Yadda rashin tura yara makaranta ya yi katutu a Jigawa - Unicef

Asalin hoton, UNICEF/FACEBOOK
Duk da cewa ilimi shi ne gishirin zaman duniya, wani rahoton asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana cewa kashi goma sha shida da ɗori ne cikin ɗari kacal suke zuwa makaranta a jihar Jigawa.
Wadannan alkaluma na nuna koma bayan da ake fuskanta ta fuskar ilimi a Jigawa.
Wannan dalili ya sa gwamnatin jihar da bangaren majalisa da kuma UNICEF din sun amince da wani tsari da zai taimaka wajen tabbatar da cewa yaran da suka isa zuwa makarantar firamare da sakandare sun shiga.
Matsalar rashin zuwan makaranta wani al’amari ne da ke ciwa al’umomin nahiyar afrika ciki har da Najeriya tuwo a kwarya, duk kuwa da irin hobbasa da gwamnatoci a matakai daban-daban ke cewa suna yi wajen magance matsalolin da yiwa yara tarnakin zuwa makarantar.
Rahoton wanda aka fitar a baya-bayan nan, ya nuna cewa kashi arba'in da huɗu na yaran da suka isa shiga makarantun firamare da kuma kashi 52 cikin ɗari na wadanda suka isa zuwa sakandire, basa zuwa makaranta.
Rahoton ya nuna yadda wasu daga cikin yaran ke gararamba da yawan tallace-tallace, lamarin da ake ganin babbar matsala ce ga makomar yaran.
Dakta Lawan Yunusa Danzomo shi ne kwamishinan ma' aikatar ilimi matakin farko na jihar wanda ya ke cewa sun bullo da matakai iri daban-daban na magance matsalar.
"Duk wuraren da ba makarantu musamman a karkara ana zama da mutane da shugabanninsu wajen nuna musu muhimmanci ilimi".
"Ana karfafawa gwiwar gina sabbin makarantu da kuma samar da filayen da za a gina. Sannan wadanda ake dasu ana kokarin kara musu azuzuwa", in ji Danzomo.
Kwamishi nan ya nuna cewa gwamnati na narka kudade wajen ayyukan gyaran makarantu da shawo kan matsalar da gibin da ake da shi a wannan fannin.
Dakta Danzomo ya kuma nuna cewa sun lura akwai wasu matsaloli da suke hana yaran zuwa makaranta ciki har wasu al'adu.
"Akwai dabi'u na mutane kamar tura yara gona da talla da wasu ayyukan karfi kafin a ce za a tura su makaranta".
"Sannan talauci da ya yi wa kasa katutu, ya taka rawa wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnati da tallafin asusun na UNICEF sun yiwa shugabannin jihar kaimi, inda yayin wani zama da bangaren majalisa suka amince su rika tallafawa yara masa galihu.
Hon Haruna Aliyu Dangyatin kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce bayan sun gana da UNICEF ya rabawa yara littafai da abin rubutu har mutum 8,000 kyauta.
"Unicef ta kawo mana bayanai har ta gayyace 'yan majalisa ta basu bayanan kowane kanana hukumomi da yaran ba sa zuwa makaranta".
"Shi ne muka ga idan har Unicef daga ketare za ta tattara wadanan bayanai ya kamata a ba ta hadin-kai wajen shawo kan matsalar," in ji Hon Aliyu.
"Shiyasa mu ka koma mazabarmu mu na aiwatar da ayyuka da daukan matakan ganin an kai yara makaranta".
Gwamnatin jihar Jigawa ta kafa hukumar kula da makarantun tsangaya, inda za a tattaro yara al’majirai da marasa galihu a mayar da su makaranta su ci gaba da karatu.
Sannan kuma an samar da wani tsari mai taken 'mathers association' wanda zai shiga jawo hankalin iyaye mata su rika tabbatar da cewa 'ya'yansu suna zuwa makaranta akan lokaci.











