makinsa na ƙarshe, wani muhimmin abu da ake buƙata don neman damar shiga kwalejojin Amurka da kuma samun tallafin karatu.