Liverpool ta sanya ido kan Semenyo, Roma ta matsa ƙaimi kan Zirkzee

Antoine Semenyo

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da Mohamed Salah zai buga wa Masar gasar cin kofin nahiyar Afrika a watan Disamba da Janairu, ana ci gaba da alaƙanta Liverpool da zawarcin ɗan wasan gaban Bournemouth, Antoine Semenyo, mai shekara 25 a watan Janairu, wanda ƙasarsa Ghana ta kasa samun gurbin zuwa gasar. (Liverpool Echo)

Liverpool na kuma shirin zawarcin ɗan wasan tsakiya na AZ Alkmaar, mai shekara 19, Kees Smit. (Soccar News).

Roma na tattaunawa da Manchester United kan batun ɗaukar aron Joshua Zirkzee mai shekara 24 a watan Janairu, ta na kuma sa ran ƙulla yarjejeniyar da za ta haɗa da zaɓin sayen ɗan wasan gaban na Netherlands a bazara kan farashin Yuro miliyan 35. (Gazzetta dello Sport).

Idan har Roma ta kasa kai labari a zawarcin da ta ke yi wa Zirkzee, za ta karkata akalarta kan ɗan wasan gaban Tottenham da Faransa Mathys Tel, mai shekara 20. (Metro).

Ɗan wasan gaba na Chelsea ɗan ƙasar Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, ba shi da niyyar yanke zaman aronsa na tsawon kakar wasa a Bayern Munich domin ƙulla yarjejeniya ta dindindin a wata ƙungiya ta daban a watan Janairu. (Florian Plettenberg).

Real Madrid na duba yiwuwar karɓar tayin Yuro miliyan 20 - daga Sunderland, da Aston Villa da Wolves kan ɗan wasan gaban Sifaniya Gonzalo Garcia mai shekara 21. (Fichajes).

Real Madrid ba ta yi gaggawar tattaunawa da ɗan wasan bayan Austria David Alaba, mai shekara 33, wanda ke shekararsa ta ƙarshe na kwantiraginsa. (AS).

Tottenham na iya rasa tsohon ɗan wasan Everton Ademola Lookman, mai shekara 28, bayan da Atalanta ta sauya kocinta. Ɗan wasan na Najeriya ya samu saɓani da tsohon kociyan ƙungiyar Ivan Juric kafin a kore shi. (TeamTalk)

Ɗan wasan tsakiya na Amurka Christian Pulisic, mai shekara 27, yana son jira har sai AC Milan ta samu tabbacin cancantar shiga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa kafin ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da ƙungiyar ta Serie A. (Calciomercato),

A yayin da Ruben Amorim ke zafafa neman ɗan wasan tsakiya, Manchester United ta sanya ido kan ɗan wasan Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21, daga Brighton. (Mirror).