Liverpool ta fara zawarcin Ekitike, Napoli ta yi watsi da batun Nunez

Asalin hoton, Getty Images
Ana tunanin cewa Liverpool za ta yi takara da Newcastle United wurin neman ɗan wasan Eintracht Frankfurt ɗan ƙasar Faransa Hugo Ekitike, mai shekara 23, bayan an shaida ma ta cewa ba a da niyyar sayar da ɗan wasan Sweden Alexander Isak, mai shekara 25 a wannan bazarar. (Sky Sports)
Yayin da ta ke neman Ekitike, Liverpool ta kuma yi bincike game da wasu ƴan wasan gaba guda huɗu idan har ta kasa cimma yarjejeniya kan Isak -inda ta sanya ido kan Ollie Watkins na Aston Villa daVictor Osimhen na Napoli, da Yoane Wissa na Brentford, da kuma Rodrygo na Real Madrid. (Mail)
Napoli ta sanar da Liverpool cewa ta janye daga batun zawarcin ɗan wasan gabanta Darwin Nunez mai shekara 26. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan gaban Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, ya bayyana ƙarara cewa yana son barin Liverpool bayan da ƙungiyar ta yi watsi da tayin fam miliyan 58.6 daga Bayern Munich. (Athletic)
Leeds United ta cimma yarjejeniyar fatar baki da ɗan wasan Newcastle ɗan ƙasar Ingila Sean Longstaff mai shekara 27. (Athletic)
Tottenham na fafatawa da Inter Milan wajen zawarcin ɗan wasan bayan Belgium Koni de Winter mai shekara 23. (i paper)
Bournemouth na son £59m kan ɗan wasan bayan Ukraine Illia Zabaryni, mai shekara 22, wanda Paris St-Germain ke nema. (Independent)
Chelsea na shirin fara tankaɗe a tawagar ƴan wasanta, inda Joao Felix mai shekara 25 ya fara tattaunawa kan komawa Benfica shi kuma Christopher Nkunku ke shirin tattara kayansa ya bar Stamford Bridge. (Standard)
Manchester United ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Juventus da Brazil Douglas Luiz a kakar wasa ta bana, inda ita ma Everton ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 27. (Football Insider)
Ɗan wasan bayan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, ya ƙi amincewa da wani tayi mai tsoka daga wata ƙungiya da ke gasar Saudi Pro League. (Mirror)
Reds ta sanya farashin £43.5m a kan Konate ga duk ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗaukar ɗan wasan a bazarar nan. (AS)
Ɗan wasan Sassuolo da Italiya Andrea Pinamonti yana jan hankalin West Ham, a daidai lokacin da abokIyar hamayyarta Brentford ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan mai shekara 26. (Standard)
Leeds United na zawarcin ɗan wasan gaban Sifaniya Gonzalo Garcia, mai shekara 21, inda ta ke neman ɗaukar aron ɗan wasan daga Real Madrid. (Football)











