Daliban da ke tafiya makaranta tun kafin asuba a Lagos

- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nigeria
Cunkoson ababan hawa da ya yi kaurin suna a birnin Legas na Najeriya na hana kananan yara samun isasashen barci.
Lokacin da Oluwapelumi Ogebere mai shekaru 14 ke barin gida zuwa makaranta da misalin karfe hudu da minti hamsin na asuba, akwai tsananin sanyi da kuma sauran duhu.
Rike da hannunta tare da na mahaifiyarta Atinuke Ogebere, jakar makarantar da ke goye a bayanta kan rika yin wani sauti a yayin da ta ke gogar rigar makarantarta a lokacin da suke cikin tafiyar fiye da mita 100 zuwa wurin jiran motocin haya.
Da kyar suke iya ganin abinda ke gabansu, hasken tocilan dake jikin wayar salular Mrs Ogbere kan iya haska siririyar hanyar da ke gabansu ne.
Amma dukanninsu na na tafiya ne yadda suka saba a kullum - sun saba yin hakan a ko wace ranar zuwa makaranta tun a shekarar 2018 lokacin da suka koma yankin Ikorodu na jihar Lagas.
Duk wani bata lokaci a kan yadda suka saba fita, ga misali idan Mrs Ogbere bata farka daga barci da misalin karfe biyu na dare ba, ko kuma bata tashi 'yarta da misalin karfe hudu na asubahi ba - ko safa ta bata - hakan na nufin Oluwapelumi za ta tsinci kan ta cikin wani lokci na ruguguwa da kokowar shiga motar haya saboda cunkoson jama'a da ababan hawa, tare da isa makarantar sakandare a makare mai nisan kilomita 18 (mil 11) daga gundumar Ikeja.
Jama'a da dama na fuskantar irin wannan hali - kana, ganin kananan yara, wasu ba su fi shekaru biyu ba, jingine a cikin motocin safa da misalin karfe biyar na safe ya zama ruwan dare a cikin birnin.
Haka su ma iyaye ma'aikata kan yi wannan ruguguwa kafin asubahin farko don sauke 'yayansu a makaranta kafin su wuce wurin aiki da wuri saboda su kaucewa cunkoson ababan hawa, kana da yamma a kan hanyarsu da komawa gida su sake dauko su daga makarantar.
Kananan yara na bukatar barci
Amma kuma masana na gargadin cewa wadannan sa'oi masu tsawo na yin mummunan tasiri kan harkokin ilimin kananan yaran da zai haifar musu da mummunan sakamako na tsawon shekaru.

"Yaron da ke ya kamata a ce ya samu sa'oi tara nab arci, na samun watakila sa'oi biyar ko bakwai ne, karamin yaro bai shirya fuskantar irin wannan rayuwa ba,'' in ji Fehintola Daniels, wata kwararriya a fannin a kwalkwalwa a Legas.
Kananan yara da ke tasowa a kan irin wannan rayuwa kan gamu da matsalar rashin barci, da firgici, da rashin natsuwa, da karancin kula, wanda kan haifar da shiga matsalolin tsanannin damuwa da bacin rai.
Yara masu shekaru uku sun yi kankantar fahimtar yanayin aiki, da cunkoson ababan hawa da ma zuwa makaranta,'' don haka ba za su fahimci me yasa mama za ata tashe su da sassafe ba,'' Mrs Daniels ta bayyana.
Mrs Ogbere ta amince cewa ilimin 'yarta ya samu nakasu saboda tashi da karfe hudu na safe har na tsawon shekaru hudu.
"In ba don wannan damuwa ba, na tabbata da ta fi haka yin kwazo a makaranta.''
"Idan n ace hakan bai shafi rayurwata ba, ina yaudarar kai na ne,'' Mrs Ogbere ta ce.
Amma tana ganin zabi kadan suke da shi lokacin da suka koma da zama a yankin Ikorodu saboda basu gamsu da zabin makarantar kudin ba - kuma ba za su iya samun makarantar gwamnati a kusa ba.
Sun zabi komawa makarantar gwamnati a Ikeja, da ya tilasata wa Oluwapelumi shiga motar haya sau biyu a rana a kan daya daga cikin hanyoyi mafi cunkoso a birnin Legas.
Lokacin shakuwa
Amma akwai wasu iyalai da ke daukr cewa iyalan gidan Ogbere sun samu sauki.
Wasu da ke zaune a tsakiyar birnin Leagsa kana suna aiki a gundumomin kasuwanci na tsibirin birnin Legas, kan saka 'yayansu a makarantu da ke kusa da wuraren aikinsu don samun sauki hawa mota.

