Waɗanne ƙasashe ne ke da nukiliya kuma ta yaya suka samu makaman?

A Yaƙin Duniya na Biyu, Amurka ta jefa makaman nukiliya kan biranen Japan biyu Hiroshima (hagu) da Nagasaki (dama) waɗanda suka yi mummunar ɓarna

Asalin hoton, Universal History Archive/Universal Images Group via Getty Images

Bayanan hoto, A Yaƙin Duniya na Biyu, Amurka ta jefa makaman nukiliya kan biranen Japan biyu Hiroshima (hagu) da Nagasaki (dama) waɗanda suka yi mummunar ɓarna
Lokacin karatu: Minti 6

Shekara 80 bayan Amurka ta jefa makaminn nukiliya na farko, shirin nukiliya na Iran na cikin abubuwan da suka jawo rikici a Gabas ta Tsakiya a baya-bayan nan.

A ranar 2 ga watan Yuli, shugaban Iran ya saka wa wata doka hannu da ta dakatar da ƙasar daga ci gaba da aiki tare da hukumar sa ido kan makamashin nukiliya nternational Atomic Energy Agency (IAEA) bayan Amurka da Isra'ila sun kai mata hare-hare.

Isra'ila da Amurka sun ce harin da suka kai ya zamar musu dole ne saboda su hana Iran ƙera makamin nukiliyar.

Har yanzu babu tabbas kan irin ɓarnar da hare-haren suka yi a tashoshin nukiliyar Iran, da kuma irin abin da sakamakon hakan zai jawo a yankin Gabas ta Tsakiya, da ma yarjejeniyar Non-Proliferation Treaty (NPT) da aka ƙulla shekara 55 da suka wuce.

Zuwa yanzu ƙasashe tara ne aka san suna da makaman nukiliya. Ta yaya suka mallake su? Ko wasu ƙasahen za su iya mallaka a yanzu?

Jefa bam ɗin nukiliya da Amurka ta yi a Hiroshima da Nagasaki, shi ne kaɗai lokacin da aka yi amfani da makamin a tarihi

Asalin hoton, Universal History Archive/Universal Images Group via Getty Images

Bayanan hoto, Jefa bam ɗin nukiliya da Amurka ta yi a Hiroshima da Nagasaki, shi ne kaɗai lokacin da aka yi amfani da makamin a tarihi

Su wane ne ke da makaman nukiliya?

Amurka da Rasha, da Birtaniya, da China, da Faransa, da Indiya, da Pakistan, da Isra'ila, da Koriya ta Arewa, su ne aka san suna da makaman nukiliya - kodayake Isra'ila ba ta taɓa amsa cewa tana da su ba.

Amurka ce ƙasa ta farko da ta fara ƙera makamin a asirce a cikin wani ɓangare na Shirin Manhattan - ko kuma Manhattan Project a Turance - yayin Yaƙin Duniya na Biyu.

Amurka ta harba makaman da suka yi muguwar ɓarna a 1945, inda ta jefa su a Hiroshima da Nagasaki a Japan - wadda ɗaya ce cikin ƙawancen soji da suka ƙunshi Nazi Jamus da Italiya - waɗanda ke yaƙi da sojojin ƙawance.

An yi ƙiyasin bam ɗin ya kashe aƙalla mutum 200,000. Har yanzu shi ne lokaci na farko kuma na ƙarshe da aka yi amfani da makaman a filin yaƙi.

Ƙwararriya kan makamai Dr Patricia Lewis ta ce "wannan ce ƙofa ta farko da aka buɗe wajen neman makaman nukiliya", inda ƙasashe musamman Tarayyar Soviet suka fara neman ƙera su ido rufe - ko dai don kariya daga hare-hare ko don nuna ƙarfin iko.

Me ya faru bayan hakan?

Ƙasa da shekara biyu bayan gama Yaƙin Duniya na Biyu, Yaƙin Cacar Baka ya fara - gwagwarmayar neman iko a duniya tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet, da kuma ƙasashen da suka mara musu baya na tsawon shekara 40, wanda aka dinga barazanar harba nukiliya a lokacin.

Tarayyar Soviet ta fara yunƙurin haɗa bam ɗin nukiliya tun lokacin Yaƙin Duniya na Biyu kuma suka yi nasarar yin hakan a 1949 lokacin da suka yi nasarar gwada shi, abin da ya kawo ƙarshen fankamar Amurka.

Bayan haka ne kuma ɓangarorin biyu suka dinga rige-rigen ƙera nukiliya da za su fi na baya muni.

Shekara 15 bayan haka, ƙasashe uku sun mallaki makaman.

A 1992, Birtaniya da ta haɗa kai da Amurka wajen ƙera makaman ta samu nata, sai kuma Faransa da ta ƙera su a 1960, da kuma China a 1964.

Yaushe sauran ƙasashe suka mallaki nukiliya?

A 1993, jawabin shugaban Amurka na lokacin Dwight Eisenhower mai taken "Atoms for Peace" a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya bayar da shawarar samar da nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, kamar samar da makamash

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A 1993, jawabin shugaban Amurka na lokacin Dwight Eisenhower mai taken "Atoms for Peace" a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya bayar da shawarar samar da nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, kamar samar da makamash

Zuwa shekarun 1960, manyan ƙasashen duniya - Amurka, Tarayyar Soviet, Birtaniya, Faransa, China - sun ƙara ƙarfafa ikonsu. Sai dai an yi fargabar ƙasashe da yawa za su mallaki makaman.

Hakan ta sa MDD ta bijiro da yarjejeniyar Non-Proliferation Treaty (NPT) domin daƙile yaɗuwar nukiliyar.

An fara aiki da ita a 1970, amma ba duka ƙasashe ne suka shiga ba.

