Sarauniya Elizabeth II: Hotunan rayuwar Sarauniyar Ingila

Sarauniya Elizabeth II a shekarar 1951

Asalin hoton, Yousuf Karsh / Camera Press

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth II ta biyu ta zama basararakiya mafi dadewa a Birtaniya a shekarar 2015 tun bayan da ta zama sarauniya a shekarar 1952.
White Line 1 Pixel
Mahaifyar Sarauniya Elizabeth Saraniuyar York kenan da mijinta King George VI Yariman York a wurin radin sunan 'yarsu Sarauniya Elizabeth II a shekarar 1926.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, An haifi Sarauniya Elizabeth a ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 1926 a Landan. Ita ce 'ya ta farko ga Albert yariman York da kuma matarsa Elizabeth wadda aka fi sani da Lady Elizabeth Bowes-Lyon.
White Line 1 Pixel
Princess Elizabeth on a tricycle in the park

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth tare da kanwarta Margaret sun yi karatu ne a gida kuma ana iya ganinsu a nan suna wasa bayan kammala darasi.
Gimbiya Elizabeth kenan tana daga wa mutane hannu yayin da ta isa Piccadilly.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Tun tana karama, Elizabeth kan daga wa jama'a hannu yayin da ta fito bainar jama'a.
Sarki George VI da Sarauniya Elizabeth tare da 'ya'yansu Gimbiya Elizabeth da kuma Gimbiya Margret Rose bayan nadin Yariman York a matsayin Sarki George VI.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Bayan murabus din Sarki Edward VIII a shekarar 1936 mahaifinta ya zama Sarki George VI, ita kuma ta zama sarauniya mai jiran gado.
White Line 1 Pixel
Gimbiya Elizabeth (dama) da kuma Gimbiya Margret yayin gabatar da shirin Children's Hour a lokacin yaki ta kafar BBC.

