‘Ba a ba mu taimakon da ya dace don dogaro da kai’

Asalin hoton, OTHER
Masu buƙata ta musamman sun koka cewa ba su samu taimakon da ya dace domin samun dogaro da kansu.
Sun yi wannan ƙorafin ne yayin bikin ranar masu buƙata ta musamman da ake gudanarwa duk shekara 3 ga watan Disamba da Majalisar Dinkin Duniya ta ware.
An ware ranar ne domin duba batutuwan da suka shafi masu bukata ta musamman, da nufin yin gangamin tallafa masu ta fuskar kare mutunci da hakkokinsu, da kuma kyautata halin rayuwarsu.
Ana amfani da wannan rana don fadakar da sauran al'ummar duniya game da muhimmancin damawa da masu bukata ta musamman a daukacin al'amuran rayuwa, kamar siyasa da zamantakewa da tattalin arziki da al'adu da dai sauransu.
Sai dai a Najeriya, wasu masu bukatar ta musamman sun ce wannan rana ta bana ta zo musu da kalubale daban-daban, da nasarori har ma da matsaloli.
Alhaji Sani Muhammad, Galadiman makafin Sakkwato, kuma babban sakatare a majalisar Sarkin makafin mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa a wasu wurare masu irin wannan lalura suna farin ciki da wannan rana, saboda irin kulawar da suke samu, saɓanin wasu jihohi musamman na arewacin ƙasar.
"Akwai damuwa kwarai da gaske ga masu bukata ta musamman domin ba sa samun kulawar da ta dace," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, ”babban ƙalubalen da suke fuskanta na rayuwa shi ne rashin tsaro da ya tarwatsa al’ummar arewa abin da ya janyo su kansu masu bukata ta musamman din ba sa samun kulawar da ta dace."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Hakan ya sa ake komawa barace-barace, kuma maimakon irin basussukan da ake bayarwa ga mutane mata da matasa a kan su rinka sana’oi don dogaro da kansu, ba a ko ina ake ba wa masu bukata ta musamman ba," a cewarsa.
Ya ce rashin samar da bashi ga masu buƙata ta musamman na tilasta wa wasu yin bara maimakon dogaro da kai.
Galadiman makafin Sakkwaton ya ƙara da cewa ba su samu wakilci a muƙaman gwamnati.
"Muna so a rinka ba mu wakilci don hakan ne zai sa mu sanana kulawa da mu.”
Ya ce dole ke sa masu bukata ta musamman yin bara saboda rashin makama aboda rashin tallafin da ya kamata, ko mutum ya yi karatu amma ya rasa aikin yi. "Hakan ke sa ba wani zaɓi illa bara," in ji shi.
Malamin addinin musulunci da ke Maiduguri a jihar Borno, Sheikh Musa Muhammad Umar, wanda aka fi sani da Bakura Addussawi, ya yi kiran jan masu bukata ta musamman a jiki maimakon kyamatar su.
Amma malamin ya sake yin kira ga masu bukata ta musamman inka sanya wa ransu cewa kamar kowanne mutum babu abin da zai gagare su koda kuwa suna da wata nakasa, su cire shakku suna jajircewa.
Tun a shekarar 1976 Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana 1981 a matsayin shekarar masu bukata ta musamman, inda kuma aka fara bikin ranar daga 3 ga watan Disamba 1992.
Masu buƙata ta musamman suna gamuwa da ƙalubale daban-daban a ko’ina a fadin duniya.
Kidididga ta nuna cewa mutane masu bukata ta musamman a Najeriya sun kai sama da kashi 15 cikin dari na al’ummar kasar - kimanin mutum sama da milyan 30 ke nan.