Indiya ta samu nukiliya a 1974, Pakistan kuma a 1998. Dukkansu ba su shiga yarjejeniyar ba, musamman saboda fargabar tsaro da suke zargin juna.

Isra'ila ma ba ta shiga ba. Amma ta ci gaba da aiki da wani tsari na ƙin amincewa ko tabbatarwa cewa tana da makaman.

Koriya ta Arewa ta shiga yarjejeniyar tun da farko, amma ta fice a 2003 saboda zargin Amurka da Koriya ta Kudu da yin atasayen soji tare. A 2006, ta gwada wani makamin nukiliya.

Ƙasar Sudan ta Kudu, wadda aka kafa a 2011, ita ce ɗaya ƙasar da ba ta cikin yarjejeniyar.

A black and white photo shows US President John F Kennedy addressing the nation from the White House during the Cuban Missile Crisis on October 22, 1962

Asalin hoton, Getty Images

Ko Iran na da makaman nukiliya?

A kwanan nan ne Amurka ta kai wa tashar nukiliya ta Iran hari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A kwanan nan ne Amurka ta kai wa tashar nukiliya ta Iran hari

Iya abin da muka sani shi ne, Iran ba ta ƙera bam ɗin ba, a cewar Andrew Futter, farfesa a fannin siyasar ƙasashen duniya da ke Jami'ar Leicester.

"Amma kuma, idan aka duba ta mahangar kimiyya ko ƙwarewarsu, babu wani dalili da aka sani da ya hana su ƙera makamin."

Iran tana cikin yarjejeniyar Non-Proliferation Treaty (NPT) kuma ta sha nanata cewa nukiliyarta na zaman lafiya ne, sannan ba ta taɓa yunƙurin haɗa makaman ba.

Sai dai wani bincike da hukumar IAEA ta yi ya ce ya gano hujjar Iran ta aikata "abubuwan da dama masu alaƙa da haɗa bam ɗin nukiliya" daga 1980 zuwa 2003, lokacin da ta dakatar da wani shirinta mai laƙabin "Project Amad".

A 2015 ne Iran ɗin ta ƙulla yarjejeniya da ƙasashen duniya shida domin rage yawan makamashin uranium da take ingantawa, kuma ta yarda jami'an IAEA su dinga saka ido kan ayyukanta a madadin cire mata takunkumai.

Sai dai Donald Trump ya fitar da Amurka daga yarjejeniyar a 2015.

Ko Isra'ila na da makaman nukiliya?

Masanin kimiyyar nukiliya na Isra'ila, Mordechai Vanunu, ya fallasa makaman nata masu matuƙar sirri, kuma daga baya aka ɗaure shi shekara 18 a gidan yari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masanin kimiyyar nukiliya na Isra'ila, Mordechai Vanunu, ya fallasa makaman nata masu matuƙar sirri, kuma daga baya aka ɗaure shi shekara 18 a gidan yari

Isra'ila ba ta taɓa amincewa a hukumance cewa tana da makaman nukiliya ba, amma an yi imanin tana da su.

A watan Oktoban 1986, wani masanin kimiyyar nukiliya, Mordechai Vanunu, ya bai wa jaridar Sunday Times ta Birtaniya bayanan nukiliyar Isra'ila mafiya girma sama da yadda ake tunani tun da farko.

Saboda haka ne a ɗaure shi tsawon shekara 18 a gidan yari, inda aka sake shi a 2004.

Cibiyar Stockholm International Peace Research Institute (SIPRI) ta ce Isra'ila na zamanantar da makaman nata.

A 2024, Isra'ila ta yi gwajin wani makami mai linzami "da zai iya zama mai alaƙa da makamin Jericho da ke iya ɗaukar nukiliya" kuma da alama tana zamanantarwa da kuma inganta su a tashar Dimona, in ji SIPRI.

Ban da hare-haren da ta kai wa Iran, ta taɓa kai wa wata tashar nukliya hari a Iraƙi a 1981, da kuma wata tasha da ake zargin ta nukliya ce a Syria a 2007.

Waɗanne ƙasashe ne suka watsar da nukiliyarsu?

Ƙasashe irinsu Brazil, da Sweden, da Switzerland sun fara aiki kan makana nukiliya amma kuma suka watsar da shirin, ko dai don kansu ko kuma saboda matsin lamba daga ƙasashe.

Afirka ta Kudu ce ƙasa ɗaya tilo da ta haɗa makamin nukiliya kuma ta lalata su da kanta.

Bayan faɗuwar Tarayyar Soviet a 1991, ƙasashen da suka fita kamar Ukraine da Belarus, da Kazakhstan sun gaji nukiliya, amma sai suka bayar da su. Ukraine ta haƙura da nata a yarjejeniyar 1994 ta Budapest Memorandum.

North Korea's former leader Kim Jong Il is sat on a chair wearing a green shirt and glasses, with North Korean flags in the background

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, North Korea successfully tested a nuclear weapon in 2006, during Kim Jong Il's rule

Makaman nukiliya nawa ne a duniya?

Saboda gwamnatoci ba su fiya faɗar cikakkun bayanai kan nukiliyarsu ba, abu ne mai wuya a san takamaimai yawan makaman da kowace ƙasa ke da su.

Amma a cewar cibiyar SIPRI, ƙasashen sun mallaki jimillar nukiliya 12,241 zuwa watan Janairun 2025, inda Rasha da Amurka ke da kusan kashi 90 na duka makaman.

Ganin cewa yawan makaman da ake jinginewa sun fi waɗanda ake amfani da su a filin yaƙi yawa, akwai yiwuwar wannan tsarin ya sauya a shekaru masu zuwa, in ji cibiyar.