Asalin hoton, Topical Press Agency / Getty Images

Bayanan hoto, A lokacin Yakin Duniya na II an dauke Elizabeth da 'yar uwarta zuwa Windsor, inda daga nan ne suka rika gabatar da shirin Children's Hour a kafar yada labarai ta BBC.
Gimbiya Elizabeth da Yariman Edinburgh yayin bikinsu a Westminster.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1947 ta auri Philip Mountbatten wanda dan uwanta ne kuma Yarima ne a kasar Girka da Denmark. Daga baya ya zama Yariman Edinburgh.
Gimbiya Elizabeth tana rike da danta Yarima Charlers jim kadan bayan bikin radin sunansa a Fadar Buckingham a shekarar 1948.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Yaronsu na farko Charles an haife shi ne a shekarar 1948.
White Line 1 Pixel
Gimbiya Elizabeth tana mika kofin kalubale na FA ga Billy Wright kaftin din kungiyar Wolverhampton Wanderers bayan sun doke kungiyar Leicester City da ci 3-1 a wasan karshe a filin wasa na Wembley.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Gimbiya Elizabeth tana gudanar da ayyuaka da dama - a nan tana mika kofin FA ne ga Billy Wright kaftin din kungiyar Wolverhampton Wanderers bayan sun doke kungiyar Leicester City a wasan karshe a filin wasa na Wembley.
Gimbiya da mahaifiyarta Sarauniya Elizabeth suna rike da malafarsu yayin da suke isa Westminster don halartar bikin auren Lady Caroline Montagu-Douglas-Scott ga Mista Ian Hedworth Gilmour.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Gimbiya da mahaifiyarta Sarauniya Elizabeth A shekarar 1951 a shekarar 1951 yayin da suke halartar bikin auren Lady Caroline Montagu-Douglas-Scott ga Mista Ian Hedworth Gilmour.
Sarauniya Mary (tssakiya) tana kallo sanda ake shigo da gawar danta George VI cikin farfajiyar Westminster a birnin Landan. Kusa da ita mahaifiyar Sarauniya ce idanunta rufe cikin alhini. Sarauniya Elizabeth II tana tsaye kusa da kakarta sanye da dankwali.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Mahaifin Elizabeth Sarki George VI ya rasu a ranar 6 ga watan Fabrairu na shelarar 1952 yayin da Elizabeth da Philip suke ziyara a kasar Kenya. Cikin gaggawa gimbiya ta dawo domin jana'izarsa. A nan suna tsaye daga bangaren hagu ita da mahaifiyarta, da kakarta, da Sarauniya Mary.
White Line 1 Pixel
Sarauniya Elizabeth II a lokacin nadin sarautarta a Westminster Abbey, 1953.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Elizabeth da gaggawa ta dawo gida, kuma an nada ta a matsayin sarauniya ne a cikin watan Yuni na shekarar 1953 a Westminster Abbey.
Sarauniya Elizabeth II tare da 'yarta Gimbiya Anne a ginin Windsor na Frogmore a shekarar 1959.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Baya ga ayyuakn ofis Sarauniya na zama tare da iyalanta - nan ita 'yarta ce Gimbiya Anne a ginin Windsor na Frogmore a shekarar 1959.
White Line 1 Pixel
Kaftin din tawagar 'yan wasan Ingila Bobby Moore rike da kyautar Rimet Trophy da ya karba daga Sarauniya bayan da ya jagorance su wajen lashe gasar cin Kofin Duniya, inda suka doke Jamus Ta Yamma a wasan karshe da ci 4-2.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Ta koma filin wqasa na Wembley a shekarar 1966 don ta bai wa kaftin din tawagar Ingfila kyautar Jules Rimet ga kaftin din awagar 'yan wasan Ingila Bobby Moore bayan da ya jagorance su wajen lashe gasar cin Kofin Duniya, inda suka doke Jamus Ta Yamma a wasan karshe da ci 4-2.
Iyalan gidan sarautar kenan a Frogmore da ke Windsor, Berkshire. Daga hagu zuwa dama: Duke na Edinburgh (mijin Sarauniya), Yarima Edward, Sarauniya Elizabeth II, Yarima Andrew, Gimbiya Anne, da kuma Yarima Charles.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Ma'auratan sun haifi yara hudu ne, kuma wannan hoto an dauke shi ne a Frogmore., Windsor. Daga hagu zuwa dama: Duke na Edinburgh (mijin Sarauniya), Yarima Edward, Sarauniya Elizabeth II, Yarima Andrew, Gimbiya Anne, da kuma Yarima Charles.
Sarauniya kenan yayin da take gabatar da Yarima Charles jim kadan bayan bikin ba shi lakabin sarauta a Caernarfon Castle.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A watan Yuli na shekarar 1969 Sarauniya ta gabatar da Yarima Charles ga jama'ar Wales, jim kadan bayan bikin ba shi lakabin sarauta cikin kade-kade da bushe-bushe a Caernarfon Castle.
Sarauniya na zaune a kan ciyayi tare da karnukan corgi a Virginia Water don kallon wasan tseren doki wanda danta Yarima Philip yake ciki. Ana kiran tseren da European Driving Championship wanda wani bangare ne na Royal Windsor Horse Show na shekarar 1973.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A lokutan mulkinta, an sha ganin Sarauniya tare da karnukan corgi. Alaka ta ginu ne tsakanin iyalan masarauntar da karnukan tun a shekarar 1933, lokacin da George VI ya sayo su a karon farko.
Sarauniya Elizabeth II tana yin tattaki a Portsmouth lokacin rangadin bikin cikarta shekara 25 a kan karagar mulki a watan Yuni na shekarar 1977.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1977 'yan kasa sun yi murnar cikar Sarauniya shekara 25 a kan karagar mulki. Ta gaisa da mutane cikin nishadi annashuwa a lokacin da take rangadi a Birtaniya.
Sarauniya q1q`da Duke na Edinburgh suna daga wa jirgi hannu yayin da yake wucewa a lokacin da suke isa Barbados.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya da Duke kenan suna daga wa jirgi hannu yayin da yake wucewa a lokacin da suke isa Barbados.
Gawar Lord Mountbatten rufe da tutar Birtaniya yayin jana'izarsa a Westminster Abbey. wadanda suka halrci wajen su ne: (daga zuwa dama) Sarauniya Elizabeth II, mijinta Duke na Edinburgh, mahaifiyarta Elizabeth, da kuma Yariman Wales a shekrar 1979.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A watan Agustan 1979 dan uwan Sarauniya Lord Louis Mountbatten ya rasu bayan wata fashewar bam a kan jirgin ruwansa a kasar Ireland. Duke na Edinburgh ya koma Birtaniya daga kasar Faransa inda yake aikin horar da tuki a wata gasa jim kadan bayan samun labarin.
Hoto na musamman a bikin Yariman Wales da Gimbiyar Wales a cikin watan Yulin 1981.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 1981 babban dan Sarauniya Charles ya auri Lady Diana Spencer. Charles da Diana sun haifi yara biyu - William da Harry - kafin su rabu. Daga baya Diana ta rasu sakamakon wani hatsarin mota a birnin Paris na kasar Faransa.
Sarauniya da Duke na Edinburgh a kasar China a shekarar 1986.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya da Duke na Edinburgh sun yi yawon bude-do sosai - nan suna kan Babban Bangon China ne a shekarar 1986.
White Line 1 Pixel
Sarauniya tana duba irin asarar da aka yi a Windsor castle.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A yayin bayaninta na Kirsimeti, Sarauniya ta bayyana shekarar 1992 a matsayin "shekarar annoba", inda ta nuna rashin dadinta ga yadda mutuwar aure ta yawaita da kuma gobara a Windsor Castle.
White Line 1 Pixel
Sarauniya na gaisawa da Geri Halliwell (Ginger Spice) daya daga cikin rukunin mawaka 'yan Amurka Spice Girls.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Bayan jam'iyyar Labour ta samu nasara a shekarar 1997, kalmar "Cool Britannia" na ci gaba da yaduwa. A nan Sarauniya tana gaisawa da rukunin mawaka 'yan Amurka Spice Girls wadanda wakarsu ta Wannabe ta zama lamba daya a kasashe 37 na duniya, ita ce kuma bakandamiyarsu.
Sarauniya Elizabeth II tare da Duke na Edinburgh suna duba fure da jama'a suka ajiye na mutuwar Diana a Fadar Buckingham Palace a shekarar 1997.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Rasuwar Diana Gimbiyar Wales ta jawo suka daga kafafen yada labarai cewa Sarauniya ba ta fito bainar jama'a a kan kari ba.
Mahaifiyar Sarauniya (hagu) ta yi bikin haihuwarta na shekara 100 a ballet, inda 'ya'yanta Gimbiya Margret da Sarauniya Elizabeth II (dama) suke tare da ita.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2000 mahaifiyar Sarauniya ta yi bikin haihuwarta na shekara 100. - nan Gimbiya Margret ce da Sarauniya Elizabeth II.
Sarauniya tare da Yariman Wales suna tafiya a gefen makarar mahaifiyarta a shekarar 2002.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Mutuwar mahaifiyarta wadda ta zo jim kadan bayan rauswar 'yar uwarta Gimbiya Margaret, ta sa an yi ta turo wa Sarauniya da sakonnin alhini a shekarar 2002 sanda ta yi bikin cikarta shekara 50 a karagar mulki a lokacin hunturu.
Daurin auren Yarima Charles tare da Camilla Parker Bowles, 2005.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2005 Sarauniya Elizabeth shaida auren danta Yarima Charles a karo na biyu tare da Camilla Parker Bowles a Windsor Guildhall.
Britain's Queen Elizabeth II, her husband the Duke of Edinburgh, the Prince of Wales and the Duchess of Cornwall attend the Braemar Highland Games

