Mutanenmu da aka kama a Abuja na cikin mummunan yanayi — Masu bukata ta musamman

Asalin hoton, OTHER
Wata kungiyar masu bukata ta musamman a Najeriya ta koka kan halin da wasu 'ya'yan kungiyar da aka kama a kan titunan Abuja, babban birnin tarayyar kasar ke ciki.
Kungiyar ta ce wasu daga cikin 'yan kungiyar ta su da aka kama sun shafe watanni ana rike da su cikin yanayi mai muni, ba tare da an sake su ba, ko an gurfanar da su a gaban kuliya.
Kungiyar ta kara da cewa halin da masu bukata ta musamman din suka tsinci kansu a inda aka kai bai kamata ace wani dan adam ya kasance a ciki ba.
Chuanoemeh Bulus Nukunya, shi ne sakataren kungiyar ta People With Disability Forum,ya shaida wa BBC cewa akwai 'ya'yan kungiyar tasu da aka kama a Abuja da suka shafe sama da wata biyu an kai su Bwari an ajiye ba tare da an sakesu ko an kai su kotu.
Ya ce," Wajen da aka ajiyesu waje ne a yadda muka samu labari babu abinci, domin har zuwa wajen mun yi mun ganewa idanunmu yanayin wajen kamar ba mutane ake ajiyewa ba, kuma a matsayinsu na dan adama bai kamata ace an ajiyesu a irin wannan wajenba gaskiya."
" Mun je mun kai musu ziyara tare da kai musu kayan abincin da zamu iya basu, to halin da muka gansu gaskiya bamu ji dadi ba."In ji sakataren kungiyar masu bukata ta musamman a Najeriyar.
Chuwano Imo Bulus Ni Kunya, ya ce" Muna kira ga gwamnati kan su san halin da mutanenmu ke ciki a fitar dasu, amma kuma idan har an same su da laifi to ya kamata akai su kotu don ayi musu hukuncin da ya dace, to amma a kullum abin da ake cewa idan an kama mutanenmu shi ne barace-baracen da ak ne ba a so."
Ya ce," To idan mutum yana matsayin dan kasa bashi da aikinyi, wasu daga cikinmu sun yi makaranta amma basu samu aiki ba gashi babu sana'aryi to ya mutum zai yi da rayuwarsa ai dole ya fita ya nemi abin da zai ci."
Sakataren kungiyar masu bukata ta musamman din na ya ce," Ba wai muna karfafa musu gwiwa su yi bara bane, yakamata gwamnati ta samar musu da abin yi ta yadda zasu sauki kaga barar ma ba za su yi sai dai su rika taimakawa wasu ma."
To BBC ta tuntubi hukumar bunkasa jin dadi da walwalar al'umma ta kasa reshen Abuja kan wannan koken, to amma daya daga cikin jami'an da aka tuntuba sun ce ba za su iya yin bayani ba, kodayake wata majiyar da bata yarda a ambaci sunanta ba a hukumar ta musanta zargin, inda ta ce tuni aka mayar da wadanda aka kama jihohin su.
Majiyar ta ce babu wani mai bukata ta musamman da ake rike da shi da suka jima ana ajiye da su.











