Abin da ke hana miliyoyin yara mata zuwa makaranta a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
- Aiko rahoto daga, Abuja
Asusun Kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce Najeriya ce ke da kashi 15 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.
Unicef ya ce kimanin yara mata miliyan 7.6 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, mafiya yawancinsu daga jihohin arewacin ƙasar.
Jakadiyar Unicef a Najeriya, Cristian Munduate ce ta bayyana haka lokacin taron bikin ranar yara mata ta duniya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Misis Munduate ta bayyana damuwarta game alƙaluman tare da yin kira ga hukumomin ƙasar da su tashi tsaye domin ɗaukar matakan magance wannan matsala.
"Abin damuwar shi ne kashi 15 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya a Najeriya suke. Kuma kashi 9 ne kawai cikin ƴaƴan talakawa ke samun damar yin karatu zuwa matakin sakandire", in ji ta.
Ta ƙara da cewa “Maganar gaskiya ita ce yara mata miliyan 7.6 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, kuma mafi yawancinsu daga arewacin ƙasar suke''.
Hajiya Binta Shehu Bamalli, wata mai fafutikar inganta ilimin yara mata a Najeriya, ta ce wadannan alƙaluma ba su zo musu da mamaki ba kasancewar adadin raguwa ya yi, domin kuwa a cewarta a shekarun baya adadin ya zarta haka.
Ita ma Zainab Nasir Ahmed mai fafutikar yaƙi da matsalolin da ke damun al'umma ta ce wannan matsala ce da ta daɗe tana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya musamman yankin arewancin ƙasar.
Me ke hadasa matsalar?
Akwai abubuwa da dama da masana suka bayyana da cewa su ne dalilan da suka haifar da wannan matsala a Najeriya :
Talauci

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Talauci na daga cikin dalilan da ke hana iyaye bai wa yaransu ilimi, ko su zurfafa shi, kasancewa suna ganin ba su da abin da za su ɗauki nauyin yaran domin yin karatun.
A wasu lokatun kuma talaucin kan tilasta wa iyayen tura yaransu mata zuwa tallace-tallace domin samun abin biyan buƙatunsu ya yau-da-kullum.
Zainab Nasir ta ce "yanayi na karatu a yanzu, abu ne wanda dole sai da kuɗi, ko da kuwa gwamnati ta ce kyauta ne, to za ka ga dole sai iyayen yaran sun kashe nasu kudin a wasu ɓangarorin, kamar kuɗaɗen zirga-zirga da na abinci".
"Wasu iyayen a maimakon su yi wannan sun gwammace su ɗora wa yaran nasu tallace-tallace, saboda idan suka ce za su tura su makaranta, to dole sai sun hana su tallace-tallacen kasancewar a makarantun ba kudi za ku samo ba", in ji Zainab.
Binta Bamalli ta ce yanayin talauci na tilasta wa iyayen bautar da ƴaƴansu ta hanyar tura su tallace-tallace domin su taimake su wajen daukar ɗawainiyar gidajensu, a maimakon barinsu su je makaranta.
Fifita jinsin maza daga ɓangaren iyaye

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin matsalolin da ke daƙile karatun mata shi ne al'adar fifita jinsin maza a karatun boko fiye da jinsin mata.
Zainab Nasir Ahmed ta ce a arewacin Najeriya ana fifita jinsin yara maza fiye da mata a fannin kai yara karatun boko.
Ta ce "wasu al'umomin arewacin ƙasar musamman mazuna karkara na ganin aure ne ya fi dacewa da ƴaƴansu mata da zarar sun tasa maimakon barin su su ci gaba da karatun boko."
Rashin wayewa
Wani abun kuma da masana suka bayyana a matsayin dalilin matsalar shi ne rashin wayewa da sanin muhimmancin karatun tsakanin iyaye da su kansu yaran.
Binta Bamalli ta ce rashin sanin wayewar rayuwa na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa wannan matsalar.
"Ai wayewa ita ce ka san ciwon kanka, ka san me ya fi dacewa da kai a matsayinka na 'ya mace, yadda za ki kula da kanki, ki tarbiyantar da kanki, kafin ma 'ya'yanki", in ji Bamalli.
Hajiya Zainab ta ce "rashin sanin muhimmancin karatun shi kansa tsakanin iyayen yaran da su kansu yaran kan taimaka wajen haddasa wannan matsala".
Rashin tsaro

Asalin hoton, Getty Images
Wanna na daga cikin manyan matsalolin da ke ƙara assasa matsalar rashin zuwan yara makaranta a Najeriya musamnan mata.
A shekarun baya-bayan nan an ga yadda 'yan bindiga ke ƙaddamar da hare-hare musamman makaratun yara mata tare da sace wasu daga cikinsu.
Wannan matsala ta razanar da mutane da dama, lamarin da ya sa wasu ke ganin ya taka rawa wajen ƙaruwar matsalar rashin zuwa makaranta tsakanin yara mata a Najeriya.
Zainab ta ce tun shekarun 2014 aka fara sace yara mata a makarantu a Najeriya.
''Haƙiƙi wannan abu ya sanya iyaye da ma sauran jama'a da dama tsorata tare da cire yaransu daga makarantun boko, saboda suna tsoron kada abin da ya samu wasu ya same su", in ji Zainab.
Batun sace yara mata a makarantu a Najeriya ya daɗe yana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, alal misali a shekarar 2014 ƙungiyar Boko-Haram ta sace ɗaliban makarantar sakandiren Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.
Lamarin da ya tayar da ƙura a Najeriya tare da jan hankalin ƙasashen duniya, inda aka riƙa gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen ƙasar.
Auren wuri

Asalin hoton, Getty Images
Wani abin da ke haddasa matsalar rashin zuwan yara mata makaranta musamman a arewacin Najeriya shi ne auren wuri.
A wasu sasan arewacin ƙasar musamman yankunan karkara iyaye kan takaita karatun yaransu mata tun daga matakin furamare ko ƙaramar sakandire domin aurar da su.
Hajiya Zainab ta ce "iyaye ba sa la'akari da illar da rashin barin yaransu mata su kammala karatu ke haifar wa yaran ba".
Rashin yanayi mai kyau a makarantu
Hajiya Binta Shehu Bamalli ta ce wani abu da ke ƙara haddasa matsalar shi ne rashin ingantaccen yanayin karatu mai kyau a makaratun yara mata.
Ta ce a wasu makarantun babu ban ɗakuna masu kyau da tsafta sannan babu wani tsari na taimaka wa yaran musamman idan suna jinin al'ada.
"In da akwai yanayi mai kyau, da yaran za su je makaranta suna cikin koshin lafiya, suna da wuraren tsaftace kansu, kamar ban-ɗakuna masu kyau, sannan suna ta saro, to su kansu iyayen yaran za a iya shawo kansu cikin sauki su bar yaran su ci gaba da zuwa makaranta", Inji Bamalli.











