Abin da ya faru a wajen naɗin Sarki Charles na Birtaniya

Asalin hoton, PA Media
Majalisar naɗa sarki ta sanar da naɗa sabon sarki a bainar jama’a a ranar Asabar, a wani biki da aka kwashe kusan shekara 70 ba a ga irinsa ba.
Daga wata murna da aka yi ta bai daya domin taya sabon sarki murna zuwa wani bayani mai taba zuciya, ya sha rantsuwa sannan dakarun kasa sun sara masa.
Ga dai wasu abubuwa da suka faru a fadar St James.
An sanar da Charles III a hukumance a matsayin Sarki a wani biki da aka yi mai cike da tarihi a Fadar St James da ke Landan.
Yayin bikin da aka yi a gargajiyance a safiyar ranar Asabar – wanda aka haska a kusan duka gidajen talabijin a karon farko – an yi kasa da tutoci da safe domin girmamawa ga marigayiya sarauniya – an kuma daga su yayin bikin domin nuna girmamawa da biyayya ga sabon Sarki.
Za a ci gaba da wasu lamuran nade-naden a fadin Birtaniya har sai ranar Lahadi, inda za a kara sassauta tuta yayin ci gaba da makokin mutuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta mutu a ranar 8 ga watan Satumba.
Sabon Sarki ya sha rantsuwa daga kwamitin nada Sarki a yayin wani bikin gargajiya, wanda rabon da a yi irinsa a Birtaniya tun shekara 70 baya.
Me ake nufi da sanarwar nadin Sarki?
Kai tsaye dama Charles ne Sarki saboda mutuwar mahaifiyarsa – karkashin dokar zamantakewa ta 1701.
Aikin kwamitin nadin sarki shi ne yayin biki, domin sanar da sunan sabon Sarki a hukumance.
A al’adance, ana yin wannan ne cikin kwana guda da mutuwar wanda ke kan karagar mulki.
Amma a wannan karon an dan samu karin lokaci tsakanin bikin nadin da aka yi a Fadar St James da kuma mutuwar Sarauniya Elizabeth II, wanda aka yi a tsakiyar birnin Landan kusa da Fadar Burkingham.
A wani mataki da ya saɓa da al’ada, Sarki Charles ya bayar da damar a haska bikin a gidajen talabijin a karon farko cikin tarihi.
Su wane ne suka halarci bikin?