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Elizabeth da mijinta Basaraken Duke na Edinburgh, Yariman Wales da Basarakiya Duchess ta Cornwell na huttawa a wajen shakatawa da ke gandun dajin tsaunin Braemar a Aberdeenshire. Wadannan 'yan sarauta sun kasance masu yawan kai ziyara wannan gandun dajin shakatawa tun zamanin Sarauniya Victoria, wadda ta fara kai ziyara wurin shekarar 1848.
Queen Elizabeth II stands in the rain as guests take shelter at the opening of the Lawn Tennis Associations new headquarters in Roehampton, London, 2007

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2007 an dauki hoton Sarauniya ita kadai, tana fake wa ruwan sama lokacin da aka kaddamar da bude taron Kungiyar wasan kwallon hannu ta Lawn Tennis da Hedkwatarta a Roehamptom.
White Line 1 Pixel
Queen Elizabeth II sits in the Regency Room at Buckingham Palace in London as she looks at some of the cards which have been sent to her for her 80th birthday

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya ta furta kalaman hikimar Groucho Marx kan lamarin da ya danganci tsufa a jawabin da ta gabatar wajen bikin zagayowar ranar haihuwarta shekara 80, cewa: "Kowa zai iya tsufa; abin da ya kamata daukacinku ku yi, shi ne, ku yi kokarin ganin kun rayu tsawon zamani." Bayan shekara guda, a shekarar 2007, Sarauniya ta yi bikin cikar zagayowar ranar aurenta 60 tare da Yarima Philips.
Queen Elizabeth II lays a wreath at the Garden of Remembrance

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Mayun 2011 Sarauniya ta kasance mai sarautar Birtaniya ta farko da ta ziyarci Jamhuriyar Ireland. Ta ajiye furannin kallo a makabartar 'yan mazan jiya da ke Dublin, inda ta aiwatar da wani aiki da ke tattare da rudani a ziyarta. Abin da ta aikata yana da matukar muhimmanci saboda lambun (da ta dasa furannin kallon) an shirya shi ne don tunawa da mutane da suka yi yakin kwatar 'yancin mutanen kasar Ireland.
Prince William and his new bride Kate bow in front of Queen Elizabeth II at Westminster Abbey

