Hanyoyin da za ku biya kuɗin makarantar yaranku cikin sauƙi

Babban mutum rike da hannun yarinya ƙarama zuwa makaranta

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da makarantu suka buɗe a sabon zangon karatu, biyan kuɗin makarantar yara na ɗaya daga cikin manyan ƙalubale da iyaye ke fuskanta musamman a wannan lokaci da rayuwa ke ƙara tsada.

A ƙasashe irin Najeriya rashin wadata na tilasta wa iyaye da dama gaza sanya yaransu makaranta, ko kuma kai su makarantar da hankalinsu bai kwanta da ita ba, kasancewar ba su da halin kai su makarantu masu kyau.

Tsadar kuɗin makaranta da kayan karatu da kuma sauran bukatun da suka shafi ilimi na iya sanya iyaye cikin damuwa da tashin hankali, musamman idan ba su shirya tsaf ba.

Ga wasu iyaye, albashi ko kuɗin shiga da suke samu ba ya isa su biya dukkanin buƙatun gida tare da na makaranta, lamarin da ke tilasta musu yin aro ko neman tallafi daga wasu wurare.

A wasu lokuta ma, rashin shiri kan sa yara su tsaya a gida saboda iyaye ba su samu damar biyan kudin makaranta a kan lokaci ba. Wannan kuwa kan kawo tsaiko ga karatun yara da makomarsu gaba ɗaya.

Sai dai duk da wannan ƙalubale, akwai hanyoyi da dama da za su iya taimaka wa iyaye wajen shawo kan matsalar biyan kudin makaranta duk da cewa abu ne da zai iya zama mai wahala idan aka yi la'akari da zamanin da ake ciki kamar yadda Dr. Hauwa Ɓaɓura, ƙwararriya a fannin ilimi ta shaida wa BBC.

Ga wasu hanyoyi da ƙwararriyar ta ce iyaye za su iya bi domin biyan kuɗin makarantar ƴaƴansu cikin sauƙi:

Daidai ruwa daidai ƙurji

Hauwa Ɓaɓura ta ce akwai salon maganar Hausawa da ke cewa 'iya kuɗin ka iya shagalinka', wanda a ganinta gaskiya ne.

"Na farko kada ku kai yaranku makarantun da kuka san aljihunku ba zai iya ɗauka ba saboda za a zo ne ana da na sani ana neman bashi, shi ya sa yake da kyau a shirya da wuri kuma a biya a hankali," in ji ta.

Wannan in ji ta yana nufin cewa iyaye su kasance masu la'akari da yanayin da suke ciki, domin kada su jefa kansu cikin nauyin bashi da zai iya haifar da damuwa.

Tanadi da wuri

A cewar Hauwa, a ƙasashen waje iyaye kan buɗe asusun banki tun suna da ciki domin tara kuɗin karatun yaro.

"Ko da mutum bai buɗe asusu a banki da sunan yaron ba, zai iya buɗe asusu a gida. shiri yana daga cikin abubuwan da ke assasa nasara."

Wannan ƙwarariyar ta ce yana nuna cewa ko da kuwa ba a tanadi kuɗi masu yawa ba, yin hakan a hankali zai kawo sauƙi a gaba.

Kasafta kuɗi

...

Asalin hoton, Getty Images

Hauwa ta bayyana cewa kasafin kuɗi yana da matuƙar muhimmanci, wato ware kuɗin makaranta tun daga farkon shekara idan mutum ba zai iya tanadinsu ba. Wannan zai rage haɗari da matsin lamba daga baya.

Yin adashi

"Wata hanyar kuma ita ce a rinƙa ware kuɗi duk wata ana ajiyewa ko kuma yin adashi. Idan har mutum zai iya yin adashi, to ya yi adashin kuɗin makarantar ƴaƴansa," in ji ƙwararriyar.

Ta ce adashi na taimaka wa mutum ya tara kuɗi cikin sauƙi ba tare da ya ji nauyi ba.

Biya a hankali

...

Asalin hoton, Getty Images

Iyaye na iya tambayar makarantu su ba su damar biyan kuɗin makaranta a hankali.

"Za ka iya tambayar makaranta ta yi maka rangwame yadda za ka iya biya kashi-kashi har a zo lokacin da za ka gama biya kafin a saka doka ta cewa idan ba ka biya ba za a kori ɗanka."

Wannan zai ba iyaye damar rarraba nauyin kuɗi ba tare da barin yaro ya tsaya a gida ba.

Samun ƙarin hanyar kuɗin shiga

Hauwa ta shawarci iyaye da su nemi ƙarin sana'ar da za ta rika kawo musu kudi.

Idan aka samu kuɗi daga wannan ƙaramar sana'a, za a iya amfani da su wajen biyan kuɗin makarantar yara, maimakon dogaro da albashi kaɗai.

Karo-karo

A wasu lokuta, neman tallafi daga ƙungiyoyi ko ƴan'uwa ko abokai na iya zama mafita.

"Wani lokaci duk abin da ka yi sai ka ga kana neman taimako musamman a gidan da ake da 'ya'ya da yawa."

A wannan yanayi mutane za su iya taimaka wa ɗan'uwansu a lokacin da yake buƙata ko cikin matsi.

Sauya ɗabi'a

Hauwa Ɓaɓura ta jaddada cewa Hausawa na yin tanadi sosai wajen aure, amma ba sa yin hakan ga ilimi.

"Za ki ga tun lokacin da aka haifi yarinya iyaye suke fara sayen cokali ko roba da tabarma da sauransu suna tanadin aurenta. Amma ba sa tunanin ilimin 'ya'yansu mata.

"Haka zalika idan namiji ne, yana kai wa balaga za ki ga an fara tunanin haɗa kayan lefe da na zance, idan aure ya tashi, babu abin da ake rasawa, har da dangi za a haɗu a rufa asiri amma kuma ba ma irin wannan hadin kai wajen ba wa ƴaƴanmu ilimi."

Ta ƙara da cewa "ya kamata yadda muke himmatuwa wajen kayan ɗaki, haka ya kamata mu himmatu wajen kuɗin makaranta."*

A taƙaice, duk da tsadar rayuwa da matsin lamba, akwai dabarun da za su taimaka wa iyaye wajen tabbatar da cewa 'ya'yansu sun samu ilimi mai inganci ba zama a gida ba.