Abin da ya sa gwamnatin Borno ta haramta bara a Maiduguri

Asalin hoton, OTHER
Gwamnatin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ta ce za ta hukunta duk wanda ta kama yana bara bayan ta sanar da haramta barar a Maiduguri babban birnin jihar da wasu kananan hukumomin .
Gwamnatin ta sanar da cewa yin bara yanayi ne na kaskantar da kai a cikin al’umma.
Matsalar 'yan gudun hijira dai ta kara ta'azzara bara a Borno wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.
Sai dai yayin da gwamnatin jihar Bornon ta sanar da aukar wannan mataki, wasu masu bukata ta musamman sun ce duk wanda aka ga yana bara ba shi da yadda zai yi ne.
Muhammed Mustapha, shi ne shugaban kungiyar masu lalurar gani, kuma daya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin masu bukata ta musamman a jihar Borno, ya shaida wa BBC cewa akwai hanyoyin da ya kamata gwamnati ta bi idan ta na so ta taimaki masu bara su daina.
Ya ce "Abin da ya bani mamaki shi ne kwanannan aka dauki malaman makaranta dubu hudu ko dubu biyar, amma ba a yi aiki da dokar da tsohon shugaban Najeriya ya sa hannu ba wadda ta ce a dukkan aikin da za a dauka a fadin a kasar, to ya kasance an bawa masu bukata ta musamman kashi biyar cikin 100 na adadin wadanda za a dauka aiki.”
Ya kara da cewa "a cikin nakasassu akwai wadanda suka yi karatu, amma ba a basu gurbi a daukar malaman da aka yi ba, to sai kawai rana tsaka ace wai an hana bara.”
Muhammed Mustapha, ya ce sau da dama ana yanke hukunci ba tare da na tuntubesu ba.
Ya ce “Idan akwai wani shiri da gwamnati za ta y iwa nakasassu na moriya ko na jin dadi, ai muma muna ganin baran kamar kaskantar da kai ne, kuma akwai wasu wuraren ma da ‘yan gudun hijira ne ke bar aba nakasassu ba.”
Masu bukata ta musamman din sun mayar wa gwamnatin jihar martani ne bayan ta fitar da sanarwa a kan haramta bar atana mai cewa kaskantar da kai ne.
Farfesa Usman Tar, shi ne kwamishina yada labarai da harkokin cikin gida a jihar, ya shaida wa BBC cewa,” Bar aba al’adar um ba ne kuma ba addininmu ba ne, kuma dama tun tuni gwamnati ta hana baran.”
Ya ce “Akwai hukumar tsangaya ta musamman, inda da malamai da kuma almajirai za a ba su taimako don su nitsu su yi karatu ba sai sun fita sun yi bar aba.”
Ya ce daga yanzu tun da an sanar da haramcin bara, to ba a son aga kowa a titi yana bara, idan har aka mutum to doka za ta yi halinta, in ji shi.
Ana dai danganta yawan barace-barace a kan tituna a jihar ta Borno da matsalar yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.