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Al'amarin da ya fi faranta mata rai daga bisani cikin shekaru, shi ne auren jikanta Yarima William da Kate Middleton a shekarar 2011. A nan ne Yarima William da sabuwar amaryarsa Kate suka russuna a gaban Elizabeth.
Britain's Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh arrive at a windy RAF Valley in Anglesey, to visit their grandson Prince William at the base.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Malfar Sarauniya saura kadan ta fadi daidai lokacin da ta iso gabar tsaunukan rundunar sojan sama ta RAF da ke Anglesley, inda suka ziyarci jikanta Yarima William, wanda aka tura shi aiki sansani daidai wannan lokacin.
Queen Elizabeth II greets High Court judges as she officially opens the Rolls Building, the latest addition to the Royal Courts of Justice in central London

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Cikin shekarar 2011 Sarauniya ta kaddamar da ginin Rolls, wani kari fadada ginin gidan sarauta da aka yi wa Kotun Sarauta ta Shari'a da ke tsakiyar Landan.
Queen Elizabeth II and Duke of Edinburgh on the Spirit of Chartwell during the Diamond Jubilee Pageant on the River Thames

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A shekarar 2012 an ga Sarauniya ta yi bikin cikarta shekara 60 a karagar mulki, inda ruwa kamar da bakin kwarya ya cika kogin Peangeant da ke Thames.
Queen Elizabeth II (left) speaks at the Olympic Games 2012 Opening Ceremony

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Al'amuran da suka biyo bayan bikin daf-da-daf su ne gasar wasan olymfik da gasar wasannin nakasassu ta (Paralympics) da aka gudanar a Landan, inda aka gudanar da kayataccen bikin bazara a kasar. A nan ne Sarauniya ta kaddamar da bikin bude wasannin, inda aka ga ta tashi cikin lema a wajen bikin tare da James Bond (mashahurin mai shirin fina-finai).
Britain's Queen Elizabeth II with her racing manager John Warren after her horse, Estimate, won the Gold Cup, 2013

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Shekaru sittin a baya ta taba kasancewa Basarakiyar farko da ta lashe gasar sukuwar dawakin sarauta ta Royal Ascot, a matsayinta na wadda ta mallaki bargar dawakai, ta lashe kofin zinaren gasar na 207, al'amarin da ya baibayeta da farin ciki ita da manajan tseren dawakinta, John Warren.
Queen Elizabeth II, on the day she became Britain's longest reigning monarch, seen on the Scottish Borders Railway

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Da karfe 17: 30 (karfe biyar da rabi), ranar 9 ga Satumbar 2015, Elizabeth ta shafe kwanaki dubu 23,226 da sa'o'i 16 da kimanin mintuna 30 tana jan ragamar mulki inda ta zarta kakar babanta Sarauniya Victoria. Ta kwana guda a Scotland, inda ta yi godiya Ga masoya da suka yi mata fatan alheri a cikin kasar da kasashen waje saboda sakonninsu na "karamci masu sosawa da tausasa zukata." Tare da Yarima Philip ta yi tafiyar jirgin kasa mai rugugin hayaki daga Edingburgh zuwa Tweedbank, inda ta bude sabuwar iyakar Scotland na tashar jirgin kasa.
Queen Elizabeth II joins members of the royal family, including the Duke and Duchess of Cambridge with their children Princess Charlotte and Prince George, on the balcony of Buckingham Palace, central London after they attended the Trooping the Colour ceremony as the Queen celebrates her official birthday today

Asalin hoton, Steve Parsons/PA

Bayanan hoto, Sarauniya tare da iyalanta 'yan gidan sarauta sun yi bikin ranar haihuwarta cikin Yunin 2016. Elizabeth ta kasance Basarakiyar Birtaniya mafi jan zarenta a tsawon zamani, inda ta cika shekara 90 da haihuwa a watan Afirilu.
Queen Elizabeth II, 2001

Asalin hoton, Lichfield / Getty Images

Bayanan hoto, "Lokacin da nake 'yar shekara 21, na yi alkawarin saraiyar da rayuwata wajen hidima ga mutanena, na kuma roki Ubangiji ya taimake ni in cimma burina na wannan kyakkyawar manufa. Kodayake wannan alwashin rantsuwa na yi shi ne cikin kuruciyata, lokacin da nake yanke hukunci gaba-gadi, ba na nadamar hakan, ko tunanin janyewa, ko da kalma guda daga cikinsa."
White Line 1 Pixel

Dukkanin hotuna suna da hakkin mallaka.