Asalin hoton, Reuters
Sama da mambobin majalisar koli 200 ne suka halarci taron – wanda yawanci masu bayar da shawara ne ga basaraken da ke mulki, mafi yawansu tsofaffi da kuma yan siyasa ne na yanzu – sun taru a Fadar St James tare da malaman coci masu yawa.
Majalisar ta dade tun zamanin sarakunan karni na 10. Mambobinta sun kai 700, amma 200 kawai aka kira.
Tsofaffin Firaiministocin Birtaniya irin su Gordon Brown da David Cameron da Boris Johnson da kuma Theresa May wadda ta hadu da Sarauniya a wurare da yawa cikin shekaru masu dama – duk sun halarci taron.
Sai kuma magajin gari Birnin Landan da manyan alkalai da kuma jami’ai masu dama.
Camila Parker Bowels matar Charles sama da shekara 17 da ɗansa Williams wanda shi ne sabon Yariman Wales duka sun halarci taron.
Mataki na farko: Sanya wa Sarki suna
An raba kwamitin nada Sarki zuwa gida biyu, kuma Chrles ya fito ne cikin gida na biyu.
A matakin farko, Shugaba – kuma mamba a majalisa karkashin jam’iyyar masu ra’ayin rikau Penny Mordaunt wadda aka rantsar a ranar 6 gawatan Satumba – ta sanar da mutuwar Sarauniya.
Daga nan kuma ta nemi malaman coci da na kwamitin nadi su gabatar da ayyana sabon Sarki, wanda ciki har da Charles da aka bai wa matsayin Sarki Charles III.
Sannan mutane kusan 200 ko sama da haka da suka halarci taron suka ce “Allah ya kiyaye Sarki” bayan kammala karanta bayanai.
An yi hakan a gaban Yarima William da Firaiminista Liz Truss da shugaban cocin Ingila Justin Welby.
Sai dai duka iyalan Gidan Sarautar ne suka sanya hannu kan takardar da ta ayyana Sarkin, da sauran wasu manyan baki ciki har da Earl Marshall – Duke na Norfolk – wanda shi ne ke da hakkin tara wannan biki.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Mataki na biyu: Bayanin Sarki
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mataki na biyu shi ne taruwar kwamitin naɗa Sarki za su taru gaban Sabon Sarki a dakin da ake nada Sarki da ke Fadar St James.
Taron farko kenan da wadannan mutane suka yi a gaban sabon Sarki kenan cikin gwamman shekaru.
Kansiloli sun yi layi sun tsaya domin yin maraba da Sarki, kowa yana tsaye babu wanda yake zaune kamar dai yadda aka saba yi a al’adance.
Ya fara da wani bayani mai taba zuciya ga kwamitn da ke nada sarki, “ya yi bayani kan mahaifiyarsa da yake mutakar ƙauna da yadda ta yi wa al’umma bauta” ya kuma yi fatan bin sawunta.
“Duka duniya na tausaya mani kan wannan gagarumin rashin da na yi, wanda ba za a iya maye gurbinsa ba.”
Mulkin da mahaifiyata ta yi babu wanda za ka iya kwatanta shi da shi a lokacinta, yadda ta sadaukar da kanta da bautar da ta yi wa jama’a. Don haka dole mu yi godiya da rayuwarta da ta yi.”
Ya kuma ci gaba da yin bayani kan hakkokin da suke a kansa.
“Ina sane da irin manyan ayyukan da na gada da kuma wajiban da ke kaina ko kuma wadanda aka dora mani.”
Ya bayyana Camilla a matsayin Sarauniya consort, matar Sarki, “Ina alfahari da farin ciki da irin goyon bayan da matata ta ke bani,” in ji shi.
Me rantsuwar da Sarki Charles ya yi take nufi?

Asalin hoton, others
Karkashin dokar rantsuwar, dole ne sabon basarake ya yi rantsuwa domin yin biyayya ga cocin Scotland.
Saboda a Scottland an raba iko tsakanin coci da kuma kasa.
Charles ya rattaba hannu kan wasu kwafi biyu na takardu gaban majalisar koli.
Wadanda suka halarci taron suma sun sanya hannu, ciki har da yarima Williams – wato sabon yarima na Wales kenan – tare da Camilla Sarauniya.
A karshe mahalarta taron sun yi wake, masu ganga suka taya su.
Mene ne ya faru a baranda?
Bayan an gama komi sai aka koma wajen fadar.
Duka mutane sun fita daga wajen dakin taron domin ganin yadda za a ayyana Sarki Charles na uku.
Dakarun gidan Sarautar sun fito wajen barandar a saman Friary Court domin karanta ayyanawar tukunna aka yi busar sarewa irin ta gidan sarauta.
An yi taken kasa wanda a karshe aka ce “Allah ya kiyaye Sarki” a Turance “God Save the King” maimakon “Allah ya taimaki Sarauniya da aka fi shekaru sama da 70 ana fada.
Me zai faru a nan gaba?

Asalin hoton, Reuters
Bikin ya zo karshe ne lokacin da shugaban Majalisar Koli ya ayyana Charles a matsayin sabon “Sarki, Shugaban kasashen rainon Ingila mai kare addini” kafin daga bisani a ce “Allah ya kiyaye Sarki”.
Penny Mordaunt ta rufe taron ne da karanto daftarin dokar ayyanawar wanda za a sahhale, sannan Sarki Charles ya sanya musu hannu daya bayan daya.
Daya daga cikinsu shi ne na ranar binne Sarauniya wadda za ta zama ranar hutun mutanen kasar baki daya.
Amma yanzu za a dauki lokaci kafin a zo a yi bikin mubaya’a da nadin sarki.
A baya wata 16 aka dauka tsakanin mutuwar mahaifin Sarauniya Elizabeth Sarki George na shida da nadata, wanda ya mutu a watan Fabirairun 1952, ita kuma aka nadata a watan Yuni 1953.











