Najeria@64: Nakasassu sun koka kan rashin 'yancin walwala

Masu bukata ta musamman

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da Najeriya ke murnar cika shekaru 64 da samun 'yancin kai, masu bukata ta musamman a kasar sun yi waiwaye kan inda aka kwana wajen kare hakkoki da kuma kyautata rayuwarsu a kasar.

Masu lalurar nakasa ko bukata ta musamman sun yi waiwayen ne a yayin wani taro da suka gudanar a birnin Kano karkashin inuwar kungiyar Northern Nigeria Disability Forum (NNDF).

A yayin taron, sun yi duba a game da abubuwa da dama ciki har da batun ilimi da lafiya da rabon tattalin arzikin kasa dama harkar zaman takewa.

Cikin abubuwan da suka gano shi ne har yanzu masu bukata ta musamman din na fuskantar matsaloli wajen harkar zaman takewa kamar yadda Yarima Sulaiman Ibrahim, shugaban kungiyar ya shaida wa BBC.

"Abin da muka lura shi ne har yanzu mutane basu fahimci matsalar masu bukata ta musamman ma bame ballantana su taimakesu, mutanen da suka fahimcemu kalilan ne."

Yarima Suleiman Ibrahim, ya ce kundin tsarin mulkin kasa ya bayar da damar samun 'yanci, amma a bangaren wannan ‘yancin ba a la'akari da masu bukata ta musamman.

"Ta fuskar walwala, masu bukata ta musamman basu da wannan ‘yanci, domin a wasu jihohin Najeriya kamar Legas da Abuja, ana yawan kama masu bukata ta musamman a tozarta shi."

Shugaban kungiyar ta Northern Nigeria Disability Forum(NNDF), ya ce a wasu jihohin akwai wuraren da ake zuwa ana ajiye masu bukata ta musamman wanda dan adam mai ‘yanci bai kamata aje a ajiye shi a wajen ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Babbar damuwarmu a yanzu shi ne za ayi gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya, bamu da wakilci a wajen gyaran ballantana ma a san menene ma matsalarmu."

Yarima Suleiman Ibrahim, ya ce "Ko shakka babu an samar da hukumar da ke kula da masu bukata ta musamman, to amma har yanzu bata yin abin da ya kamata ace ta yi saboda har yanzu mutanenmu na bara a kan titi, to da ace hukumar na aikin da ya dace to ba za a ga masu bukata ta musamman na bara a kan titi ba."

"Babbar ribar da zamu ce mun samu ita ce fadin albarkacin baki don yanzu kam muna da damar fadin albarkacin bakinmu, to amma sauran hakkokinmu ne muka rasa."

Shugaban kungiyar ta Northern Nigeria Disability Forum(NNDF), ya ce yanzu za su yi fito na fito da matsalolin da ke damunsu don su tunkaresu da gaske.

"Muna bukatar ‘yan majalisun tarayya da sanatoci da su bar kofofinsu a bude saboda gyaran kundin tsarin mulkin kasa da za ayi yanzu muna so mu shigo ciki domin ayi damu, saboda a gyara abubuwa da dama da ke ci mana tuwo a kwarya kamar cin zarafi da kuma yadda ake yi mana kallo."

"Mu yanzu abin da muke so hukumomi su yi mana shi ne a rinka duba me dokar kasa ta ce a bamu, domin dokar kasa ta ce duk wani abu da za a raba a bamu kashi biyar cikin 100, sannan kuma muna so gwamnatocin jihohi su samar da hukumomin da zasu rinka kula da bukatunmu," In ji shi.