Wata ma'aikaciyar banki Adaora Uche da ke zaune a unguwar Shangisha da ke tsakiyar birnin tare da dan ta mai shekaru uku duka kan fita daga gida da misalin karfe hudu da minti arba'in da biyar na safe zuwa yankin Victoria Island - wata tafiyar kilomita 27.
Tafiyar motar kan kai su har kan gada ta uku ta tsakiyar birnin wato Third Mainland Bridge - wacce ta yi kaurin suna wajen cunkoson ababan hawa da akan shafe kusan sa'oi hudu a daidai lokacin ruguguwar ffitar.
Dole su wuce ta wannan hanya sau biyu a rana.
"Ba ni da wani zabi illa in dawo da shi kusa da wurin aikina,'' in ji Mis Uche mahaifiyar yaron.
Daya zabin shi ne ta saka yaron nata a makarantar da ke tsakiyar birnin amma kuma hakan na nufin za ta rika daukarsa a makare kamar da karfe tara ko takwas na dare.
"Tafiyar motar na ba mu damar kara shakuwa. A lokacin da muke makale a cikin cunkoson ababan hawan mu kan rika hira game da abubuwan da ya kamata mu tsara, hakan ma in barci bai dauke shi ba kenan,'' ta ce.
Amma wadannan abubuwa nay au da kullum na da mummunan sakamako, Mrs Daneil ta yi gargadi - wani abu da Lawrence James, wanda yanzu shekararsa 30 ya riga ya saba da shi.
Lokacin yana karamin yaro yak an bar gida da misalin karfe hudu da rabi na safe har na tsawon shekaru 12 a lokacin yana karatu a birnin Legas.
"Lokacin da ka shiga cikin makaranta, ka riga ka galabaita ta yadda ba za ka iya daukar darasi yadda ya kamata ba,'' ya ce.
Ya ce hakan ya sa ya kan kosa a matsayinsa na baligi - kuma ya kasa jure wa da zaman Legas.
Yanzu ya bar Legas ya koma Calabar a kudancin Najeriya, inda y ace rayuwa ta fi sauki kuma tana tafiya cikin kwanciyar hankali da samun natsuwa.
Neman makarantu a kusa da gida
Suk an su malaman makarantar a Legas na cewa sun fara gainin karin yara na barci a cikin aji ko kuma zuwa makaranta a hargitse.

"Ba sa aikin gida saboda sun riga sun gaji, bai kamata a rika wahalar da su haka ba saboda sun yi kankanta,'' in ji Fayan Ekeng, wata malamar makaranta a yankin Iyana Paja na Legas.
Amma ta fahimci cewa dole iyaye su yi aiki don tallafa wa iyalansu tare da bayar da shawarar cewa idan sun samu hali su kan koma neman makarantu a kusa da gida kana su dauki 'yan aiki don rage musu wahalhalun renon yara a Legas.
Lokacin da Oluwapelumi ta isa tashar mota ta Agric don samun motar haya da wuri zuwa Ikeja, ta tarar tuni wurin ya cika makil da masu hawa motar a can - ana iya ganin wani dogon layin da ya lankwasa daga fitilar tocilan ta cikin wayoyin salular kowa.
Akasarinsu na sanye da kayan makaranta, wani karamin yaro sanye da koriyar rigar sanyin makaranta na barci a bayan mahaifiyarsa.
A cikin jakar makarantar Oluwapelumi akwai wayar salula, ta kan yi wa mahaifiyarta sakon kar-ta-kwana a lokacin da ta isa makaranta a cikin sa'oi biyu.
Mrs Ogbere ta yi wata gajeruwar addu'a tare da fatan dawowar 'yarta gida cikin koshin lafiya nan gaba kadan - dawowarta gida zai kai zuwa tsakanin karfe hudu zuwa karge bakwai na yamma.











