Kaduna: Yadda za ku nemi aikin koyarwa a jihar

Kaduna State school

Hukumar kula da malamai da yi musu rijista ta jihar Kaduna ta bayyana cewa tana shirin ɗaukar sabbin malaman makaranta a jihar, bayan soke shirin da ta faro na ɗaukar malaman a shekarun 2018/2019.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa a wannan karon za a ɗauki malaman makarantar sakandare ne kawai.

A wannan karon, ana sa ran cewa gwamnatin jihar za ta ɗebi malamai masu ɗumbin yawa da za su koyar a makarantun sakandare da ke a ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Abubuwan da za a tanada kafin neman aikin koyarwa

  • Dole ne mai neman aikin koyarwar ya zama yana da digiri ko kuma babbar difiloma daga makaranta ko kuma kwaleji wadda aka tabbatar da ingancinta
  • Ka da mai neman aikin ya wuce shekara 50 da haihuwa
  • Dole ne mai neman aikin ya zama yana da shaidar kammala shirin yi wa ƙasa hidima ko kuma takarda a rubuce wadda ke nuna an sawwaƙe masa
  • Masu digiri na biyu da digirin-digirgir za su iya neman aikin
  • Kuma dole ne su zama cikin shiri domin zuwa duk wurin da gwamnatin jihar ta tura su domin koyarwa

Yadda za ku nemi aikin koyarwar

Dole ne masu neman aikin koyarwar su cike fom ta intanet a shafin da aka tanadar wato tsbrecruitment.com

Shafin zai zama a buɗe domin masu neman aikin koyarwar tun daga ranar 28 ga watan Disamban 2020 zuwa 12 ga watan Janairun 2021.